Ticker

6/recent/ticker-posts

8.7 Dutse Gadawur - Daga Diwanin Waƙoƙin Aminu Ladan Abubakar (ALA) (Page: 400)

Yakasai, S. A. & Sani, A-U. (2021). Diwanin Waƙoƙin Aminu Ladan Abubakar (ALA). Kaduna: Amal Printing & Publishing Nigerian LTD. ISBN: 978-978-57624-9-0.

Amshi

Birnin Dutse ne na Gadawur tushen talifi,

Ko a cikin birane Dutse Gadawur na gaba.

Jagoran maza uban tafiya sarkin gari,

Nuhu Muhammadu Sanusi abin alfahari.

 

Ya Hayyul Kayyumu ya Tabara abin bauta ɗaya,

Mahalicci dai kake a rububiya da ƙuluhiya,

Ya Buwayi ina riƙon asama'ullahi gaba ɗaya,

Ka yi mani lamuni a abin da na tsara zan biya.

 

Nai riƙo da abin riƙo da aminci babu batun riya,

Gaisuwa ga abin yabo Mahamudu abin ai kwaikwaya,

Ali har asahabihi da suka riƙe hanyar gaskiya,

Rabbu na yi tawassali so da ƙauna kana da bibiya.

 

Nai nufin diga dan mafari yabo na nufata na kattaba,

Zani wake garin Dutse Jigawa yabo ba aibu ba,

In ka ɗauke ummul kura Makka Madina a kan gaba,

Ban ga tamkar Dutse ba bini sannu ka deɓe fargaba.

 

 

An hasashe duniya wai Abuja tana a sahun gaba,

A cikin jerin birane da sunka yi saurin cigaba,

Haka Dutse Jigawa ma a ƙasarmu ba ay yi kamarta ba,

Hauhawa ga cigaba arzikin jama'a ba a kai ta ba.

 

Ga tsohon tarihi a ƙasar Dutse mai armashi,

Na mulkin tale tale Dutse ta cika birnin armashi,

Garurran tarihi na ƙasan mulkin Dutse da shi,

Za ni kira su yau babu su tarihi bai yi ba.

 

Fari ga sarkin gari liman na gari fa uban gari,

Sarkin yaƙin gari gagarau makasau cigari,

Rawani da amawali tunkume Akaram sarkin gari,

Nuhu Muhammadu Sanusi abin alfahari.

 

Mai asarki farin gani mai halin a yaba ba kyankyami,

Masani kan zamani, masanin kur'ani ka'imi,

Adali jigon gari ginshiƙin talaƙawa jarumi,

Nuhu Muhammadu Sanusi jakadan malami.

 

Garin mulki a Dutse da garu da kachi na kattaba,

Limawa Galamawa da Gwari yina na zuzzuba,

Jugurgur Maranjuwa ba zan wuce ko da ɗayansu ba,

Gizirawa Maremawa da Takalafiya gaba.

 

Sauran ƙofar gari goma sha uku ba zan bar su ba.

Fari ga ta Maranjuwa da Yina in har ba ku san su ba,

Ga ƙofar Kokiya ga ta Bukka da Tago a kan gaba,

Ga Ƙofar Ma'ai ga ta Kachi Gadadin na gaba,

 

Ga ƙofar Rariya da Galadimawa shugaba,

Ga ƙofar Burtilan da Galammawa rukunin gaba,

Ƙofofi sun cika sha biyu rikicib na kattaba,

Ƙofar Dutse ne mashigarsu a nan na rattaba.

 

Jigawa ƙasar Dutse a komai ban ga kamarta ba,

Ƙasar noma a Dutse da kiwo ba a ɗara su ba,

Dukkan janibin cigaban zamani ba a fi su ba

Birnin Dutse dai zakka a birane har gaba.

 

Ta yarda garin Abuja ya sami dubunnan karsashi,

Biranen duniya yana a sahun 'yan armashi,

A saurin cigaba ko na ce bunƙasa ba ya shi,

Haka nan Dutse take a jihohi fannin armashi.

 

Ga ƙasa nan shimfiɗe a Jigawa ta noma arziki,

Ai noman hatsi dawa da su shinkafa ciki,

Haka kayan marmari kankana da dabino ba haki,

Ga kyawun gari Dutse ta ɗara tsara tsaraki.

 

Dutse ga ta da arzin masana da fitattun ja gaba,

A kowanne janibin mashahurai za ni na kattaba,

Da sunka riƙe ƙasa a Arewa suna a sahun gaba.

Wasu yau sun ƙaurace duniya wasu na nan zan zuba.

 

Gaisuwa gun jagaba ɗan amanar Dutse abin yabo,

Alhaji Nasiru ɗan amanar Dutse cikin yabo,

Ka zamma gabar rabo a cikin waƙoƙin sha yabo,

Nuhu Muhammadu Sanusi uba babban rabo.

 

Godiya na jaddada a gurin sarki mai martaba,

Da naɗin Nasir Dano ɗan amanar Dutse farin uba,

Allah ya riƙa masa darajoji suy yi awon gaba,

Nasiru ɗan Dkjano ungo mai hana roƙon yan uba.

 

A .B.M  Muktari Muhammad ga ni da jinjina,

Wazirin Dutse ne Muktari Muhammad Jinjina,

 

A tsarin jinjina rukuni na muhimmai zayyana,

Haɗa da abin yabo Alhaji Bashir Dalhatuna,

Mai Girman darraja walin Dutse a jinjina,

 

Alhaji Nasiru Haladu Dano na yi jinjina,

Chairman N.H.D Interbiz na ayyana,

Projects Limited da ya dau nauyi nai zayyana.

Daga Diwanin Waƙoƙin Aminu Ladan Abubakar (ALA)

Post a Comment

0 Comments