Ticker

6/recent/ticker-posts

8.8 Mahaukaciya - Daga Diwanin Waƙoƙin Aminu Ladan Abubakar (ALA) (Page: 403)

Yakasai, S. A. & Sani, A-U. (2021). Diwanin Waƙoƙin Aminu Ladan Abubakar (ALA). Kaduna: Amal Printing & Publishing Nigerian LTD. ISBN: 978-978-57624-9-0.

Waiyo kaico,

So sa’itina,

Gidan mahaukata na je babu kulawa,

Waiyo kaico,

So sa’itina.

 

Gidan mahaukata ALA yaz zagawa,

Waiyo kaico,

Ya ga babu kulawa.

 

Allahu buwayi mai tasarrufi na,

Nai nufin bayani ka ida nufina,

Karɓi baitukana su isar da nufina,

Sa a karɓi saƙo daga baitukana.

 

Ya Rabbi salatai adadina ƙauna,

Ƙara wa ma’aiki Ɗaha ɗan Amina,

Shugaban adalai Ɗaha Annabina,

Suyidul wujuduna so ka da ƙauna.

 

Gidan mahaukata na je ban koma ba,

Ban sake zuwa ba dan ba zan iya ba,

Abin da na hango ba zan jure ba,

Ban tausai mallam sai ka duba.

 

Abin ai kaico ba ai biris ne ba,

Abin Allah wadai ba an yi kurum ba,

Abin gori ne ba dan cin fuska ba,

Abin gori ne ba dan cin fuska ba.

 

Ni da na kai ziyara ta gani da idona,

A gidan taɓaɓɓu sai da ma na tsani kaina,

Na tuhhumi kaina da ma duk dangina,

Da shugabanni da masu arziƙina.

 

Na tuno halitta ta ɗan Adam jinsina,

Na tuno martaba ta ɗan Adam irina,

Na tuno kamalantaka ta jinina,

Mafi girma a jikina halittar sarkina.

Sai zubar hawaye daga cikin idona,

Har kundukuƙina zuwa gaɓa a tona,

Sai na ji fa kaina yai durum hakannan,

Sai na ji ƙafafu da ƙyar su ɗau jikina.

 

Sai naj ji juwana neman ka da jikina,

Na ta galauniyana samu guna zauna,

Na numfarfashi kamar zai fita raina,

Sai naɗ ɗaga kaina na roƙi Ubangijina.

 

A gidan taɓaɓɓu babu kula ta ƙauna,

Ba shi da yalwa ba ɗakunana kwana,

Ba abinci ba magani ku je ku tona,

Waiyo Allana ya Ubangijina.

 

Sai na hau tunani ina saƙa a raina,

Matsala ta hauka bawa me yai tukunna,

Maikuɗi da bayi guri guda ka zauna,

Talaka da mai arziƙi a gunka zauna.

 

Ni sababina hauka daban-daban sanina,

Wani aljanu ne ke taɓa shi sanina,

Wani tsafe-tsafe da sanbakal sanina,

Wani aksident ne ku duba ku tunana,

Wani karrayar arziki a kan sanina,

Wani ko kwatar mulki ‘yan uwa sanina,

Wani zazzaɓin taifot yake taɓa shi jina,

Wani muttuwar sahibi na so da ƙauna,

Wani ko tsiron basir ƙarƙashin shinana,

Wani sammu ke kai shi gurin ya je zauna,

Wani addu’o’in gidoga a sanina,

Wani rantsuwar ƙarya ƙarƙashin sanina,

Wani bakin mutane zauta shi sanina,

Wani kambum baka ni ƙarƙashin zatona,

Wani fushin iyaye ke zauta shi sanina,

Wani hakin marayu ƙarƙashin sanina,

Wasu miyagu na ƙwayoyi a sanina,

Wani baliyon wani banalin ka sa shi ɓarna,

Wasu ko ta shaƙar koken ka sa su ɓarna,

Ya Ubangijina mai tasarrufina,

Ka ida nufina,

So sa’itina.

 

Dan zubar hawaye yai jajur idona,

Baƙin ciki ya maye gani da jina,

Sai na ji ana hira a sama-sama a kaina,

Nai zubur na tashi nutsuwa ta wanzu a guna.

 

Jami’ai na hanga na gwamnati a idona,

Sun iso ziyara a ƙarƙashin zatona,

Na matsa gare su don in kare zatona,

To ashe mutanen gari ne iri-irina.

 

Wata ƙungiya ce ta sanya kai ganina,

Masu tallafawa mahaukata ganina,

Sakatar allebiyetion asosiyeshin na,

‘Yan uwa shaƙiƙai a bai wa ɗan yabona.

Na ga tambarinsu da logonsu na ƙauna,

A cikin baka PAAN aka zana,

Sai na je gare su da tambaya ta ƙauna,

Suka bayyana min manufarsu ta ƙauna.

 

Sai na ji farin ciki ya ɗarsu a raina,

Sai na ji dirar so da ƙauna duka a raina,

Sai nai ajiyar zuciya na hir da kaina,

Sai nai ta hamdala gurin Ubangijina.

 

Sun taho da kyauta ta temako da ƙauna,

Sun taho ziyara a ƙarƙashina ƙauna,

Hauhawa yake yi farin ciki a guna,

Dole nai rijista da su a don ƙauna.

Daga Diwanin Waƙoƙin Aminu Ladan Abubakar (ALA)

Post a Comment

0 Comments