1-
APC sun yi shegiya,
Asuwajo ya min tsiya,
Don ya yi ɓarinmakauniya,
Rantsarwa za su wataya,
Kai Bola 'Dan mutuniya,
Jagoran Y'an a rausaya,
Tinlin Tinubun buhun wuya,
Ni ban fatan ka tausaya,
Dilan ƙwayar a kewaya,
Gaɓun
galaɓon Baturiya,
Cinnaka 'Dan magajiya,
Mai tsotsa ruwan kwatanniya,
Bana yin sak na antaya
Na bi y'an alalen kunun tsiya,
Ko wawayen Bahaushiya,
Mai kai wasu Naru-hawuya,
Ko masu zarar kuɗin
lya,
Su raba biyu su da ƙungiya,
Oga zai cilla ƙugiya,
Su yi mamure 'Danbarauniya,
Tutarmu su kau da koriya,
Su sako jajur wakiliya,
Shi ma Baharin garin ɗiya,
Gagaji na Y'an Tatsunniyya,
Ya kai mu cikin garin wuya,
La'ananne da ta shegiya,
In kun isa zo mu zagaya!!!
Marubuci:-
Abdullahi Lawan Kangala
Phone:- +2348033815276
KANGALA GLOBAL AWARENESS VIA MEDIA
0 Comments
ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.
HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.