Ticker

6/recent/ticker-posts

8.2 Al’adun Hausa - Daga Diwanin Waƙoƙin Aminu Ladan Abubakar (ALA) (Page: 391)

Yakasai, S. A. & Sani, A-U. (2021). Diwanin Waƙoƙin Aminu Ladan Abubakar (ALA). Kaduna: Amal Printing & Publishing Nigerian LTD. ISBN: 978-978-57624-9-0.

A kaɗa a raya mu 'yan Arewa ba za mu ki kalma ba.

Nakasa mu ake sanadin ba mui dace da iyaye ba,

Cutar mu ake sababin ba mui dace iyaye ba,

Halaƙa mu ake asalan ba mui dace hukuma ba,

Kyarar mu ake manufa ba mui katari da sawaba ba,

Binne mu ake fa kawai da rayukka ba mu gane ba.

 

Riga ta aro malam ba ta zama walki ba,

Wando na aro malam ba zai zama walki ba.

 

Dode katara malam sai ka yi abin kanka,

Kai ka zama hankaka ba ka koyin kanka.

 

Sai mun riƙe al'ada sannan a ga kimarmu.

 

Sai mun riƙi al'da ne ma kai banyenmu.

 

In ba mu da al'ada me za mu gwada namu?

 

Busa mani kukuma don zan yi ta'adunmu.

 

Adabinku madubinku in kun ci gashin kanku,

Sa'in da kuke kira ai kun ci gashin kanku,

Ku ke da diga garma har ma da fatanyunku,

Kun kera kurada har da gizagon saranku.

 

Zangon da muke ƙira,

Loton da muke saƙa,

Sa'in da muke jima,

Da can da muke noma,

Kiwo da fataucinmu,

Mun kau da zaman banza,

Mun kere sa'a malam.

Ba mai taɓa dangarmu.

 

Da barin al'adunmu lalacewar ta kai an ɓata kamar Hausa,

Yau Hausawa babu kama da rigarsa ba ka gane Hausa,

Mun zamma alankosa ba ma kishin kanmu barci tamkar kasa,

Riga ta aro mun sa kullum sai sa-in-sa nauyinmu kamar tasa.

Daga Diwanin Waƙoƙin Aminu Ladan Abubakar (ALA)

Post a Comment

0 Comments