Ticker

6/recent/ticker-posts

Hukuncin Matar Da Take Bayyanar Da Tsiraicinta A gidanta

𝐓𝐀𝐌𝐁𝐀𝐘𝐀

Mallam ga tambayata kamar haka ya ya hukuncin matan aurenda take barin tsiraicinta karara amma a gidanta sai tawuni takwana baruwanta idan miji ya yi magana sai tace itada gidanta?

𝐀𝐌𝐒𝐀❗️

الحمد لله وحده.

Asali shi ne ya halatta mace tasanya tufafi agaban mijinta wanda zai bayyanar da al'aurarta gareshi, haka shima ya halatta ya yi shigar dazata bayyanar da al'aurarsa agaban matarsa, domin umarnin kiyaye al'aura baya shiga cikin bayyanar da al'aurar ma'aurata ga junansu atsakaninsu, da abun da damansu tamallaka (kuyanginsu)

Daka mu'awiya bin haidata Alkushairi ya ce: nace ya manzan Allah Al'aurarmu meya kamata mubayyanar kuma meya kamata mu kiyayi bayyanar dashi? ya ce: (ka kiyaye al'aurarka saifa ga matayenka ko kuyanginka) sai ya ce: sai na ce; ya manzan Allah idan kuma mutanen sashi daya suke fa maza zallah ko mata zallah? sai ya ce: (In za ka iya kada ka sake kowa yaga Al'aurarka, to ka yi hakan kada ka sake wani yagani) sai ya ce: sai na ce; ya manzan Allah idan dayanmu yakasance akeɓancefa shi kaɗai? sai ya ce: Allah shi ne yafi cancanta aji kunyarsa, sama da mutane)

Turmuzi ya ruwaito shi (2794) da Abu dauda (4017) da ibnu majah (1920) Albani ya ingantashi a cikin sahihul turmuzi.

Saboda haka abun da take aikatawa haramun ne idan tana takama gidan tane to ai Allah shi ya fi cancantar aji kunyarsa sama da mutane kamar yanda ingantaccen hadisi ya nuna dan haka wajibi ne mijinta ya tsawatar mata ya tashi sosai a kanta har sai tagyara wannan mummunar al'ada, dan muddin yadauki abun sako sako hakan zai yi tasiri sosai wajan gurbacewar tarbiyyar 'ya'yansa dama rashin albarka a cikin gidansa, kuma Shaiɗanu za su yawaita a gidan daman barin al'aura da kazanta a gida da rashin jin kunyar Allah suke baiwa Shaiɗanu gindin zama a cikin gidan mutum gidan ya rikice kullum babu kwanciyar hankali.

Amma duk dahaka wannna hadisi yana nuna mana halaccin wasu ababe kamar haka, yahalatta mace tasanya kananun kaya ga mijinta, da kuma shara shara waɗanda suke bayyana al'aurarta, da matsatstsun kayan dasuke bayyana duk wani tudu da loko najikinta ga mijinta, saboda ya halatta atsakaninsu suga juna tsirara, babu wata hujjah tahana ma'aurata sanya matsatstsun kayawa junansu damasu shara shara da kananu, saboda yahalatta suga juna tsirara.

An tambayi malaman lajnatul da'ima na saudiyya, shin sanya matsatstsun kaya damasu shara shara haram ne ko halal saboda mace tanayi da nufin yiwa mijinta ado dashi?

Sai suka amsa: Idan mace takasance tanayin haka ne kawai awajan mijinta yahalatta, idan ba mijinta kawai take bayyanawa wannan shigar ba bai halatta ba, saboda abun da ke cikin hakan nabayyana surar jiki, da bayyanar da guraren da ake fitinuwa da mace, Fatawa lajnatul da'imah (24/34)

Yazo a cikin mausu'a fiƙhiyyah (6/136)

Bai halatta sanya matsatstsun kaya ba ko shara shara idan yana bayyana al'aura, ta yanda za a iya gane launin fatar mutum jah ce ko baka ko kasa kasa, da maza da mata duk hukuncin ɗaya ne, mace ko da a gidan tane bai halatta ta sanya irin waɗannan kayan ba, idan akwai wanda zai iya ganinta wanda ba mijin taba, saboda dalilai da suka zo akan hakan, waɗanda suke da alaƙa dahakan, da kuma abun da ke ciki na zub da mutunci, dakuma saɓawa tafarkin magabata nakwarai, bai halatta yin sallah da irin wadanan tufafin ba, amma yahalatta mace tasanya shi idan babu wanda zai gani sai mijinta.

shaik salih Alfauzan hafizahullah ya ce: bai halatta ga mace tasanya irin wadannan tufafi matsatstsu da masu bayyanar da surar jiki ko shara shara agaban 'ya'yanta ba, ko muharramanta saidai abun da al'ada ta gudana akai na yaye abun da babu fitina a cikinsa, zata sanya sune kaɗai ga mijinta, fatawa shaik salih alfauzaan (3/170).

Duk da haka bai halatta mace tasa tufafin da maza kaɗai suka keɓanta dasanya suba, ko wanda ya yi kama da yanda kafirai suke shigarsu.

WALLAHU A'ALAM.

Zauren Tambaya Da Amsa Abisa Alkur'ani Da Sunnah. Ga Masu Buƙatar Shiga Wannan Group Zaku iya bi ta Links ɗin mu...

𝐅𝐀𝐂𝐄𝐁𝐎𝐎𝐊👇

Https://www.facebook.com/groups/336629807654177

𝐓𝐄𝐋𝐄𝐆𝐑𝐀𝐌👇

https://t.me/TambayoyiDaAmsoshi

ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚ

**************************

Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.

Question and Answers in Islam

Post a Comment

0 Comments