Ticker

6/recent/ticker-posts

8.4 Zariya Gidan Ilimi - Daga Diwanin Waƙoƙin Aminu Ladan Abubakar (ALA) (Page: 394)

Yakasai, S. A. & Sani, A-U. (2021). Diwanin Waƙoƙin Aminu Ladan Abubakar (ALA). Kaduna: Amal Printing & Publishing Nigerian LTD. ISBN: 978-978-57624-9-0.

Amshi:  Zariya gidan ilimin arabik da ma zamani,

Zariya gidan ilimin arabik da ma zamani.

 

Allah abin yabawa a abin riƙo lazimi,

Na karkato da waƙar ahlin gidan ilimi,

Da ma a ce na zamto maalam ko ɗan malami,

Da ka ji baitukana a zuba kamar magani.

 

Alhamdu zance da kai Allahu ya Rahimi,

Ka ban aron fasaha da ta mai dani malami,

Ka ƙara ƙaran wata ta sa na ƙara ƙaimi,

Yadda anka juyan ya zamo ana bi da ni.

 

Ga gaisuwa ga yabo ga Aminu Ɗan Amina,

Abin yabo annabi baban Faɗima Nana,

Da alu as sahabi ataba’u malamaina,

Da masu son annabi na jiya da ‘yan zamani.

 

Na karkato baituka da gidaddajin ilimi,

Na zaiyano malaman Zazzau gidan ilimi,

Ku ɗan jiyo talibin Zazzau gidan ilimi,

Zai sa ku yo salati ku haɗo du’ai  da ni.

 

Da ka ji an ce da kai Zariya gidan ilimi,

Ka so gida na ilimi ko na tashar ilimi,

Zuwa gida na liman Gauɗo kafar ilimi,

Zuwa gidan su liman Ja’e ilimin addini.

 

Cikon gidaje biyar a gida gidan ilimi,

Gidan na liman Durum makwankwaɗar ilimi,

To sai na sanyo gidan Zagezagen ilimi,

Makarkara ilimi daga Daura har zamani.

 

 

 

Ko da batun ilimi na tsaya ku shaide ni ni,

Ya kyautu in yo yabon Zazzau in yo dalauni,

In shirya baitin yabo in yi ya riskar da ni,

Cikin zukatan mutan Zazzau su saba da ni.

 

Zan waiwaya mashigar Zazzau da ba aibu ba,

In zana ƙofar garin Zazzau in kakkattaba,

Ka ji su ƙofar Takwarbai duk in rarrattaba,

Farko da Kwarbai da ƙofar Kona aka ce da ni.

 

Gami da ƙofar Galadima cikin baituka,

Haɗa da ƙofar Gayan a cikin sahun baituka,

A sa da ƙofar Kuyan bana ba ragi na ɗaka,

Ƙofar Kowa har da ƙofar Doka duk na sani.

 

Na sa da ƙofa ta Jatau a cikin baituka,

Gami da ƙofar Tukur Tukur na ɗan karaka,

Ka ji fa ƙofa ta Karki da na ɗan karaka,

Mashahuran Zariya na ara su sa magani.

 

Kun ji fa jaddawalin farko gidan ilimi,

Sannan da jaddawali na biyu bayan ilimi,

Kamar shiga Zariya ta shigun ta batse gumi,

Baɗi an haddace sanadin ga har ma da ni.

 

Akwai fa sauran ɗaya da aka gushe ba a guta,

Ta farko ta Jatau sanadi na ba da cuta,

Ta nan ya san mafita aka rarakai ya fita,

Camfi da jita-jita da bushe ta ‘yan zamani.

 

Hallau a jaddawali na uku fagen sana’a,

Zariya gari na noma fa matattagar sana’a,

Zariya mazan su da matansu suna sana’a,

Kan haka na zam jiyau ganau akan ce da ni.

 

 

 

Har wayau a jadawali na uku fagen sana’a,

Zariya garin maɗinka a tiri rini sana’a,

Zariya garin masaƙa ƙira farar sana’a,

Badon Kanon Dabo ba da turun ku ce ne da ni.

 

Zariya gari na yalwa sunansa babban gari,

Ina da masu neman matar zama ta gari?

Zariya ka je da aure sha’aninsu ba garari,

Warwara da fiɗa nake da bugun misali dani.

 

In ka jiyo malami shuhurarsa ƙololuwa,

Gari-gari maluman shahara da faɗɗakarwa,

A sannu kai bibiya Zariya sunka zauwa,

Makwankwaɗar ilimi a cikin su sun ya da ni,

 

Dukan gurin ilimi za ka iske kwai aƙidu,

Da ra’ayoyin daban na mawallfan takardu,

Da ra’ayoyi daban na mawallafan ƙasidu,

Kowa da hujjarsa don ilimin sanin zamani.

 

Da godiya salonken Zazzau ina ɗimaka,

Sanadinku na tattaro ilimi na waƙar baka,

Da salonke dokaji Zazzau jinjina an dabaka,

Na haɗa da Yusufu Baru dadai kun manta da ni.

 

Sai Alhaji Alhaji Bashari da ya ce da ni,

Bashani gun Buba karkwaso to mai yabon a gani,

Mai ingezuwa da baiwar hikima a juya da ni,

Bashar jinin saraki kada dai ka manta da ni.

 

Ga dan Abubakar mai laƙabi da halin yabo

Mai jinjina ga sarkin na Kano da Zazzau yabo

Na kamala da baitin Zazzau ina a Dabo

Alan Kano da Zazzau kada de ku manta da ni.

Daga Diwanin Waƙoƙin Aminu Ladan Abubakar (ALA)

Post a Comment

0 Comments