Yakasai, S. A. & Sani, A-U. (2021). Diwanin Waƙoƙin Aminu Ladan Abubakar (ALA). Kaduna: Amal Printing & Publishing Nigerian LTD. ISBN: 978-978-57624-9-0.
Amshi
Amana radio ta badangalci da ta kere tsara,
Amana a riƙe ta gadon barci in har da lura.
Buɗewa
Hazaƙa ko nagarta,
ƘwArewa ko bajinta,
Karimci ko ba jigata,
Salama babu ƙeta,
Adon harshe bajinta,
Fasaha tsaggwaronta,
Amana sun naƙalta
Amana radio ta badangalci kau ba irinta,
Zalaƙa ce nagarta mui aniya ba ta da tsara.
Hazaƙa ko nagarta.
Amana radio ce.
ƘwArewa ko bajinta,
97.5 Amana
Karimci ko ba jigata,
Amana radio ce.
Salama babu ƙeta,
97.5 amana.
Adon harshe bajinta,
Amana radio ce.
Fusaha tsaggwaronta.
97.5 amana.
Amana sun naƙalta.
Amana radio ce.
Amana radio ta badangalci kau ba irinta,
Zalaƙa ce nagarta mui aniya ba ta da ƙura.
Amana radio sawun giwa mai ɓad da saura,
Amana in ka kunna sai tsara su zamo a saura,
Fage na nishaɗuwar rai kunna amana ka sarara,
Amana radio FM da a yanzu ta tsere tsara.
A fannonin ƙwarewa babu kamarta fagen ƙwarewa,
Fagen aikin nagarta ba ya amana kan ƙwarewa,
Da gogaggu ƙwararrun masu gudanar da ƙwarewa,
Ina mai talla ga dama zakara ya ƙwalla ƙara.
A nanti sabin foyin fayif za ku ishe mu tashar amana,
Mita casa'in da bakkwai sai fa ɗigo da biyar amana,
Muna dijital a sauti dibidi radio amana,
Da inganci na sauti mun fintinkau ba mu tsara.
Fagen da ta tsere tsara masu shirin adabi suna nan,
Shirin adabi na Hausa babu kamarmu a nahiyar nan,
Da al'adun Arewa tarihi na sarakunan nan,
Da 'yancin tallakawa haƙƙoƙi na kira da kara.
Da labarun nagarta ban da na shaci faɗo na ƙarya,
Da labarun kasashe har na kasarmu Nijeriya,
Shirinmu kakaf a tsare komai namu tsatsaf ku shirya,
Na ce tafiyar sahara sai su amale saboda ƙura.
0 Comments
ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.
HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.