Ticker

6/recent/ticker-posts

8.19 Hajji Garin Manzon Allah - Daga Diwanin Waƙoƙin Aminu Ladan Abubakar (ALA) (Page: 424)

Yakasai, S. A. & Sani, A-U. (2021). Diwanin Waƙoƙin Aminu Ladan Abubakar (ALA). Kaduna: Amal Printing & Publishing Nigerian LTD. ISBN: 978-978-57624-9-0.

Amshi

Birnin alkhairi za ni garin manzon Allah,

Nai niyyar hajji duk da garin ba baƙo ne ba.

 

Na ƙudure niyya da izinin Sarki Allah,

Zan zama alhajji a rukunin bayin Allah,

Arkanuddeni da suka zo daga gun Allah,

Farko imani da mahalicci na Allah,

Ɗan Abdullahi bawan Allah Sarki Rabba.

 

Sannan ga sallah kamsussalawat lillahi,

Kana ga saumu arramadana lillahi,

Sai haƙƙin Allah zakkah bi'izinillahi,

Hajjul mabruru wanda akai don lillahi,

Arkanuddeni sun cika ko ɗai bai tauye ba.

 

Nai haramar niyya ba guzurin ko da naira,

Na ƙudure niyya duk ɗamara duka na ɗaura,

Babu tsumin sisi ba wayo koko dabara,

Face lillahil izzati Sarkin ƙaddara,

Wanda ake roƙo bai taba kosawar bayi ba.

 

Daren wata Larabba na ɗauki wayana amsawa,

Na sa ta a kunne nai kasaƙen saurarawa,

Sauti na Kabiru Barde Babawa ya kunnowa,

Ɗan sarki Ado Bayero mai Kano san kowa,

Shi yay yi bushara za ka tafi hajji gun Rabba.

 

Sanadin soyayya ALA je ka gari babba,

Makka da Madina gun Mahamodu gwanin Rabba,

In ka je ALA shabbaki na farin duba,

Miƙa buƙatunmu kai adu'a a gurin baba,

Ya san ƙudurinmu Rabbu ba za ya ƙi amsa ba.

 

 

Kayan alatu dagga cimaka mai tsafta,

Nan nay yi hani'an nai shukra Sarkin bauta,

Nan na yi magariba nai issha'i zan kwanta,

Zazzaɓi ya rufe ni ciwon kai da makyarkyatta,

Na kwana ibada mai tsanani daga gun Rabba.

 

Na gode Ilahu mai karɓar adu'ar bayi,

Shi ke jarabawa mai tsanani a ruwan sanyi,

Ɗazu-ɗazu i hakka babu sukunin ya zan yi,

In ya so Mabuwayi yan nufi kaffara zan yi,

 

Saraki Kabiru sai ya kashe daga sadarwa,

Shauki ya ishe ni za ni garin manzon baiwa,

Murna ta ishe ni ga zagwaɗi tsananin kwawa,

Na kirayi Kabiru Barde jadda godewa,

Ban son godenka ƙauna ai ba ta ƙare ba.

 

Zan tashi Abuja gidan na Laraba nai zango,

Karimin bawa Abubakar mai son ungo,

Yab ba ni masauƙi sakatare na yi ɗan zango,

Ranar Asabar ne jirgin sama ya zo kago,

Yat tashi Abuja sai ko Madina gari babba.

Daga Diwanin Waƙoƙin Aminu Ladan Abubakar (ALA)

Post a Comment

0 Comments