Yakasai, S. A. & Sani, A-U. (2021). Diwanin Waƙoƙin Aminu Ladan Abubakar (ALA). Kaduna: Amal Printing & Publishing Nigerian LTD. ISBN: 978-978-57624-9-0.
Rayuwa abar riritawa,
Lafiya abar alkintawa,
Sai da lafiya aka komai,
In babu lafiya ka zam hoto.
Bisimilllah Sarkin baiwa,
Wannan da ya kaɗaita a bautawa,
In da lafiya mui bauta,
In babu lafiya ko ya yafewa,
Ga yabo gurin Manzona,
Ɗan Abdu Annabi a gurin kowa,
Da wanda sukai amanna,
Har ma waɗan da sun kafircewa.
Ilimi madubin kowa,
Mai armasawa harkokin kowa,
Sai da lafiya a ka yin sa,
In babu lafiya bai samuwa,
Ko idan fa ka same shi aiki da lafiya yaka motsawa,
Lafiya nake yi wa baiti waƙen ga sai da ita ka harbowa.
Sai da lafiya aka bauta,
Bautar Ubangiji mai yayewa,
Sai da lafiya aka nema dan tara dukiyar alkintawa,
Sai da lafiya aka gayu masu ayyuka dan birgewa,
Sai da lafiya aka mulki in babu lafiya ka zam gawa.
Sai da lafiya aka iko ikon sarautakar mai mulkawa,
Ai zubi na tsarin mulki ga Hakimai da jerin fadawa,
A yi karagar mai mulki ga figinai suna fiffitawa,
Ɗa ma ana na maka take ƙi gudu sa mazaje tserewa.
Sai da lafiya aka iko ikon sarautakar mai mulkawa,
Ai zubi na tsarin mulki ga Hakimai da jerin fadawa,
A yi karagar mai mulki ga figinai su na fiffitawa,
Ɗama aba na ma ka take ƙi gudu sa mazaje arcewa.
Sai da lafiya aka gwamna ko shugaban ƙasa mai mulkawa,
Da mahauni ga SS ga jami’an tsaro na gilmawa,
Sun ci ɗamarar ta kwana ga bindigu da hodar fesawa,
Sai da lafiya suka motsi in babu babu ikon harbawa.
Sai da lafiya aka noma ai sassabe a kai har girbewa,
Ko saye da mai saidawa duk sai da lafiya aka ƙullawa,
Ka jiyo amon Ɗankoli na talle san da yake zagawa,
Aikatau da aikin ƙarfi jarinsu lafiya gun talakawa.
Ko da fagen ‘yan yara sai in da lafiya kan darawa,
Haka saurayi da budurwa sai in da lafiya kan soyewa,
Lafiya ake wa aure mai sa a kai ga samun haihuwa,
Dariya idan an yi ta takenta lafiya ke nunawa.
Haka saurayi da budurwa sai in da lafiya kan soyewa,
Lafiya ake wa aure mai sa a kai ga samun ƙaruwwa,
Dariya idan an yi ta takenta lafiya ke nunawa.
Rayuwa idan ta samu ruhinta lafiya mai ɗorewa,
Lafiya idan ka rasa ta saƙon na mutuwa ke nunawa,
In na ce gwada mini wawa nuna shi wanda bai alkintawa,
Sai da lafiya aka komai mun yarda kafin alkintawa.
No comments:
Post a Comment
ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.
HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.