Ticker

6/recent/ticker-posts

9.4 Liɓerty 'Yanci Kaduna - Daga Diwanin Waƙoƙin Aminu Ladan Abubakar (ALA) (Page: 461)

Yakasai, S. A. & Sani, A-U. (2021). Diwanin Waƙoƙin Aminu Ladan Abubakar (ALA). Kaduna: Amal Printing & Publishing Nigerian LTD. ISBN: 978-978-57624-9-0.

Amshi

Tashar Badangalci Radio da ,

Tasha ta liɓerty 'yanci Kaduna.

 

Shimfiɗa

Idan dara za a yi kai uwa a gefe,

Kun san tashar liɓerty fa babu gefe,

Domin tashar liɓerty tana da fefe,

Wajen balansin fadi gaskiya da fefe,

Idan suna tufka warwara a faife,

Suna zagwanyar da baƙin hali a gefe,

Kamar ana bandar giwa a ƙarfe,

Ɓera ya na fince nai ta gefe-gefe,

Auren gidan girma dole a yi da lefe.

 

Ubangijin iko mai raba wa kowa,

Sarkin da ba shi riƙon shamaki da barwa,

Na gurguso Allah don ka ƙara baiwa,

In waƙe liɓerty ta jihar Kaduna.

 

Duk ɗan Musulmi in yai nufi umuri,

Sunan gwani Allah za ya sa a fari,

Sannan salati gun rahatul suduri,

Manzonmu mai rauda a garin Madina,

 

Allahu kai ƙari na dubun salati,

Gare shi manzo mai kyan hali da zati,

Haɗa sahabbai nai har da ali baiti,

Waɗanda ƙaunarsu ta zamo jinina.

 

Rana idan ta fito rahama ga kowa,

Rana mudun aiki ta zame wa kowa,

Waɗansu na shanya wassu na tulawa,

Take na liɓerty ta jihar Kaduna.

 

Mai tambarin ‘yanci liɓerty Kaduna,

Haki na al'uma liɓerty Kaduna,

'Yanci na radin kai liɓerty Kaduna,

Damar faɗin ra'ayi liɓerty Kaduna.

 

Suna da nisan zango daga Kaduna,

Ana ganin su da ji duniya sanina,

Afurka na saurara daga Kaduna,

Kun dai ga antainar na jihar Kaduna.

 

Saboda kayan sautinsu mai nagarta,

Kaya na zamani mai game maƙota,

Saboda kyan sauti liɓerty ta keta,

Ta keta tsarori tsarakin Kaduna.

 

Idan na ɗau hanya na baro Kaduna,

Rigacikum ta zam tazzara Kaduna,

Da marraba Birnin Yero jaji kana,

Anan nake gane liɓerty Kaduna.

 

Idan na ƙara taki farakwai igabi,

Kan ma na kai zangon ayya ta igabi,

Daidai wajen da ake yaka sayyi zabi,

A nan ake rarrabe liɓerty Kaduna.

 

Kafin tashar Yari in ɗan yi makku kara,

Anan ake gane zakkara da cara,

Da na fa canza tasha ta ishen da ƙara,

Dan dole liɓerty zan ji a Kaduna.

 

Duk inda nak kama shu take na ƙara,

Ba ka fahimta balle ka ɗan sarara,

Da otimatic serching ya kai na lura,

Sai dai ya dawo kan liɓerty Kaduna.

 

 

 

One O three dot one liɓerty Kaduna,

Sashe na Hausa Zalla tashar Kaduna,

Da ninety-two point one liɓerty Kaduna,

Sashe na Turanci liɓerty Kaduna.

Daga Diwanin Waƙoƙin Aminu Ladan Abubakar (ALA)

Post a Comment

0 Comments