Ticker

6/recent/ticker-posts

Bayi

Yakasai, S. A. & Sani, A-U. (2021). Diwanin Waƙoƙin Aminu Ladan Abubakar (ALA)Kaduna: Amal Printing & Publishing Nigerian LTD. ISBN: 978-978-57624-9-0.

Amshi

Rayuwar Afrikawa,

Lokacin sayen bayi,

Lokacin zuwan turawan mallaka ƙasar Hausa.

 

Dori ne a kai yo bayi,

Yanzu ma ana yin bayi,

Zamani sayen bayi,

Rayuwa akwai ɗoyi.

 

Ja’iba cikin sanyi,

Balahira a kai yayi,

A zamani sayen bayi,

Mulki na mallaka sauyi,

Demokaraɗiya yayi.

 

Allah Ubangijin ƙarfi Mai arawa mai ƙarfi,

Allah Ubangijin mai rauni in Ya so Ya mai ƙarfi,

Rayuwa ta ɗauri na waigo zamani na mai ƙarfi,

Shi yake da iko yai sharafi cikin ƙasar Hausa.

 

Wayyo ni wayyo ni ALA za ni tona ajalina,

Yawan karatu da bincike-bincike za ni kai ga ajalina,

Tamfureca jinina na ta hawa tana ta karkaina,

Baƙin cikin talauci da ɗauri da yau a yankunan Hausa.

 

Ƙulafuci da ƙwawa ya hana in shiru da bakina,

Idan karatuna nake yi hawaye ke ta bin juna,

Yana ɗisa kan takarda sai kuma ya dishe idanuna,

Inna tuno aƙubar nan day au ta shafi ɗan Hausa.

 

Tun dauri kan zuwan Turawa da akwai sayen bayi,

Tun da ana da hulɗa ta jakadanci saye-sayen bayi,

Tun lokacin zuwan Larabawa nahiyarmu kwai bayi,

Harka ta yaƙe-yaƙe da fin ƙarfi ake da ingausa.

 

Tun zamani na daular Fu’uta Jallo kwai sayen bayi,

Har zuwa lokacin Fototoro ma ana sayen bayi,

Kawo zuwa lokacin futobandoka ana sayen bayi,

Nahiyar Afrika ku waigo ɓangaren gida Hausa.

 

Ƙarni na sha biyar ya zuwa ƙarni na sha tara dangina,

Kawo zuwa alif ɗari tara za ku ji a waƙena,

Tsarin Koloniyal Sistam ɗin nan da yak karakaina,

Fotugal, Ingila, Faransa amma a nahiyar Hausa.

 

Abin da anka yi waccan ƙarni kan tsatson iyayena,

Tun ina zubar da hawaye ya ƙafe hawayena,

Zan faɗawa mutane ko kwa tallafawa kokina,

Dad a yanzu duk ɗaya ne a gurin talakka ɗan Hausa.

 

Ba zaman lumana sai ɗar-ɗar arewa ‘yan Hausa,

Yawan hare-hare don yaƙi ya ɗimauta ‘yan Hausa,

Yanzu za a mayar da garinku kufai abin kamar wasa,

A maid a ‘yan ɗiyanku da matanku ganima ba wasa.

 

Idan na rintse idona sai hoton su ne a gabana,

Ina ganinsu a sarƙa mata har maza cikin rana,

Ba a bayanin kishirwa ko yunwa a kansu ga rana,

Wayyoni ni iyayena na nahiyar ƙasar Hausa.

 

Da zuwan Koloniyal Rulas in su nasara mai jan kunne,

Ya sake sabon salo Sulebtured da da ake gane,

Ya burkice taransa haras labturat salon sani,

Sai sub a ka madubi sui yi awon gaba da ɗan Hausa.

 

Guri guda haɗin gambiza gaggamin sayen bayi,

Da anka dosa kamar garken shanu da hantara bayi,

Sarƙa wuuya sarƙa hannu sarƙa a ɗaure sawaye,

Afurka mun shiga tasku har yaren uwa uba Hausa.

 

 

Ina da masu kiwon tattabara a nahiyar Hausa,

Ka tarkato ɗari a cikin kwali haɗi na ingausa,

Ba ka ma rabe mace ko namiji bare ka numfasa,

Kwatankwacin hakan a cikin sarƙa a ke ta tursasa.

 

Idan ka je ‘yan awaki kwatankwacinta ake sayen bayi,

Sarƙa wuya da hannu da ƙaffa ko cikin gumi sanyi,

Ko yanzu in ka je birnin Ikko akwai turakunan bayi,

Maza je ka Badagiri ka gano tarko na tirke ɗan Hausa.

 

Fagen ciyar da su za ka ji tausai ko da ka ƙi ko kaso,

Doya ake dafawa a watsa mussu suit a warwaso,

Bayan suna a ɗaɗɗaure kamar dabba suke ta wasoso,

Allah isar mana da mu da iyayenmu a nahiyar Hausa.

 

Sannan fa wanda duk yas sayi bawa dole yai yi tambari,

Dole yai musu alamar mallaka cikin sauri,

Ƙarfe suke sakawa a wutta su ɗaɗara yana ƙauri,

Allah wadan Bature mai jan kunne mai idan mussa.

 

Su kai ta saffarar mata da mazanmu mattsayin bayi,

Allah Mudabbiru Mai sauya salo cikin rowan sanyi,

A yau a baƙaƙen fatar da ake kai Yurof a kan bayi,

Su ne suke ta mulkin duniya ba musu da sa’insa.

 

Matsalar da sunka gadar a malladansu ka maida mu bayi,

Sun karya tattalin arzuƙan ‘yan Afruka don bayi,

Sun karya Fofuleshan ɗinmu Afrika don sayen bayi,

Da uwa uba wariyar launin jikin Afruka ‘yan Hausa.

 

Bara in juyo gida Naijeriya arewa ‘yan Hausa,

Ko zan iya rabe dauri da yanzu a kan talakka ɗan Hausa,

Talaka na dauri fa ya san farfaru da babbaƙun Hausa,

Domin suna karatun al’ajami cikin salon Hausa.

 

Bauta ta yanzu ta zarce bautar dauri in a kai tona,

Biyo ni sannu in feɗe maka birrai zuwa bindi zauna,

Bawa na yanzu da duka zagi ake yi mai jar ƙuna,

Ba said a sasari ko sarƙa ke turke ‘ya’ya na Hausa.

 

Sasarin riƙe bayi yau Illimi ake tauyewa,

Wanda duk ya san damarsa fa zai wuya ya zamto wawa,

Babu Illimin zamani babu Arrabi baubawa,

Babu ƙirƙirar zamani ba mu’amalar wayewa,

Babu lafiya babu zama lafiya cikin talakawa,

Babu cigaba kullum na abinci dai ake samowa,

A yau a duniya kayan nauyi ƙarfe ake ɗorawa,

Amma a nahiyarmu mutane su ake azawa garwa,

Noma na cigaba katafila ce take ta bi nomawa,

Yau a yankunanmu mutane su suke haƙon nomawa,

Bawa na dauri can a gidan Ogansa ne yake kwantawa,

Bawa na yanzu ko bias hanya yake zuwa yana kwantawa,

Dukkan ma’aikatu na hukuma ko na mai kuɗi mai yalwa,

Bawa na yanzu k enema masa dukiya suna karɓewa,

Da an biya shi ladan aiki sai ya je cikin kasuwa,

Ya karkashe kuɗin a abincinsa ba gurin kwantawa,

Da babu lafiya shike nan babu likkitan dubawa,

Sai barar masallatai da a yau ta zamma rigar sawa,

Ka je ka assibitoci kai tausai kana kokawa,

Ka je ma’aikatun kamfunna ka ga dandazo na ‘yan Hausawa,

Ka je ga rumfunan kasuwanni nan wasu suke kwantawa,

Ka dubi gefunan hanya kag ga mahaukata ɗiyan Hausawa,

Titi da rastuwaran tafi kai kallon bara ta ‘yan Hausawa,

Ka je ƙasashen waje ka ga yarda ake ta saffarar Hausawa,

Leƙa gidaje na masu kuɗi ‘yan aikatau ɗiyan Hausawa,

Dukkan sana’ar dab a ilimi a cikinta nemi ɗan Hausawa,

Da ka yi furruci na daba leƙa ɗiyan mu ne Hausawa,

Harkar jagaliya a siyasa duk ɗiyan mu ne Hausawa,

Jama’ar Rasulu ina mafita kan rayuwar ɗiyan Hausawa,

Wannan irin dabdala babun-baɗilahu muke ɗiyan Hausawa,

Ba nutstsuwa ta bautar Allah ba duniya ɗiyan Hausawa,

Najeriya ƙasa mai arziƙai da sun fi kai ƙirgawa,

Muna ka tsaida mulki ɗayya da zai game gidajen kowa.

 

Rayuwar Afrikawa,

Lokacin sayen bayi,

Lokacin zuwan turawan mallaka ƙasar Hausa.

Daga Diwanin Waƙoƙin Aminu Ladan Abubakar (ALA) 

Post a Comment

0 Comments