Ticker

6/recent/ticker-posts

Du'a'i

Yakasai, S. A. & Sani, A-U. (2021). Diwanin Waƙoƙin Aminu Ladan Abubakar (ALA)Kaduna: Amal Printing & Publishing Nigerian LTD. ISBN: 978-978-57624-9-0.

Rabbana ka tsare ka ƙire Allah kaidi na zamani,

Rabbi alhamdullah, Allah Ka ƙara karewa,

Rabbi na gode, Allah ba zan butulce ba,

Rabbi na gode Allah ba zan mugunta ba,

Rabbi na gode Allah ba zan yi cuta ba.

 

Rabban ka tsare ka ƙire Allah kar in ga saɓani,

Ya zamo Allah ba zan yi kaico ba.

 

Rabbana ka tsare ka ƙire Allah kar in yi ruɗani,

Ya zamo Alan waƙa ba zan yi wayyo ba.

 

Rabbana ka ƙire Allah ƙangi na zamani,

Ya zamo Allah ba zan yi cuta ba.

 

Rabbana ka tsare ka ƙire Allah ruɗi na shaidani,

Ya zamo sarki Allah ba zan yi wauta ba.

 

Ba zan yi cuta ba, Allah ba zan yi wauta ba.

 

Rabbana ka tsare dukkan sharrin jinni wa insani,

Ya zamo Allah ba zan yi hauka ba.

 

Rabbana ka tsare sharri na damuna da sharrikan rani,

Lokacin rani Allah ba zan ga cuta ba.

 

Rabba ka tsare iyayena a wanga zamani,

Su zamo Allah ba su ga kaico ba.

 

Rabbana ka tsare ƙannena ga sharrikan ƙarni,

Ya zamo ruɗin duniya bai hallaka su ba.

 

Rabbana ka tsare masoyana a wanga zamani,

Ya zamo magautana ba su ga lagonsu ba.

 

Rabbana ka tsare abokaina da wanga zamani,

Ya zamo ruɗin duniya bai hallaka su ba.

 

Rabbana ka tsare mai saurarena da ruɗani,

Ya zamo magautana ba su ingije shi ba.

 

Rabbana ka tsare ƙawayena raba su ruɗani,

Ya zamo waƙoƙina ba su gundire su ba.

 

Rabbana Ka tsare yayyena ga wanga zamani,

Ya zamo ruɗin duniya bai hallaka su ba.

 

Rabbana ka tsare harshena da ido abin duba,

Ya zamo al'amurana ban zo da cuta ba.

 

Rabbana ka tsare kiyaye hange tunanina,

Ya zamo hasashena ban zo da cuta ba.

 

Rabbana ka tsare gaɓoɓina zuwa ƙafafuna,

Ya zamo duk motsina ban yo na saɓo ba.

 

Rabbana ka tsare sarki Allah da malumayena,

Ya zamo bayan raina ba zan yi wayyo ba.

 

Rabbana ka tsare abincina da sutturar sawa,

Ya zamo cina shana ba da haramun ba.

 

Rabbana ka tsare ni da hassada cikin sana'una,

Ya zamo harkar aiki ba hassada zan ba.

 

Rabbana ka tsare ganin kaina na issa na girma,

Ya zamo nai martaba ba ji da kai na ba.

 

Rabbana ka tsare 'yan yarana da ke yi min waƙa,

Ya zamo tafiyar da muke ba su yi ta banza ba.

 

 

Rabbana ka tsare 'yan yarana da ke yin min hidma,

Ya zamo ba sui da-na-sani a bibiya ta ba.

 

Rabbana ka kashe mu da ƙaunar Ɗaha Annabin Falala,

Ya zamo aibata aibi ba zai shigo gunmu ba.

 

Rabbana ka zamo ji da ganina a lokacin ƙangi,

Na fi ƙarfin zuciyata mai sani nai kwaɓa.

 

Rabbana ka tsare min lafiyata nai yi ma bauta,

Nai godiya gun ka ba za ni mance ba.

 

Rabbi alhamdulillah, Ka ƙara karewa

Rabbi na gode ma, Allah ba zan butulce ba.

Daga Diwanin Waƙoƙin Aminu Ladan Abubakar (ALA)

Post a Comment

0 Comments