Ticker

6/recent/ticker-posts

8.22 Baubawa 2 - Daga Diwanin Waƙoƙin Aminu Ladan Abubakar (ALA) (Page: 435)

Yakasai, S. A. & Sani, A-U. (2021). Diwanin Waƙoƙin Aminu Ladan Abubakar (ALA). Kaduna: Amal Printing & Publishing Nigerian LTD. ISBN: 978-978-57624-9-0.

Allah kai kab ban dama nai saƙa na baitukan bawan burmi,

Munanan jagorori Allah sun iza mu mun faɗa kurmi,

Jabbarul Ƙahharu, Allah taimaka ka tsame mu a rami.

 

Allah kai mana jagora kai mana kattari da zaɓin tumun dare,

Rabbu zame mana linzami ja ragamarmu taimaka mana mun tsere,

Don ko dauɗar zalunci ta sassarƙafe mu ta hana mu more.

 

Ya Nabiyal Rahamanu, Annabi Nurul-huda Darul Khairi,

Mai tarbiya adala, Annabi mai kamar kamala da sururi,

Ya Ahhamadu Humaidu Mahe, Mahiru, Muhammadu Minnuri.

 

Babu tsumi babu daraba, Allah kai muka doso neman tsira,

Allah na nufi yin tsani da sunanka Rabbana tsanin tsira,

Ka dube mu ka cece mu don ƙauna da biyayyar manzo Nura.

 

Rahamarka muke so, tausayinka muke so

Kai kake daƙusarwa,

Kai kake danƙwafarwa,

Kai kake dilmiyarwa,

Kai kake wargazawa,

Kai kake tambaɗarwa,

Kai kake ruguzawa,

Rusa duk mai cutarwa,

Ka tsare talakawa.

 

Rahamarka muke so, tausayinka muke so

Kai kake tausasawa,

Kai kake tallafawa,

Kai kake darajawa,

Kai kake mutumtawa,

Kai kake rahamawa,

Kai kake fallalawa,

Kai muke sujjadawa,

Ka tsare talakawa.

 

Ya Allahu Rahamanu, Ubangijin Adamu har ɗan Maryama,

Ya Malikul Ƙuddusu, Ubangijin Musa har Ibrahima,

Ya sallamul Muminu, Ubangijin Hudu da Nuhu abin girma,

 

Ya Muhaiminu Azizu Ubangijin Ismaila Ayuba ma,

Ya Jabbarul Ƙahharu Ubangijin Dawuda da Is’haƙa ma,

Ya Wahhabul Razzaƙu Ubangijin Iliyasu da Yusif ma.

 

Ya Fattahul Allimu Ubangijin Alyassa'a Suleman ma,

Ya Hakkimul Addalu Ubangijin Yahaya har Zakariya ma,

Ya Alhaƙul Sabburu Ubangijin Idrisu, Zulƙifli ma.

 

Ya Albariƙu Ra'ufu, Ubangijin Yunusa har Yusha'u ma,

Na yi tawassul ya Allah, don neman tsari na haƙƙin al'umma,

Dube mu ka cece mu, ja ragamarmu mun zamo kayan tsumma.

Daga Diwanin Waƙoƙin Aminu Ladan Abubakar (ALA)

Post a Comment

0 Comments