Ticker

6/recent/ticker-posts

8.17 Addu'a Ga Masoyana - Daga Diwanin Waƙoƙin Aminu Ladan Abubakar (ALA) (Page: 421)

Yakasai, S. A. & Sani, A-U. (2021). Diwanin Waƙoƙin Aminu Ladan Abubakar (ALA). Kaduna: Amal Printing & Publishing Nigerian LTD. ISBN: 978-978-57624-9-0.

Amshi

Rabbana kadamin da ka ɗora ni,

Ba wai da zane ba.

Rabbana ka hane mu ka munkari,

Ni jar masoyana.

 

Rabbana masanin sarari ɓoye, rani da damina,

Rabbana masanin sirrin ɓoye aljan da insana,

Rabbana masanin sharrin ɓoye ƙauye da birnina,

Rabbana ka hana mu ganin sharri ni har masoyana.

 

Rabbana ka tsare mu da yin shirka babba da ƙarama,

Ka hane mu dukan nau'in shirkar ɓoye muna nema,

Ka tsare mana imani Allah don annabin girma,

Ka hana mu halin homa Allah jiji da kai girma.

 

Rabbana ka tsare min imani kar nai bakar jewa,

Ka saka mini albarkar gawo toho da yaɗuwa,

Lokacin da bisashe ke fari domin rashin ruwa,

Sa'ilin da yake toho gawo kana da yaɗuwa.

 

Ka hana ni shiga shirgi Allah 'yan ribatar kowa,

Ka tsare ni a kiɗa mummuna hanya da gantsarwa,

Ka kiyaye Musulmi al'uma kar su yi bakar jewa,

Ka aza mu tafarkin alhairin da babu cutarwa.

 

Rabbana kogin zunubi Allah ya shanye duk kaina,

Na ɓace a cikin gulbi Allah kai ne ka ceto na,

Rabbana ka tsare mu da yin shirka ko ɗis!! A bakina,

Rabbana ka saka mu yi kyan ƙarshe ni har masoyana.

Daga Diwanin Waƙoƙin Aminu Ladan Abubakar (ALA)

Post a Comment

0 Comments