Ticker

6/recent/ticker-posts

BBC Hausa

Yakasai, S. A. & Sani, A-U. (2021). Diwanin Waƙoƙin Aminu Ladan Abubakar (ALA)Kaduna: Amal Printing & Publishing Nigerian LTD. ISBN: 978-978-57624-9-0.

Amshi 

BBC Hausa hantsi leƙa gidan al'umar duniya,

BBC Landon gamzaki mai fita da subahi duniya.

 

Shimfiɗa

Ruwan dare mai gama duniya,

Kafar sadarwar duniya,

Kafar horarwa duniya,

Suna rikiɗa ya hawainiya,

Kore shuɗi ko rawaya,

Fari da baƙi ba tsirkiya,

Fagen sadarwa ka jiya,

Kawai ka kira su da zawiya,

A kan sadarwa tun jiya,

Ko ma ka kira su da maliya,

Kafar sadarwar duniya.

 

BBC Landon ninetin fifty-seɓen suka fara,

BBC Landon har kawo yau ba su da tsara,

Kafar sadarwa babu kamarta a fanni cara,

BBC Landon sai a kira ta ruwan dare mai gama duniya.

 

Kafar sadarwa ko ka kira ta kafar horarwa,

Saboda ƙwarewa ne na kira ta kafar horarwa,

A nan aka horon mai fikira a fagen sadarwa,

Madubin duban dukka tashoshin sadarwa nan duniya.

 

Bisa kirdado waɗanda sun ka jin BBC,

A ɗan takadirin yawa na masu jin BBC,

Million ashirin ne da ukku masu jin BBC,

Kadan takadiri a nahiyar ƙasashen faɗin duniya.

 

Suna daidaito da zamani kafar BBC,

Suna sadarwa  da radio BBC,

Kafar internet da shafuka na zumunta BC,

Duk sun sinkake duk watta da'irar sadarwar duniya.

 

Cikin manufofi manya na wanzuwar BBC,

Suna aiki ne don kare ra'ayi BBC,

Muradi haƙƙin al'umma tai tashar BBC,

Suke karewa shi yas saka ake ƙaunar su a duniya.

 

Kawai BBC tamkar majama'ar al'uma,

Kawai BBC tamkar matankwarar al'uma,

Kawai taska ce rumbu ma'adanar al'uma,

Kafar hujja ce sashe na massana ilimin dud duniya.

 

BBC Hausa ƙasurgumai da ba na biyunsu,

Fagen labarai koko programe tsarinsu,

Musamman hira fannin da na ji babu kamarsu,

Da sun tattauna ɗan lokaci kaɗan ta zagaya duniya.

 

Hakan ya tuna min hira da Umaru 'Yar Aduwa,

Da Mansur Liman yay yo da shugaba 'Yar Aduwa,

Hirar da ta zamto sha kundum a kafar sadarwa,

Hirar su Naziru Mika'ilu da A’isha ta gama duniya.

 

Nazir Mika'il hira ta sa da A’isha Buhari,

Ta zammana topic duk inda kai ana ta sururi,

Matsawar BBC sashen Hausa ta kalli umuri,

Shi za a yi yayi duk inda kab bi saƙo lokon duniya.

 

 

 

Da Turawa ne ke sarrafa BBC Hausa,

Isa A. Abba shi ne na fari sashen Hausa,

A jinsin mata Hajja Jamila Tangaza ta gama duniya.

 

Shirin BBC wanda ake na labarina,

Shirin BBC a karkara da yai karakaina,

Dukan su Jamilat Tangaza ce take ta bayana,

A birni ƙauye ba inda ba a amfana ba a duniy

Daga Diwanin Waƙoƙin Aminu Ladan Abubakar (ALA)

Post a Comment

0 Comments