Ticker

6/recent/ticker-posts

8.25 Makauniya - Daga Diwanin Waƙoƙin Aminu Ladan Abubakar (ALA) (Page: 443)

Yakasai, S. A. & Sani, A-U. (2021). Diwanin Waƙoƙin Aminu Ladan Abubakar (ALA). Kaduna: Amal Printing & Publishing Nigerian LTD. ISBN: 978-978-57624-9-0.

Amshi

Na yi gamo da tausayi da cutukan mutuwar tsaye,

Yanar ido amodari, Allahu kai mana magani.

 

Allah gafuru rahimu Allah mai izini a gani a ji,

Wanda ya ƙirƙiri cutuka har maganinsu Ubangiji,

Wanda ya yi ni da kunnuwa da an magana ya yarda na ji,

Allahu yarda da nai kira gurin jama’a kowa ya ji.

 

Ina riƙo da Muhammadu tsanin zuwa bautarKa fa,

Ina riƙo da biyar ɗafa ƙaunar da nai yi wa Musɗafa,

Ka sada saƙon nan da nake kafin a ce na zurfafa,

Ka say a zam gurin jama’a mafakarsu ko bargon rufa.

 

Wata rana ina kishingiɗe a cikin gida don gajjiya,

Tsautsayi ya saka ni ɗaukar rediyo don in jiya,

Tashar Kano na kunna sai na ji hira da daktan idaniya,

Kwanzaltan likitan ido Dakta Hadi don kajjiya.

 

Yai hira daban-daban kan cutuka na idaniya,

Yai bayani kala-kala na rigakafi na idaniya,

Na ji ƙorafe-ƙorafe daga jamma’a ba kushiya,

Koke-koke na jamma’a kan gwamnati zam matashiya.

 

Ran Litinin da safiya na ɗau jakata na rataya,

Ga Laftof don taskace abin da na roro in sakaya,

Ga Bidiyo Kyamara ta ɗaukar abin da yaf fi in tsinkaya,

Ga Ƙalumana da Waraƙa domin rubutun rairaya.

 

Goma na safe a asibiti na Nassarawa ta tarar da ni,

Na tambaya ɓangaren ido ‘Eye Clinic’ aka ce da ni,

Nai aniya Murtala Muhammad Hospital ba bumbuni,

Dakta Hadi yana da aiki na intabiyu da maras gani.

 

Na garzaya don in samu ganawa da Dakta a kauwame,

Ina isa na iske mutane ba adadi ga su kauwame,

Maza da mata yara ƙanana tsoho da tsohuwa a kauwame,

Salo-salo jeri na gwano wasu idanun a ƙyanƙyame.

 

Wani idanu sun fito kamar su faɗo ƙasa haba,

Wani kwa yana da dundumi ta sa shi samko don a duba,

Wani kwa ciwon Amodari girar ido mai ja’iba,

Wasu ko ciwon hawan jinni mai sa idanu kawai zuba.

 

Wasu ɗiya ‘yan jirajirai wasu a goye na tsinkaya,

Wasu a hannu dagwai-dagwai babu idanu don su tsinkaya,

Wani kwa tsoho tukuf-tukuf ko tafiya ma bai iya,

Na ji hawaye yana dira a kunduƙuƙi da idaniya.

 

Nai azama na wuce ciki ina ta’ajibin halin wuya,

A zuciyata ina ta tufka da saƙa wancen da wariya,

Ina ina ma da arziƙi ko ilimi na idaniya,

Da na yi babbar gudunmuwa gurin lalurar idaniya.

 

Na iske Daktan idaniya aiki yake babu gajjiya,

Na bi sahun mara lafiya domin a duban idaniya,

Sannu a sannu har aka zo gare ni domin idaniya,

Nas saka kaina a ƙarƙashin na’urar awon idaniya.

 

 

 

Sakamakon da ya ce da ni yawan karatu ya ce da ni,

Yanzu karatu in za na yi said a gilashin ƙarin gani,

Medikal gilas atifishiyal zai taimakan a wajen gani,

Na goda Allah Huwallazi Mai tasarifin ji da gain.

 

Na ce idan kai lamuni zan zo ga neman sani kuwa,

Likita yai mani lamuni ya ba ni dammar zuwa kuwa,

Na je da burin a bincike don ilimantarwa kuwa,

Na sami ilimi daban-daban don ƙaruwar jama’a kuwa.

Na tamayo likitan ido rabe-raben cutar idaniya,

Ya ce da ni akwai su da dama amman kaɗan zan ƙidaya,

Akwai Gilakoma hawan jini na ido ko idaniya,

Akwai Turakoma amodari na ido ko idaniya.

 

Ya ce Gilakoma hawan jini na ido haɗarin tsiya,

Yana makantar da ido a karo guda babu tsinkaya,

Kafin a farga yake kashe lens ɗin ido daga jijiya,

Karo guda kashi casa’in na ganinka zai zama rakiya.

 

Sannan akwai Kantaras da anka sani da yanar idaniya,

Wannan da take saka mai gain gararar idaniya,

Ganinka zai zama dussu-dussu hazo-hazo babu tankiya,

Wacce ake cewa dundumi idonka a buɗe ba dubiya.

 

Ya ce da ni yanar idanu har haihuwar yaro ake da shi,

Sannan ga mai yawan shekaru daga arba’in zai gan shi da shi,

Daga Diwanin Waƙoƙin Aminu Ladan Abubakar (ALA)

Post a Comment

0 Comments