Ticker

6/recent/ticker-posts

CTV

Yakasai, S. A. & Sani, A-U. (2021). Diwanin Waƙoƙin Aminu Ladan Abubakar (ALA)Kaduna: Amal Printing & Publishing Nigerian LTD. ISBN: 978-978-57624-9-0.

Amshi

CTƁ take murna an naɗa Mallam Sardauna,

CTƁ muna murna an naɗa Mallam Sarduna.

 

Allan nan da ake bauta,

Mai kyauta ya maimaita,

Mun roƙa ka hamaimaita,

Ka amsa ka maimaita,

Yau kuma ga shi muna bita,

Ka naɗa Mallam Sardauna.

 

Mallam ya yi halin barka,

Masoyansa suna barka,

Maggautansa suna barka,

Aikin solo idan barka,

Tsofaffinmu suna barka,

Manya yara ‘yan mata.

 

Allah ka san manufarmu dan murnar naɗa Sardauna,

Babu abin da ya damemu sai murnar wannan rana,

Allah mai kyautar mulki mun gode maka Sarkina.

 

Taro ya yi ƙwari ta cika don murnar naɗa Sardauna,

Na ga matsatstsaku mai baki duk a jikinta ta na gunna,

In dai karkata shi baki nan ya wuyanka gun juna.

 

Ɗan gado nake kan aure ba gado a sana’u na,

Ta ka kai sama suna na harƙar zay ya na waƙe na,

Madallah daba jikan bayi Allahu maƙagi na.

 

CT bin mu tashar girma alfarmarku muke murna,

Ku ne taskar tarihi kuke taskace saƙona,

Yau ma ga shi muna murna an naɗa Mallam Sardauna.

 

 

CTƁ nake kallo ‘ya‘yana har matana,

CTƁ abar kallon kowa har da abokaina,

CTƁ tashar girma mai alkinta ta’aduna.

 

Marmaza kui dakwamentin ol tarihin naɗa Sardauna,

Ga Sarki da Sarakunnan Arewar mu da ko a ina,

Ga gwamnoni sun zoz zo murna dan naɗa Sardauna.

 

Ni ma na buga kugena na kuma doki kalanguna,

Kowa nawa yana murna har ‘yan amshi yarana,

Ga Sarki na kalangu Laku-laku kaɗa ganguna.

Daga Diwanin Waƙoƙin Aminu Ladan Abubakar (ALA)

Post a Comment

0 Comments