Ticker

6/recent/ticker-posts

Inuwar Marubuta

Yakasai, S. A. & Sani, A-U. (2021). Diwanin Waƙoƙin Aminu Ladan Abubakar (ALA)Kaduna: Amal Printing & Publishing Nigerian LTD. ISBN: 978-978-57624-9-0.

Amshi

Inuwar marubuta jihar Kanawa da Hausa,

Masu burin karaɗe cikin ƙasashe da Hausa.

 

Rabbu sarki guda ɗaya,

Wanda ya yi mu gari ɗaya,

Ya ba mu niyya iri ɗaya,

Muke rubutu da Hausa.

 

Na yi salati a cure,

Inda matsayi ya tare,

Wanda shi ne ya jure,

Fagen kira babu wasa.

 

Asalin salsalar masana sani sai rubutu,

Sansanin sada soyayya salima rubutu,

Sashen so da sallaɗuwar sani sai rubutu,

Sassaucin sanar da sani a sauƙi da Hausa.

 

Ƙungiyar marubuta,

Da maza har da mata,

Masu saitin zukata,

Na mai karatu da Hausa.

 

Mu muke faɗakarwa,

Da nishaɗi na baiwa,

Mai isarwa da annashuwa,

Da ta zarci gasa.

 

Soyayya da tarbiyya ta sa wa a hanya,

Hanyar yaye jahilci ga yara da manya,

Yiwuwar yane yanga yayyafin soyayya,

Hanyar yaɗa wayewa da yaɗo na Hausa.

 

 

Darajar marubuci,

Masani mai azanci,

Ta fa zarci,

Ta duk wani mai sanarwa da Hausa.

 

Gaisuwa ta da jinga,

A gurin Paul mai ganga,

Ka biya ni da ganga,

Ina ta waƙa da Hausa.

Daga Diwanin Waƙoƙin Aminu Ladan Abubakar (ALA)

Post a Comment

0 Comments