Ticker

6/recent/ticker-posts

8.6 Duniya Tana Ruɗa Ni - Daga Diwanin Waƙoƙin Aminu Ladan Abubakar (ALA) (Page: 399)

Yakasai, S. A. & Sani, A-U. (2021). Diwanin Waƙoƙin Aminu Ladan Abubakar (ALA). Kaduna: Amal Printing & Publishing Nigerian LTD. ISBN: 978-978-57624-9-0.

Amshi:

Duniya tana ruɗa ni,

Zuciya ki bar rufta ni

 

Na tashi zan je Birget sai ta mai da ni Tarauni,

Na durƙusa nai zaune yanzu ka ga ta tada ni,

Na yunƙura na miƙe take ka ga ta zaune ni,

Nai gabas ana madallah baya za ta zo mai da ni.

 

Na yunƙura hannun dama sai ta dama yar in yi hauni,

Bare zuciya bar ja na kar ki maida ni majanuni.

 

Zuciya tana ruɗa ni,

Ga ni dai maraya ne ni,

Kuma ga shi nai imani,

Rabbana tsare ruɗani,

In guje kaba sheɗani.

 

Saƙe-saƙe ya kama ni,

Ga tararradi kullum ni,

Wasi-wasi na binne ni,

Ya Mudabbirul zamani,

Ahadun ka kange ni.

 

Zuciyar ga nafsul ammara mai izo da sossoke ni,

Yau tarairayo alkhairi gobe sai tamin umarni,

Yanzu nai hali mai gobe nai hali mai muni,

Yanzu ga mutum tartibi gobe ya zamo majnuni.

 

Ya Ubangiji zulmanni kar ka bar ta ta kada ni,

Sa in dallashe kaifinta kar a san da tai gomarni.


Godiya gurin Mannani,

Mai kaso rabo ya ba ni,

Ya raba da ni imani,

Addu’a a ran tada ni,

Kar na tashi ba imani.

 

Ka haɗo iyayena ni,

Rabbi har iyalaina ni,

Har da malamai rahamani,

Ban cire abokaina ni,

Ka haɗa dasu.

Daga Diwanin Waƙoƙin Aminu Ladan Abubakar (ALA)

Post a Comment

0 Comments