Yakasai, S. A. & Sani, A-U. (2021). Diwanin Waƙoƙin Aminu Ladan Abubakar (ALA). Kaduna: Amal Printing & Publishing Nigerian LTD. ISBN: 978-978-57624-9-0.
Amshi
Jakadiyata waƙa mai tafi da saƙona,
Jakadiyata ba ƙuiya a aika saƙona.
Bayi Sarki Allah Mai tasarrufin komai,
Sarkin da ke bai wa bayi kuma ya yo maimai,
Baiwar fasaha na ambaliya tana ammai,
Allah riƙa min in ja kar ta ja ni Maulana.
Dubun salati gun gwadabe da babu gantsarwa,
Matarbiyantar al’uma da babu karkarwa,
Balaraben bawa Hashimmu ɗan Ƙuraishawa,
Da assahabu wa ali baitihi sa’an juna.
Hanya ta karta kwana fagen isar da saƙona,
Zan bar wasiya gun ‘ya’ya da jikokina,
Ranar da kun ka zo duniya ku ɗauki saƙona,
Saƙon hikaya harsashe cikin tunanina.
Jakadiyata hanya ce ta ajje saƙona,
Jakadiyar ga hanya ce ta aika saƙona,
Garin da za ta ba na zuwa da gangar jikina,
Tana shiga har ƙoƙon zuciya da saƙona.
Hikkima ba ruhi ko jiki ba hangena,
Baa bin kallo ko ɗauki dubi ba tuna,
Hikkima ba Rauhanai ka bai bad angina,
Hikkima Ilhamiyya nake karatuna.
Hikkima taguwa gunsu muminan bayi,
Duk inda ya gan ta yaɗ ɗau abinsa ba shayi,
Ya sarrafa ta yadda ya so cikin rowan sanyi,
Ya sami arzuƙƙai har martaba tunanina.
Halin mutum sai Allah wanda yai yi mai kwana,
Ba ka iyawa kai da ɗan Adam a hangena,
Dabba da aljan ka iya sarrafa su a ganina,
Amma fa ba dai halin ɗan Adam a hangena.
Jakadiyata saƙona zuwa ga ‘ya’yana,
A lokacinmu ba ƙauna da taimakon juna,
A lokacinmu ba kishin ƙasa da addina,
Lokacinku ya zo kar ku bar kafar ɓarna.
Ku mori yarinta taku gaban zuwan tsufa,
Ku nemi ilimi kafin mamayar zuwan tsufa,
Ku mori samu kafin muttuwa ta durfafa,
Kafin zuwan mai yanke so na masu son juna.
Biyewa son rai sadarwa yake zuwa nadama,
Ku zam ƙaranci sai ku ga kun zamo abin nema,
Gujewa abin hannun jama’a ka samu alfarma,
Tsare mutunci kai daraja ka zam abin ƙauna.
Biyewa duniya kai yi nutso a kogin nadama,
Ka kama kanka sai jama’a su ma naɗin girma,
Tsare batunka kai ƙima da hikkimar nema,
Tsare ganinka zan hana zuciya saƙa ɓarna.
Halin mutum sai Allah wanda yai dare rana,
Kar ku biyewa neman burge wani ‘ya’yana,
Ba kwa iiyawa burge duniya ɗiyannina,
Da saisa-saisa al’amuran mutum ɗiyannina.
Abin da duk kai in wani ya yaba kana murna,
A kansa ɗin dai za ai maka hassada ɗana,
Abin da kag ga za ka iya ka yi kawai ɗana,
Ka barwa Allah sauran Mai tasarrufi ɗana.
Allah da Kansa wasu kokwanto suke kansa,
Sannan Ma’aikan Allah wasu na ta sa’insa,
Kasantuwarsu jakadodin Ubangijin Isa,
Ba wani nau’in al’amari da ba a sa’insa.
Jakadiyata waƙa mai tafi da saƙona,
Jakadiyata ba ƙuiya a aika saƙona.
0 Comments
ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.
HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.