Ticker

6/recent/ticker-posts

8.20 Zuciya Ta Auri Tunanina - Daga Diwanin Waƙoƙin Aminu Ladan Abubakar (ALA) (Page: 425)

Yakasai, S. A. & Sani, A-U. (2021). Diwanin Waƙoƙin Aminu Ladan Abubakar (ALA). Kaduna: Amal Printing & Publishing Nigerian LTD. ISBN: 978-978-57624-9-0.

Amshi

Zuciya ta auri tunanina,
babu walwala akwakwalwata,
Hankali ka ceci gabobina,
kada zuciya ta ga bayana.

Ga ido yana daka zucina,
Ga ƙafa tana biye zucina,
Hannuwa suna biye zucina,
Lafuza suna biye zucina,
Rayuwa a kan haka ba shakka,
Ba ta haifi da ɗa idanuba.

Yaya za ku min haka gaɓɓaina?

Kusallamawakalbina?


Na gaza da rintse idanuna,

Don saboda saƙar zucina.

Na gayyawa dukka kafafuna,

Da ke biye wa ƙalbina.

Da iman a aikace kalbina,

Ta auri dukka tunanina.

Hankali ka yi mani rinjaye,

Maallake ta dukkkan ƙalbina.

Ilimi suturta jikin Ala,

Ka yi min ado da gaɓɓaina.

Rabbu kar ka bar ni da wayona,

Ba za na ɗauka ba.

Ka riƙe gani da tunanina,

Ba za na jure ba.

Kada kas sakar wa akalata,
Ba za na jure ba.

Ji gani dukansa tunnanina,

Ba su cetan ba.

Tun da nai riƙo da madubina,
Ba za na taɓe ba.

Annabin da ban ga kama tai ba,
Ba za a sake ba.

Don saboda so da biyar manzo,
Ka ida dukka muradina.

Daga Diwanin Waƙoƙin Aminu Ladan Abubakar (ALA)

Post a Comment

0 Comments