Ticker

6/recent/ticker-posts

AM FM

Yakasai, S. A. & Sani, A-U. (2021). Diwanin Waƙoƙin Aminu Ladan Abubakar (ALA)Kaduna: Amal Printing & Publishing Nigerian LTD. ISBN: 978-978-57624-9-0.

Shimfiɗa

AM FM,

Nishaɗantarwa.

 

FM AM,

Maisantuwa.

 

AM FM,

Tallatarwa.

 

FM AM,

Kwai gamsarwa.

 

AM FM,

Sauƙaƙawa.

 

FM AM,

Armasawa.

 

AM FM,

Rediyon Kano.

 

Amshi: AM FM rediyon Kano babbar magana,

AM FM rediyon Kano ga mu nan zuwa.

 

FM AM rediyon Kano,

Babbar magana.

 

FM AM rediyon Kano,

Hana kukan yaro.

 

FM AM rediyon Kano,

Babbar shigifa.

 

 

FM AM rediyon Kano,

Sha ƙundum ku jiya.

 

FM AM rediyon Kano,

Mai farar aniya.

 

Ga fili ga doki ku zakuɗa mu ga mai ƙwazon tafiya,

Wani kaya sai amale raƙumi a fagen tafiya.

 

Ka haɗa kaya ka ɗaure,

Amma ba wurin zuwa.

 

FM AM rediyon Kano,

Maryam can naka zuwa.

 

Alan waƙa me za ka yo,

A AM FM rediyon Kano?

 

Zan je na kai talla,

Ya karaɗe lardin nan na eriyar Kano.

 

FM AM rediyon Kano,

Farkon farawa jahar Kano,

Sanya ji amon mutan Kano,

Ko wa’azi tarwai daga Kano,

Ko tallar hajan mutan Kano,

Ya karaɗe jahohin Kano,

Kanun labarai daga Kano,

Al’adar Hausa ta Kano,

Tarihin Hausa a Kano,

Harshen Turanci a Kano,

Wazobiya a Kano,

Wasan barkwanci mutan Kano,

Haɗe kan al’umma a Kano,

Ba ƙabilanci a Kano,

FM AM rediyon Kano,

Ga mu nan zuwa.

 

Ba sa kirdado a wurin faɗin labarai,

Rediyon Kano.

 

Ba sa hasashe a wurin bayanai tsantsa,

Rediyon Kano.

 

Ba sa kintati a wurin kanu na labarai,

Tashar Kano.

 

Ba sa shaci faɗi sai sun bi kanu an tace,

A Kano.

 

Su suaka kere sa’a a nisan zango saƙo don a jiya,

Maso biɗar aike garzaya tashar AM tafi ba tambaya,

Su suka ba maraɗa kunya wurin labarai ba tirjiya,

AM FM rediyon Kano,

Ga mu nan zuwa.

 

Sakkwatawa,

Zamfarawa,

Katsinawa,

Daga can sai ka jiya.

 

Zazzagawa,

Barnawa,

Tarabawa,

Mun kai tun tun jiya,

 

Nasarawa,

Da Jigawa,

Ga Jasawa,

Su ma duk sun jiya.

 

Kudawa,

Arewawa,

Daɗa kalmarmu ko’ina an jiya.

Daga Diwanin Waƙoƙin Aminu Ladan Abubakar (ALA)

Post a Comment

0 Comments