Ticker

6/recent/ticker-posts

8.13 Sakkwaton Usmanu - Daga Diwanin Waƙoƙin Aminu Ladan Abubakar (ALA) (Page: 413)

Yakasai, S. A. & Sani, A-U. (2021). Diwanin Waƙoƙin Aminu Ladan Abubakar (ALA). Kaduna: Amal Printing & Publishing Nigerian LTD. ISBN: 978-978-57624-9-0.

Amshi 

Sakkwaton Usumanu ga baƙo da ba na husuma ba,

Alan Kanawan dabo mai tambari da waƙar faɗakarwa.

 

Shimfiɗa

Allah tsare min harshe, kar na zamo a masu zinar zance,

Da zazzaɓin kan harshe ka ba ni magani in yi sirace,

Don ka raba ka ba ni Allah hana da ayyi min fauce,

Shi rabo managarci, ai rayuwa da kyakkyawan dace.

Duk mai awo na fahimta, shi ke da ribatar ribar zance.

Da rayuwa da kininta, ribarsu na ga aiki ingance.

Kamar fitar harsashi, hakanga ni nake zarafin zance,

Da na naɗa na ƙulla sai masu nazzari kan sinsince,

Yau Sokoton Usumanu, ga ni a jami'a a dabarbarce,

Kolo gaban malumma, ai dole yai ɓari ya yi sambace.

 

Alhamdu lillah Allah kan goɗiya muna kakkarawa,

Fi sabilillahi lillahi wahidun mun godewa,

Hasken fasaha Allah ka ba ni kai daɗin bunƙasawa.

Malikuddayyanu kai min tsari da in yi zinar zance.

 

Tsira aminci Allah ƙara wa Musdafa sirrin zance,

Sirril kalami nabiyu, mai kyan hali da daddaɗan zance,

Ya nural anwaru bautar gumaka yau ya magance,

Mai gargaɗi da bushara tsani da kai idan an yi an dace.

 

Hallanzu dai soyayya ce ta saka nake yin bakance,

Alkawari na ɗauka zan zo ni Sakkwaton Usumanu ce,

Domin ganin farfesa na Hausa ni da shi fa mu tantance,

Gamon jinin soyayya da ni da Salisu babban zance.

 

Bawan masoyi ne ni, a kan batu na ƙauna ba zaɓe.

Ni ba ni raina masoyi, balle a ce tsakani nai zaɓe.

Ina rawa da bazarku, ya za a ce tsakani nai zaɓe.

Allah ka bar mu da ƙauna, ka sa rabon shiga aljanna ce.

 

Wani cikinsu masoya, burinsa yag ga dai na yo zarce,

Ko da cikin salloli koko a nafila ƙarshen zance.

Babu dare ko rana fatansa Rabbana a cikin zance.

Allah ya ɗaukaka Ala, ya tsere tsaraki nai yai ficce.

 

Kowa a nasa bigiren, yanai da gwargwadon ƙarfi nasa,

Wani yanai da kuɗinsa, wani da illimi ba sa-in-sa,

Wani ya nai da ziyara, kowansu ni ina yaba ƙaunarsa,

Allah ka bar soyayya Allah ka sa rabon aljanna ce.

 

Yau ga ni birnin Shehu, na zo da tamburan soyayya ne,

Na gurin farfesa da ɗalibai zuwan na zumunci ne,

An ce da ni yaba ƙauna, tukuicin ya zamma zumunci ne,

Allah ya bar soyayya da ni da Salisu albarka ce.

 

Buri gare shi masoyi, ya dai ga ga shi ga ko abin sonsa,

A yanzu ga ni gareku, ALA da kansa har da wazirinsa,

Na sam cikar burina, don na ga Salisu a muhallinsa,

Ko yanzu na bar waƙa, motsin da nay yi tsabar riba ce.

 

Ga addu'a ta masoya, duk inda sukke Allah kare su,

Allah zamo gatansu, Allah hana wa sharri yab bi su,

Da su da mai ƙaunar su, Allah tsare su sharrin sususu,

Ka bar mu har aljanna, domin zumin zumuntaka soyayya ce.

Daga Diwanin Waƙoƙin Aminu Ladan Abubakar (ALA)

Post a Comment

0 Comments