Ticker

6/recent/ticker-posts

8.23 Mashigan Kano - Daga Diwanin Waƙoƙin Aminu Ladan Abubakar (ALA) (Page: 437)

Yakasai, S. A. & Sani, A-U. (2021). Diwanin Waƙoƙin Aminu Ladan Abubakar (ALA). Kaduna: Amal Printing & Publishing Nigerian LTD. ISBN: 978-978-57624-9-0.

Yau yabo zan yi wa abubawan kambamawa,

Mashiga tak Kano abin gwanin armasawa.

 

Rabbana ƙadirin Allah abin girmamawa,

Wanda ikonsa ne na buɗe bakin ga nawa,

Nai nufin ambato abubuwan kambawa,

Tarihin Kano jaha abar girmamawa.

 

Rabbana kai daɗin tsira mara ƙididdigewa,

A gurin Annabi cikamakin Annabawa,

Har ɗiyan Faɗima Zahara'u ‘yar Larabawa,

Nai tawassul da sonsa ka ba ni ikon gamawa.

 

Zan batu kan ababen tarihin Kanawa,

Wasu an banzatar wasu an bi an adanawa,

Mai yiwa yin hakan zai tinzirar da Kanawa,

A gurin kariya da abin da zan ambatowa.

 

Farko ganuwa ta Kano ta kekkewayewa,

Wacce tau wanzu tun zamaninsu Annabawa,

Hikimar farisi Salmanu ɗan Farisawa,

Mutanen Kano muna ta rurrugujewa.

 

Wasu na iƙƙirarin zamani ya sauyawa,

Wai sun cigaba kawunansu ya zam wayewa,

Ni kuwa sai na ce tuna baya shi ne yabawa,

Tozartar da tarihi ya zai zam wayewa.

 

Wai ina gwamnati tarihi zai gushewa,

Martabbinmu ne fa ake ta ballaggazarwa,

Tarihimmu sarki amma fa ya zam gushewa,

Mu ne kariya ga martabobin Kanawa.

 

Gidan tarihi na Makama Museum da ke garin Kano.

 

Gidan tarihi na Makama Museum da ke garin Kano.

 

Ƙofofin Kano nai nufin in ɗan wassafowa,

Na jikin ganuwa da ta zaga birnin Kanawa,

A bisa nazzari da na bincika ba rufewa,

Sirrin Kano abin gwanin armasawa.

 

Sarkin Kano Gijimasu sarkin Kanawa,

Shi ne sila da ya fara ƙaƙƙaƙarowa,

Ƙofofi goma guda huɗu ka zam daɗawa,

Tafiyarsa Rumfa ya maye gurbi Kanawa.

 

Shi ne ya rushe guda takwas ba daɗawa,

Ya ƙara nasa guda huɗu a kai, a kai sanarwa,

Kafin zuwan Bayero sha ukku sun cikewa,

Ya ida sha shida wanda zan zayyanowa.

 

Gado-ƙaya wani malami ne Kanawa,

Mai taƙƙawa zuhudu abin ba shi faɗuwa,

Sam ba shi barci bisa abin shimfiɗawa,

Shi ne ya furta gado ƙaya ba musawa.

 

Dukawuya suna ne ba musawa,

Na wani sadaukin jarumi marra ƙwawa,

Giddansa anka biɗa ya ce ba shi baiwa,

Sarki ya zo da ƙafarsa don faɗɗakarwa.

 

Ya ce da bawan nan ni na izo fadawa,

Gidanka za ai maka wani abin yabawa,

Sannan fa ƙofar sunanka za a sawa,

Kun ɗan ji tarihi gwanin armasawa.

 

Ƙofar Ruwa da ake faɗi ku ji Kanawa,

Sunan ɗiyar sarkin Kano ce Kanawa,

Sunanta lungui babu ja ba musawa,

Shi ne fa sunan ƙofar dad daɗewa.

 

Ƙofar Mazugal ma disem ‘yan Kanawa,

Sunan ɗiyar sarkin Kano ce 'yar baiwa,

Jika gurin suntilma mai martabawa,

Ba a canza sunan ta ba, ba mai ɓatarwa.

 

Ƙofa ta Wanbai zan faɗo don sanarwa,

Ƙofar dagacci da ake ambatawa,

Sarki uban Abdu Rumfa nak Kanawa,

Shi yai naɗin wamban da ba tumɓukewa.

 

Ƙofar Fagge da a yanzu aka tumɓukewa,

Ƙofa ta Mata da hakka ake sanarwa,

Wani hattsabibi na mata kira shi wawa,

Shi ne dalili, ko akwai mai musawa.

 

 

 

Ke Nassarawa abu abin ƙayatarwa,

Ita ce kafa ta Nasara mai idon kyanwa,

Sunansa ne aka sa wa ƙofar Kanawa,

Azzalumai masu halin ɓatarwa.

 

Agundi sunan wata ɗiyar Maguzawa,

Wacce dalilin ɗanta ne anka sawa,

Ƙofar fa suna Ɗan’agundin Kanawa,

Shi ke tsaron ƙofar gari 'yan Kanawa.

 

Ƙofa ta Waika ba abin rikkitarwa,

Wani ɗan’adam ne mai kashi dat tsarewa,

Sunansa ne aka bai wa ƙofar Kanawa,

Sauran kaɗan sha shida in zam kammalawa.

 

Ƙofar Nadilke ta zam ana cewa sabuwa,

Don ɗalibai aka yi ta don sauƙaƙawa,

Ƙofa ta Famfo kuma dalilin zuwan ruwa,

Sauran Dawanau, Na’isa in kammalawa.

 

Ƙofar Dawanau asalinta Kanawa,

Maje Karofi da Abdallahin Sikawa,

Kullum idan ya rako shi mahaɗa ta rabuwa,

Zai ce a nan Malam mu ɗan dawayawa.

 

Wasu sunka ce Bafulatani ne Kanawa,

Ya taho da garken shanu wai zai wucewa,

Sarki na ƙofa ya hana masa wucewa,

Da yai fushi yai wa kansa hanyar wucewa.

 

Sarki Sulaimanu ya aika ya zowa,

Yat tambaye shi dalilin ruggujewa,

Wai sai ya ce sarki isa ce tasawa,

Daga nan akai masa lamunin tabbatarwa.

 

Wani laffazin zan zayyano kwa rabewa,

Wani malamin sarki abin girmamawa,

Zawaciki daga can yake lallaɓowa,

Shi ne sila ɗan dakata ka ji sanarwa.

 

Hanyar Sharraɗa ta nan yake lallaɓowa,

Ya iso wajen sarki a cikin gajjiyawa,

Sarki ya ce zan fidda ƙofa ta shigowa,

Domin ka sam sauƙi gurin kewayowa.

 

Na isa? Ya ce a cikin girmamawa,

Sarki ya ce ka isa har ma ka ɗarawa,

Sannan akai ƙofa a don girmamawa,

Sai kui hukunci bisa misalan ga nawa.

 

Tammat a nan zan dakata in tsayawa,

Da batu a kan mashigar Kano masu baiwa,

Wani lokacin zan karkata majemawa,

Har karofi, marina ku ji abin yabawa.

 

Alan Kanawa shi ya zaman kattabawa,

Almajiri ke jinjina don yabawa,

Alhamdulillahi wanda ya ba ni baiwa,

Don kammalo waƙar yabo gun Kanawa.

Daga Diwanin Waƙoƙin Aminu Ladan Abubakar (ALA)

Post a Comment

0 Comments