Ticker

6/recent/ticker-posts

Tambarin Masoya

Yakasai, S. A. & Sani, A-U. (2021). Diwanin Waƙoƙin Aminu Ladan Abubakar (ALA)Kaduna: Amal Printing & Publishing Nigerian LTD. ISBN: 978-978-57624-9-0.

Amshi 

Sai da so da ƙauna ake shiri na aure,

Ga tambarin masoya ranar bikin amare.

 

Shimfiɗa

Abin farin ciki ne,

Abin a wa yabo ne,

Abin a wa kiɗa ne,

Bikin badujala ne,

Bikin na begilan ne,

Bikin sarewuka ne,

Bikin na assali ne,

Bikin kayan karau ne,

Bikin asin asin ne,

Bikin acan acan ne,

Bikin na mai ido ne,

Wannan bikin amare.

 

Ubangijin sarauta mai juya yau da gobe,

Abin yabo da gode ‘yanci na so da zaɓe,

Wannan da ke da ƙarya takenta yau da gobe,

A kwan a tashi yanzu ana gaba ta aure.

 

Mai Makka mai Madina tsani na masu aure,

Annabi ɗan Suwaiba sunnarka ce fa aure,

Muna riƙo da sunnar zuwanmu ce fa aure,

Allah ka ƙarfafawa waɗanda sun ka aure.

 

Aure na so da ƙauna a kai a yau masoya,

Aure a kai na manya a ɓangaren masoya,

Aure gidan Mayere ɗiyan gida na manya,

Maryama an yi dace a yau ake fa aure.

 

Yayan uban gidana mai darraja ta farko,

Baba Lawal Mayere da al'uma ta ɗauko,

Bikin ga yau na yi ne ku bar ni in yi sakko,

Na je da tamburana nai jinjina ta aure.

 

Na gane an yi dace Maryama na da lura,

Fitar kamar wata ne samaniya da zarah,

Abin ƙawa da kallo na hankali da lura,

Ɗagwas! Ɗagwas!! Abinku ana biki na aure.

 

Kama da gajimare fiton ango amarya,

Suna tafe a jere a sannu babu zarya,

Kowansu yai adon ɗas!! Dukansu babu ƙarya,

Wanne ya zarci wanne ana biki na aure.

 

 

 

 

Duk inda kai da kallo sarewuka ka tashi,

Sannan amon maroƙa da sautuka ka tashi,

Sautin kiɗan amare da dumdufa da taushi,

Suna faɗin amarya Maryama ta yi aure.

 

Duk inda kai da kanka ƙamshi kawai ka tashi,

Da ɗai ba attabai ba irinsa wanga ƙamshi,

Asin asin da gwal ne na arziki da ƙamshi,

Bikin gidan Mayere uba wajen amare.

 

Uwa abar kulawa Fati uwar amarya,

Hajjaju Fatima Mayere uwar amarya,

Uwa maba da mama Fatima mai abaya,

Ranar farin ciki ce abar yabon amarya.                 

 

Mama Fatima sannu farar uwa 'yar Fulani jinsin kirki,

Ke uwa ce mai shayar da ɗa babu cuta babu ko miki,

Mai kishirwa za ya taho ya sha ba gazawa ba kya raki,

Ga ɗiyarki za ta gidan miji Allah sa tai gado naki,

Ta yi tausai jin ƙan jamma'a ta yi koyi duk da halinki,

Allah kyautata wannan aure ki ga ‘yan jikoki naki.

 

Janaral PMB na ƙasa baba ka sauke nauyinka,

Ladabi da ka bai wa ɗiyar daga yau ka sauke hakinka,

Rayuwa ta ɗiya mace an sani farkonta yana a wuyanka,

Rayuwa ta ɗiya mace an sani na biyunta a gun sirikinka,

Rayuwa ta ɗiya mace an sani ta uku ko tana gun jika.

Ga ɗiyarka ta nufi aure addu'arka ta sam albarka

Daga Diwanin Waƙoƙin Aminu Ladan Abubakar (ALA)

Post a Comment

0 Comments