Ticker

6/recent/ticker-posts

Inuwar Marubuta Jihar Arewa Da Hausa

Yakasai, S. A. & Sani, A-U. (2021). Diwanin Waƙoƙin Aminu Ladan Abubakar (ALA)Kaduna: Amal Printing & Publishing Nigerian LTD. ISBN: 978-978-57624-9-0.

Amshi

Inuwar marubuta jihar Arewa da Hausa,

Masu burin karade ƙasar Afurka da Hausa.

 

Inuwar marubuta.

Masu zance da Hausa,

Sui rubutu da Hausa,

Ai karatu da Hausa,

Su yi waƙa da Hausa

Don talla ta Hausa.

 

Manufar marubuta tallatar harshen Hausa,

Ƙudurin marubuta yaɗa al’adar Hausa,

Burikan marubuta yaɗa dini da Hausa,

Nasarar marubuta mamayar harshen Hausa,

Tambarin marubuta a ji yare na Hausa,

Cinikin marubuta ilimi a yi da Hausa,

Ɗaukakar marubuta k’ ina a ji Hausa,

Ya zamo marubutan jihar Arewa da Hausa,

Sun karaɗe Arewa da duniya duk da Hausa.

 

 

 

Nai salati a cure,

Manufata a ɗaure,

Inda matsayi ya tare,

Koko in ce ya cure,

Wanda shi ke da sunnoni ciki har da aure.

Wanda shi ne ya jure fagen kira babu wasa.

 

Assalin salsalar masana sani sai rubutu,

Sansanin sada soyayya salima rubutu,

Sashen so da sallaɗuwar sani sai rubutu,

Sassaucin sanar da sani a sauƙi da Hausa.

 

Soyayya da tarbiyya ta sawa a hanya,

Hanyar yaye jahilci ga yara da manya,

Yiwiwar yaye yanga yayyafin soyayya,

Hanyar yaɗa wayewa da yaɗo na Hausa.

 

Darajar marubuci na da ɗimbin karamci,

Masani mai azanci ya wuce gidadanci,

Falalar marubuci da ke nazar da azanci

Ta fa zarci ta duk wani mi sanarwa da Hausa.

 

Ƙungiyar marubuta mai maza har da mata,

Sun zamo makarantar masu saitin zukata,

Ɗauki koyi da kanka kamar kana makaranta,

Sun tafi da nishaɗi na mai karatu da Hausa.

 

Mu muke faɗakarwa da nishaɗi na baiwa,

Ba hululi muke ba cikin sanin illimarwa,

Bisa doron ta'ada muke zubin faɗakarwa,

Da isar wa da annashuwa kira babu wasa.

Daga Diwanin Waƙoƙin Aminu Ladan Abubakar (ALA)

Post a Comment

0 Comments