Ticker

6/recent/ticker-posts

8.14 Alan Waƙa Zai Koma Gida - Daga Diwanin Waƙoƙin Aminu Ladan Abubakar (ALA) (Page: 415)

Yakasai, S. A. & Sani, A-U. (2021). Diwanin Waƙoƙin Aminu Ladan Abubakar (ALA). Kaduna: Amal Printing & Publishing Nigerian LTD. ISBN: 978-978-57624-9-0.

Alan waƙa ka koma gida,

Alan waƙa zai koma gida.

 

Mai mota ka kai mu gida,

Alan waƙa zai koma gida.

 

Kyan tafiya a waiga gida,

Mai tafiya a dawo gida,

Mai tafiya a gai da gida,

Alan waƙa zai koma gida.

 

Da an cirani a koma gida,

Da an samo a kawo gida,

Mai tafiya ka waigo gida,

Alan waƙa ya dawo gida.

 

Na je Jos na ci kasuwa,

Mai mota ka kai ni gida.

 

Bisimil Ƙadiri Al-muƙutadiri Ubangijin rani da damina.

Ubangijin da yai gumi yai ɗari yai bazara yai bana,

Shi ya yi baɗin baɗaɗa ka yarda burus kaya Rabbana,

Rabba ka amince mun in tsara waƙa kan tafiyarmu bana.

 

Kai ran nan mun yi baƙar tafiya,

Domin mun tako ƙarangiya,

Mun yi gamo gamon hatsaniya,

Gamo da sojojin kan hanya,

Falgorin daji kan hanya,

Nan aka ce mu tsaya muka ƙiya,

Sojoji sun san kan tsiya,

Ashe a can gaba za mu tsaya,

Don ko babu gada bisa hanya,

Da komowarmu sunka tsaitsaya,

Kan titi da shirin hatsaniya.

 

Sojoji sun ba mu ruwa,

Alan waƙa ya komo gida.

 

Sojan da ya shuna mani bindiga,

Kamar Ahamad kulu da bakara.

 

Ga mu a mota an rufe gilas,

Ala ran nan ya takura.

 

Rana na kuɗar mu,

Ga shi ba iskar shaƙa don a tsira.

 

Ga sharkaf mu kay yi gumi,

Kamar tsami na ruwan jakara.

 

Isa Ɗahiru ɗan Yakasai,

Yana kyarma yanai masassara.

 

Ya yi ƙumaji ya yi ƙamiri,

Kamar gishirin annir a ruwa.

 

Lawan direba ya takura,

Zuciya tasa ta tunzura,

Fuskarsa ta botsara,

Lamarin fa ya ta’azzara,

 

Kamar zakaran da an ka yi wa,

Tawai da aka tsoma ruwa.

 

Koko in ce kamar shamuwa,

Ma sha ruwa,

A ruwa.

 

Da suka sake mu muna kan hanya,

Ba sassaucin buɗe wuta.

 

Isa Ɗahiru yaɗ ɗau tabarsa,

Da ashana ya aza wuta.

 

Ba musu ya fesa sama,

Can na ji ƙara naf firgita.

 

Motarmu na wantagaririya,

Tai wata ƙara mai firgita.

 

Ƙara ce mai sa firgita,

 

Ashe taya ce tai bindiga,

Muka ja birki mai tunga,

Muka sa safaya ga da ga,

Tafiyar ga munka raya,

Muna Allah ka kai mu gida.

 

Na aje motar malti midiya,

Da isa muka bi motar haya.

 

Da muka fito daga Na’ibawa,

Sai Jos ne fa munka tsaya.

 

Kuma mun yi dare ƙarfe takwas,

Fa ba babur nah haya.

 

Ana ta ruwa sanyin garin nan,

Yai mana shegen duka ta tsiya.

 

Mun yi jagab mun yi sharkab,

Kamar tsummar shanya a ruwa.

 

Ga yunwa tana sukuwa,

Cikina na rugugi na tsiya.

 

Ga shi garin Jos ban san kowa ba,

Babu fa inda za ni tsaya.

 

In mun ga mutum yana tafiya,

Da mun ce malam ga tambaya.

 

Sai ka ga ya ruga a guje,

Yana tsoron cuta da wuya.

 

Mun je hotel har kashi biyu,

Kuɗinmu fa ba su isa mu biya.

 

Muna tafiya sai nai tsinkaya,

Da mai masara a gefen hanya.

 

Nai azamar yiwo guzuri,

Ina tsoron kwana da yunwa.


Sai nai azamar na dawo gida.

Daga Diwanin Waƙoƙin Aminu Ladan Abubakar (ALA)

Post a Comment

0 Comments