Ticker

6/recent/ticker-posts

8.3 Ala: Basasa - Daga Diwanin Waƙoƙin Aminu Ladan Abubakar (ALA) (Page: 392)

Yakasai, S. A. & Sani, A-U. (2021). Diwanin Waƙoƙin Aminu Ladan Abubakar (ALA). Kaduna: Amal Printing & Publishing Nigerian LTD. ISBN: 978-978-57624-9-0.

Amshi: Allah muna ta yin raka’o’i,

Sannan muna ta yin addu’o’i,

Tsare mu rikicin basasa,

Ya Zaljalalu ba dan mu ba.

 

Ya Zaljalalu da tsarkinka,

Domin kaɗaita karzatinka,

Domin mu tsarkakan sunanka,

Ba dan isar mu ko bauta ba.

 

Da sau da bibiyar manzonka,

Wanda ya ida saƙo naka,

Habibu Mustafa Manzonka,

Da bai yi ma gamin bauta ba.

 

Tsoro da firgici ya ci mu,

Ya ta da hankulan kowanmu,

Birni da karkarun lardinmu,

Ba kwanciya ta hankulla ba.

 

Masu hada-hadar harkoki,

Wasu zama suke na makoki,

Ba nutsuwa bare su yi aiki,

Ba wai da hankula sun so ba.

 

Rannan na tashi za ni ziyara,

Domin zumuntaka ko kara,

Kwana guda kawai na tsara,

In zo gida fa ban komo ba.

 

Sai na ji ana an fara,

Gudu ake kwatancin fara,

Ɗan jim kaɗan sai gobara,

Ta ko’ina idan kai duba.

 

Kan mai uwa da wabi ake,

Harbi das sare-sare ake,

Gudu nake kwantacin falke,

Ban san fa inda zan dosa ba.

 

In an raka waɗannan haka,

Da an jima kaɗan jim haka,

Suma su ɗauki sandan duka,

Ko jinjiri ba sa kyale ba.

 

Wani ka hangi an kamo shi,

Ana ta ja a ƙas sai nishi,

Sara ake yana ihu shi,

Kan a jima ba zai motsi ba.

 

Wani da ransa ka hango shi,

An masa da’irar garwashi,

An sa wuta da taya kanshi,

Ba za a bar shi yai motsi ba.

 

Da jami’an tsaro sun kunno,

Sai duk a tarwatse sun danno,

Sai harbe-harbe ƙarar kwano,

Da kashe wuta take yi ba.


Ni dai kawai ina bin dangi,

Na sarƙafe su tamkar dagi,

Ni ma a hannu na ɗau dagi,

Ba dan na doki kan kowa ba.

 

Ba mai kula da ya ci abinci,

Ina ka gan shi balle ka ci?

Ga masu raunuka na kwanci,

Wasu da nan ba sa tashi ba.

 

Kwana biyu da yini baba,

Haka na yi fa ban karya ba,

Yunwa tana kisan ɗan baba,

Ga harzuƙa uba har baba.

 

Ka ga uwa tana fasa kuka,

Kaga uba yana fasa kuka,

Sun ga ba layira ba duka,

Ƙ ofar rago ba su hango ba.

 

Sai dai in ce da kai la haula,

Wala ku wata illa billa,

Jini kawai ake ta malala,

Ba rikicin aka ƙare ba.

Daga Diwanin Waƙoƙin Aminu Ladan Abubakar (ALA)

Post a Comment

0 Comments