Ticker

6/recent/ticker-posts

8.15 Nasarun Minallahi Sojojin Nijeriya - Daga Diwanin Waƙoƙin Aminu Ladan Abubakar (ALA) (Page: 418

Yakasai, S. A. & Sani, A-U. (2021). Diwanin Waƙoƙin Aminu Ladan Abubakar (ALA). Kaduna: Amal Printing & Publishing Nigerian LTD. ISBN: 978-978-57624-9-0.

Amshi

Nasarun minallahi sojojin ƙasar Nijeriya,

Nasara tana banku sojojin ƙasar Nijeriya.

 

Shimfiɗa

Burga da ƙafafa tana a zama ƙalau Nijeriya,

Kuri da jarumta yana a tsaron ƙasar Nijeriya,

Kishi na ‘yancin kai yana tsare martabar Nijeriya,

Zama ɗan ƙasa na gari yana tsare tattalin Nijeriya,

Tsari da bin doka yana daga darrajar Nijeriya,

Daraja da kimarmu tana ga tsare ƙasar Nijeriya,

Peace unity duka ma yana a ƙasan zamanmu lafiya,

Nasarun minallahi ga sojojin ƙasar Nijeriya.

 

Lillahi Wahidun Sattaru tsare ƙasar Nijeriya,

Sarkin da shi ya kaɗaita da bauta wa gwani wahaɗaniya,

Sarkin da ya yi Afurka ya sanya uwa ta zam Nijeriya,

Shi ne nake roƙon sa ya ba mu zama ƙalau Nijeriya.

Sojojin Nijeriya a bakin aiki.


Sojojin Nijeriya a bakin aiki.

 

 

Ku sani mazan fama da ke tsare kewayen Nijeriya,

Ku tuna da alƙawari na rantsewarku kan Nijeriya,

Daraja mutumcinku yana ga tsare ƙasar Nijeriya,

Nasara tana banku munai maku addu'a Nijeriya.

 

Rikicin cikin Nijeriya fa barazanar iffirikiyya,

Mutuwar ƙasar Nijeriya mutuwar ƙasar iffirikiyya,

Arzikin ƙasar Nijeriya arzikin dukkan iffirikiya,

Har wa yau zaman Nijeriya lafiya zaman ifirikiyya.

 

Ko duniya fa muna sahun na bakwai ƙasar Nijeriya,

Kan tattali da ma'adanai na ƙasar uwa Nijeriya,

Fanni na sojoji Afurka fa ba kamar Nijeriya,

Duk duniya an san ƙasa ta uwa uba Nijeriya.

 

Kada kul ku bar ƙofa ta masu shirin rabe Nijeriya,

Kada kul ku saurara ga ta da ƙaya ta ban Nijeriya

Rikicin ƙabilanci da addini ya bar Nijeriya.

Peace and unity muke fata ƙasar Nijeriya.

 

Nasarun minallahi

Mazan fama

Gidan soja

Ki gudu sa gudu

Tamburan soja

Gidan jaji

Daga Diwanin Waƙoƙin Aminu Ladan Abubakar (ALA)

Post a Comment

0 Comments