Ticker

6/recent/ticker-posts

8.11 Astagfirullah - Daga Diwanin Waƙoƙin Aminu Ladan Abubakar (ALA) (Page: 409)

Yakasai, S. A. & Sani, A-U. (2021). Diwanin Waƙoƙin Aminu Ladan Abubakar (ALA). Kaduna: Amal Printing & Publishing Nigerian LTD. ISBN: 978-978-57624-9-0.

Abin da na yo bisa kure Sarki Allah,

Gare ka nam miƙa wuyana ya Allah,

Astaggafirullah,

Astaggafirullah.

 

Abin da kullum naka raya shi a rayina,

Da abin da kullum naka ganin sa da idona,

Abin da kullum naka jin sa a kunnena,

Da abin da kullum naka faɗin sa harshena,

Da abin da kullum naka tuna a ƙwaƙwalena,

Da abin da kullum naka taɓa shi da hanuna,

Da wajen da kullum naka zuwan sad a ƙafafuna,

Da abin da na yi da gangan bisa ra’ayina,

Da abin da na yi rashin sani yash sha kaina,

Astaggafirullah,

Astaggafirullah.

 

Abin da na yi saƙar sa da fusahata,

Da abin da nai yi na isar da hikimata,

Da abin da na yi da ‘yan dabaru na fasalta,

Da abin da nab biye wa son zuciyata,

Da abin da nay yi ya wuce can na manta,

Da abin da nay yi yanzu Allah gafarta,

Da abin da zan yi gobe Allah gafarta,

Sarkina kar ka bar ni ni da dabarata,

Jallallah ba tsumi garen da dubara ta,

Astaggafirullah,

Astaggafirullah.

 

Ya Allah Al-Mudabbiru mai juyarwa,

Ya Allah Al-Musawwiru mai sauyawa,

Sarki mai juya zamani mai shiryawa,

Bawanka ya ga zamani mai rikitarwa,

Na duƙa na yi ƙas da kai na dan huruwa,

Yarje min na cika da ƙarshe kyawawa,

Sarkina kar ka bar ni nay yo dambarwa,

Gwadabena na riƙe marsashin gantsarwa,

Nurullaha ɗa ga Ƙuraishawa,

Astaggafirullah,

Astaggafirullah.

 

Ya Allah Allah Rahmanu Rahimu buwayi,

Ya Allah Almaliku Ƙudusu buwayi,

Ya Allah As-Salamu Muminu buwayi,

Allah Al-Muhaiminu Azizu buwayi,

Ya Allah Al-Jabbaru Ƙahhara buwayi,

Ya Allah Al-Wahabu Razaƙu buwayi,

Ya Allah Al-Fattahu Alimu buwayi,

Ya Allah At-Tawwabu Ganiyu buwayi,

Nai tsani Allah da kai ba wani shayi,

Astaggafirullah,

Astaggafirullah.

 

Kai na riƙe garkuwa muhallin kwancina,

Kai na riƙa mai tsaro muhallin tashina,

Kai na riƙe kaliƙi muhallin tafiyata,

Kai na riƙa sanda fargabba tash shiga raina,

Kai na tuna tuntuɓe idan nai da ƙafana,

Kai na riƙe in larura ta sha mini kaina,

Kai na riƙa san da maƙƙiya suka rufu kaina,

Kai na riƙe san da nar rabauta da mai so na,

Kai na riƙe lokacin da nar rasa Abbana,

Astaggafirullah,

Astaggafirullah

Daga Diwanin Waƙoƙin Aminu Ladan Abubakar (ALA)

Post a Comment

0 Comments