Ticker

6/recent/ticker-posts

8.21 Bazazzagiya - Daga Diwanin Waƙoƙin Aminu Ladan Abubakar (ALA) (Page: 427)

Yakasai, S. A. & Sani, A-U. (2021). Diwanin Waƙoƙin Aminu Ladan Abubakar (ALA). Kaduna: Amal Printing & Publishing Nigerian LTD. ISBN: 978-978-57624-9-0.

Ga yabo zan da amintacciyar murya,

Da haruffa ma su ƙarshe da harfuyya.

 

Mahaliccinmu da kai mun ka togaciya,

Rabbu allahu gwani wahadaniyya,

Kaliƙi jallah abin sujjadarmu ɗaya,

Massarauci mai sarauta sahihiyya,

Wanda nakkewa ibada rububiyya,

Haka nan shi na kaɗaita ƙuluhiyya,

Assama’ullahi husuna na khairiyya,

Na riƙe sunanka Allah a tsaniyya,

Zan yi raddi ka hana in yi mundirya,

Dogarona da isar mai hijabiyya.

 

Rabbu in kai lamuni na azo niyya,

Babu waige ko in ce za ni ja baya,

Babu karkarwa bare in yi Dawayya,

Za ni waƙe Gwadaben al’umar duniya,

In yi Raddi na ƙasida Bazazzagiya,

Babu burga a yabon Sayyidil Anbiya,

Don Ibada ba asa Ujjubu da riya,

Ba a yi don nuna fifiko Tsinkaya,

Ikkilasi shi yake tsarkake hanya,

Mannufa ke tajadidin Haƙiƙiyya.

 

Zan yi don wanda ka keɓe kususiyya,

Ya yi aure daga ɗai har ga shaɗaya,

Mahabubu da ka haifa a Makkiya,

Babu mai kyau na ɗabi’a da Halayya,

Da ya kai har a kwatanta shi don gayya,

Da masoyi da ya zarce mu jin kunya,

Wanda ba ya yin dabo ko ko Ramliyya,

Ɗaha ba ya ɗaura guru bare laya,

Shugaba gun Talikan fari Usuliyya,

Shugaba gun su na ƙarshensu kulliyya.

 

Sabbabi gun talikai don mu san shiriya,

Sannadin yanke uzur gun su shakkiyya,

Zani tsintsinka bayanan maza na jiya,

Za ku ji su rukunoni shiya-shiya,

Gwargwadon hujja ta mai bi ga Malikiyya,

Gwargwadon hujja ta mai bi Wahabiyya,

Gwargwadon hujjata mai bin su Shafi’iyya,

Har Hanabillah da ke bi ga Hanbaliyya,

Za ku ji su nukuɗa-nukkuɗa zirya,

Babu danshi ko kuwa sofanan ƙarya.

 

Bissa hujjojin sahabbai na Salafiyya,

Za ni faro kafuwar Issilamiyya,

Daga haifar Abdu ɗan Abdu marraya,

Baƙuraishe Madaniyi uban gayya,

Ɗaha raino na Halimatussadiya,

Wanda ba ko Sofanen ibbilisiyya,

A jikinsa ba rabo na shaiɗaniyya,

Tsarkakakken asali Ɗan Balarabiya,

Baƙuraishe masu harshe na Arabiyya,

Shugaba gun su Bilalu na Habashiyya.

 

Ɗaha na Salman na Farisiyya,

Mai Abubakar da Umar maza tarya,

Mai Aliyu Ɗan Abi-Ɗalibi ku ji ya,

Zunnuraini silar Ussumaniyya,

Daularsa ta gabaci Abbasiyya,

Kafirai sun sha kaɗa sai kace Kanya,

A gurin su Asahabu Imamiyya,

Zani zano yaƙunan Muhammadiyya,

Daga kan Uhudu zan yo da ƙafiyya,

Ya zuwa yaƙin Ahazab da harfuyya.

 

In taho kan na Badar kuj ji gwamayya,

In dire yarjeniya ta Huɗaibiyya,

Kuj ji artabu gumurzu da ninkaya,

Da Sahabbai suka yo don farar aniya,

Babu mai kyawun hali ko ko talbiyya,

Da ya kai ay yi kwatanci ko a taya,

Shi Muhammadu fa ba ya da ƙyaliyya,

Ko da yaushe zahirinsa da nuriyya,

Ɗaha baya ƙyalƙyalewa da dariyya,

Murmushi kullun a fuskarsa haibayya.

 

Da yana ɗan ƙarami ba ƙuruciya,

Wacce ‘yan yara su ke yi ƙiriniya,

Ko yana a tafe kansa a sunkuya,

Ba shi yin rubda ciki ko a kwanciya,

Laddabi za ka gani ko a zauniyya,

A mu’amillarsa bai nuna wariya,

Ba’a bar massa amana yai noƙiya,

Ɗaha ko gun magana ba shi bauɗiya,

Ba shi ƙarya ko bayani na shirgiya,

Ba a mai wasa kwatancin na zolayya.

 

Wahayi an ka yi mai ba tatsuniya,

Baƙƙuraishen asali babu ɗauraya,

Hashimiyyi asali babu gaurayya,

Kyakkyawa a kala babu rawaya,

A kalarsa babu kore da shuɗiya,

Bai zamo tsanwa ba ba algashishiyya,

Hasken atafa ko ko tufaniya,

Ko ko silba darhami da zinariyya,

Ko Lu’u-lu’u da Yaƙutu kirgayya,

Ko Zubardaji haɗa Alhaririyya.

 

Ba su kai Ɗaha ba hangen wawalniya,

Ɗaha mai hangen da yaz zarce mikiya,

Mai ganin baya fa ba da tujalliyya,

Ɗaha mai ba da bayanin gabanniyya,

Kar ku ce na ce fa ya san fa gaibiyya,

Ƙuddura ce daga Rabbil magarabiyya,

Wanda yassaukar masa da mu’ujiziyya,

Ya ilumta shi da sannai ya Maliya,

Ya azanya shi samanmu da kaifiyya,

Ya rabauta shi da shaiɗan na jinniyya.

 

Ya katange shi da shaiɗan na insiyya,

Ya katarshe shi da Ibilis Shaiɗaniyya,

Ya zamnto Annabi Mursali ku ji ya,

Mursali daga Ulul A’azamiyya,

Sidi mai Mu’ujiza da Ƙur’aniyya,

Ɗaha ba dogo ba zanƙal ya falwaya,

Ba gajere ɗan duƙus ba ya muciya,

In ya taka tafukansa a tsandarya,

Ka zata hoton ƙafar ne zananniya,

In a yashi ko ya taka su ba shanya.

 

Babu shati ko alama fitacciya,

Ɗan Adam ne ba kamarmu ba bebanya,

Mu riƙe Al-Isilamu kamar igiya.

Kulluhum mussilumun mu yi biyayya,

Don hakanne fa mu ke yin auratayya,

Har mu sadar da saye har da sayayya,

Ƙarƙashin rainonsa ne mukka cinikayya,

Wanda yabbishi fa ya sami kariya,

Zai zamo dimun a kullum a marariyya,

Ran ƙiyama yai katar kuma da sakayya.

 

Kag ga lada na zuba sai ka ce shaya,

Kafurai ko sufa sai dai fa izzaya,

Ban da wawa mai fahar koko fankiya,

Mai asarar duniya shi ka danniya,

Shi ka halin bishiyar nan ta shirinya,

Wacce bata tohuwa daga tushiya,

Ta tsiro kan ‘yar uwarta tai bankiya,

Mai hakan za shi ya koka kamar tsanya,

A cikin dai fa ido anka tsawurya,

A cikin ƙwallon ido an ka yin hakiya.

 

 Rabbana kai arziki gunmu dukiya,

Wanda ya zarce na Dirham da tsakiya,

Ya fuce garke na shanu da Goɗiya,

Son Ma’aiki sai kawai muyyi godiya,

Wanda ya kasa hakan shi da soshiya,

Babu banban da haka ko da Tinkiya,

Ran ƙiyama za ya narku da nakiya,

Za ya sha casa na duka da cashiya,

Da mahangurɓa da narka da totsiya,

Za ya koma dan zarennan na tsirkiya.

 

Shi ya kawo kamsussalawatiyya,

Ɗai cikin shika-shakan mussulunciya,

Fari Imani da Allah Rabbaniyya,

Da Muhamadu abin bi haƙiƙiyya,

Wa tuƙimussalata in-saniyya,

Ku biya zakkar kuɗin ku halaliyya,

Watu saumu Azumin Ramadaniyya,

Wa tu Hajju Baitillahil Haramiyya,

Limanistaɗaha Ilaihissabiliyya,

Kun ji tushen Isilama da taskiyya.

 

Uhudu inna tuna sai na ce kayya,

Don ko mun tafka asara da ta fibiya,

Don a rannan Sayyadi Hamza yai aniya,

Yai yi baƙuntar kushewarsa Marsiyya,

Hindu ta ɗauko haya ta gwanin kibiya,

Bahabasshenta gwanin jefa mashiyya,

Shi ya jefa shi ga Hamza a zuciya,

Har da hantarsa ta yanko da tutiya,

Mahamudu ya fusata ya ɗau mahaya,

Zai yi ramko sai Ilahu ya ce Ayya!

 

Assabar ya sahibul sabaru kulliya,

Kalidu ɗan Walidu yai yi turjiya,

Da ya hango ɓaraka a Sahab Mabiya,

‘Yan baka wanda ka ce kar su bar ƙurya,

Daga hango galaba sai sukai zarya,

Sai ko Khalid bini Walid ya dulmiya,

Sai ya hau saran Musulmi kamar kanya,

Khalidu yai mana ɓarnar da sai jinya,

Ɗan Kaisu shi ya doki mijin Mariya,

Da Abubakar da Umar sukai tarya.

Sai Aliyu sai ka ce an kiɗan kurya,

Sai ya zare fa Takubba Muhaddayya,

Sun kaɗa sun rikiɗe dukkanin ijiya,

Kawuna ke ta zubarwa ya maggarya,

Sai ƙire arna ya ke sai ka ce ƙirya,

Kan ka ce kanzil fa Arna fa sun karaya,

Sai Muhammadu ya ce ce Ali ya tsaya?

Kar ya ƙarar da Ƙuraishu da sharaɗiyya,

Wassu an bar su gwagware kamar gafiya,

Wassu na zubda mugunya cikin tsiya,

 

Sai bushara daga Allah Rabbul Bariya.

Ga Muhammadu fa domin a sanyaya,

Ko ina haskenka zai je ya zagaya,

Gashi daula ta Muhammad ta kewaya,

Gashi haskensa a yau har a Bosniya,

Masu ƙaunar Annabi har Sumaliya,

Masu addini na Allah Ethofiya,

Daula ta Islama a Turkiyya,

Mamaya ta musulum har cikin Libiya,

Yanzu ƙanshin Musulunci fa har Kenya.

 

 Na ga ƙwazon su Aliyu Tunusiyya.

Har wa yau dai Islam na Iraniyya,

Kuma tushen Musuluncinmu Saudiyya,

Mamaya ta mamayo har Malesiyya,

Har Arewa da ƙasarmu Nageriya,

Har da sassa na kudancinmu Kufriyya,

Ya yi naso Musulunci a Indiya,

Danshi-danshinsa fa har da Burtaniya,

In da yai ambaliya har Tanzaniyya,

Sun ji ƙanshin Musulunci Namibiya,

 

Issilam yai sansani a Aljeriyya.

Yanzu ma zai kafa daula Ejifshiya,

Inda Fir’auna ya rayu da Kibriyya,

Har Afurkawa a yankin Laberiya,

Wani sashen Saraliyon ya zaizaya,

Ya daɗe yai sansani a Sudaniyya,

Hakaza yai mamaya a Indunusiya,

‘Yan uwa kadda na mance Afganiyya,

Har Amurka da na cewa Imrikiyya,

Rabbu baya alƙawar yaiyi Zobayya.

Na faɗa na kaurara har da Tafkiyya,

 

Yanzu yaƙin Al-Ahazabu zani biya,

Kafurai sun ƙudurin za su yanka wuya,

Na Musulmi ba na mai bin Masihiyya,

Da Ƙuraishu da haɗakar Yahudiyya,

Wanda sun wa Ɗaha sammu jikin cinya,

Don buƙatar su ya ƙaura su Sharɓi miya,

Sammu ya ci kariya ta Ilahiyya,

Kafirai sun sa ribaɗi a zawiyya,

Yau ina da mafita ko dabarayya,

 

Sai Sahabi Masa’udun Sa’udiyya.

Sai ya ce Inna-lana kwai makidiyya,

Sai ya kukkula makida ta takkiyya,

Da Ƙuraishu da Yahudu hatsaniyya,

Kan ka ce ƙala fa sun kama kwafsiyya,

Sai fa iska daga sararin samaniyya,

Ta kaɗa tai kokuwa tayyi gaurayya,

Kafirai sai rikita turmutsetseniya,

Kan ka ce dal! Babu ko da ɗigon aya,

Kafurai sun sulluɓe sun bi rariyya.

 

 

 

Al-Ajabbi ga Musulmi da dubayya.

Al-Issilamu fis an tassalimiyya,

Kun ji addini na so har da lobayya,

Za ni yaƙi na Badar kujji cuɗanya,

Na gumurzu da akai a tantagarya,

Kujji kwafso da ƙashi harda ɓargwanya,

Inda jini ya malala da muggunya,

Sannadin tsaida hukunci na shar’iyya,

Ka ga wafta da salon gilmemeniya,

Da wucewa da Takubba ya walƙiyya.

 

Kaj ji ƙarar Kafirawa ya gyaranya,

Wanni ƙararsa kamar wanda ke sakiya,

Kagga rimin kafirai da haniniyya,

Ran Badar an ‘yanta bayi wuyayiyya,

Don ko an sami ganima Baladiyya,

Wassu sun karkarɓi kalma Shahadiyya,

Ran Badar shumagaban Izgililiyya,

Ya zamo gawa mataccen kuciciyya,

Da Abu Jahil na ke samfurin hauya,

Wanda yattakura Manzo Madubiyya.

 Ya zuba massa tunbinsa na Saniya,

 

Ya bi hanyarsa ya shirya masa ƙaya,

Miƙƙidadu shi ya sa shi hajijiya,

Da ya doke shi a ka ɓangaran ƙeya,

Yai yi kumaji ya faɗi kamar taya,

Annabi yagga yana ta harbebeniya,

Sai fa karkarwa yake ya farfaɗiyya,

Ya kusanto shi da kalma siyasiyya,

Rabbu yaccewa uba gun sharifiya,

Ni na ke ikon kashewa ni zan raya.

 

Sai Muhammadu jikinsa ya sanyaya.

Sai ya bar iko gurin miƙa Wulaya,

A gurin wanda ya keɓu da Kibiriyya,

Ɗan Abu Ɗalibi ya zam ƙarangiya,

Sai zubar Arna ka ke ji ya ɗan ɗinya,

Sai ka ce ƙwari a fesa fiya-fiya,

Sai da Allah yai Ishara ta nunayya,

Ga Malaku da su je suyyi kariyya,

Kada Kuffaru su wa Ali rafkiya,

A sadaukai daga Ali sai Fatiyya.

 

Ango ne na Umama da Shamsiyya,

Haziƙi Baban Hasan da Husainiyya,

‘Yan ɗiya gun Taufatul Ahawaziyya,

Kun ji hurul eni Sadiƙa Nadiyya,

Faɗimattu Al-Karimatu Gimbiya,

Ka ji tsokar Annabi kuma Waliyiyya,

Man Azaha ya ce a kitabiya,

Faƙad a zani kawai babu bauɗiya,

Man Azani in ji shi Abal Adiya,

Faƙad Azallahu sai mui a uziyya.

 

Hamza ma ya kashe Arna kuna zurya,

Ya yi fyaɗa ta kaɗanya da zamiya,

Don gwani ne na makama da sabiya,

Zan tsaya nan sai ka ce wata kamariya,

Da batun yaƙin Badar in yi jirgiya,

Ga Huɗaibiya da an kaiyi yarjeniya,

Kan Huɗaibiyya bara in yi dajiya,

Da yabon wanda na ke yi da rausaya,

Na ya be shi da salo na ba Sakkwaciya,

Na yi baiti da ƙari na Bazanfariya.

 

Na yi waƙa da salon a boboniya,

Na yi waƙa da amo na Fulfuldiya,

Na yi gunji da fatan na Babarbariya,

Na yi an amsa da amshin Bayerabiya,

Na yi an yo jinjina ta Badakkariya,

Na yi har toshi akai da Ba’adariya,

Na yi har ɗinki a kai min da wundiya,

An saka min taguwar nan Ba’aganiya,

Godiyata nikayowa kaya-kaya,

Ga Maƙagin teku farkonta har wutsiya.

Daga Diwanin Waƙoƙin Aminu Ladan Abubakar (ALA)

Post a Comment

0 Comments