Ticker

6/recent/ticker-posts

Waiwaye Adon Tafiya

Dafa-duka 'Dan gidan Marka,

Ya kar akuya ya bar jaka,

Ya sanya uwar cikin salka,

Ya lanƙwasa kan ya tattaka,

Ya tara giya ya hau zuƙa,

Ya din ga layi yana miƙa,

Suna ta kiɗa kamar hauka,

Su zo da kuɗi su lilliƙa,

A ci ci a sha suna gauƙa,

Suna ta rabon ƙahon-zuƙa

Abuja Kaduna sun mulka,

Suna ta fakon su yanka ka,

Su sace kuɗi su raina ka,

Da kai magana su ɗaure ka,

Su sa Folis su more ka,

Jihar ka su tarfe hanyar ka,

Su sa yara su sace ka,

Wurin sana'a su kore ka,

Gabanka su rushe shagonka,

Sun amshe kuɗin harajinka,

Da ka dawo su kama ka,

Su zargi gida da fanshe ka,

Su barka ana ta dukanka,

A dauji babu babarka,

Folis ne za su kare ka,

Amma su ne ke zane ka,

'Dan kore ya din ga zaginka,

Da hauri har da shurinka,

Ka yarda kawai su yasheka,

Su kwace gida da motarka,

Ran zaɓe sai su zo gun ka,

Su tsuttsuguna su gaida ka,

Suna sun san mutuncinka,

Ka ba su aron mubayu'ar ka,

Gabanka su seba lambarka,

Da sun tafi sai su share ka,

Idan ka kira su yanke ka,

Kana da ɗa yi su toshe ka,

Ka je ofis su karya ka,

A karye su je su ɗaure ka,

A hannu ka tai da ankwarka,

DSS za su caje ka,

Gida da wajen sana'arka,

Su hana a ba da belinka,

Ga ba damar ibadarka.

Marubuci:-

Abdullahi Lawan Kangala

Haƙƙin Mallaka:

Phone:- +2348033815276

KANGALA GLOBAL AWARENESS VIA MEDIA

Post a Comment

0 Comments