Ticker

6/recent/ticker-posts

Madina Garin Ma'aiki

Yakasai, S. A. & Sani, A-U. (2021). Diwanin Waƙoƙin Aminu Ladan Abubakar (ALA). Kaduna: Amal Printing & Publishing Nigerian LTD. ISBN: 978-978-57624-9-0.

Amshi

Shukuran da garin masoyi da muka je can baiti sire,

A Madina garin ma'aiki an mana karɓar girmamawa.

 

A Madina garin ma'aiki

An yi min kyautar turare.

 

A Madina garin ma'aiki,

Muk ka ci shinkafa da tsire.

 

A Madina garin ma'aiki,

Na ga masoyana a jere.

 

Daraja a garin ma'aiki,

Ta wuce kirdadon kirare,

 

A garin na zaman ma'aiki,

Babu husuma koko bore.

 

Shukuran da garin masoyi,

Mai ƙamshi wane turare.

 

Ikon Allah Buwayi ba shi da farko koko ƙarshe,

Falalar Allah Saraki ba ta kwatanto ko hasashe,

Ni'ima ta sa Mabbuwayi mai saka kwankwanto dusashe,

Maza dubi zubin bisashe ya mai kallon hasashe.

 

A cimakar duniya yau har da Bahaushe a kwatance,

A Madina garin ma'aiki na ga abin sharafi kwatance,

A abincin duniya kaf har da na Hausa cikin kwatance,

A Madina a baiti sire can na ga mamakin kwatance.

 

Mota na gani a layi kowa ya zo baiti sire,

Da na tambayi baiti sire sai a ka ce rinka ta tsire,

Ma'anar rinka ta tsire wai manufar ta gida na tsire,

Duk ƙasaitar Bakurde ko basarake sai da tsire.

 

Da na zaga gida na tsire sai na ga Hausawa a jere,

In suna yaren Sa'udai ba ka rabewa ko a jere,

In suna Hausar Kananci tamkar ALA na kirare,

Wai ashe ‘ya’yan kano ne su suka mallaki baiti sire.

Daga Diwanin Waƙoƙin Aminu Ladan Abubakar (ALA)

Post a Comment

0 Comments