Ticker

6/recent/ticker-posts

7.5 Galadiman Udubo- Daga Diwanin Waƙoƙin Aminu Ladan Abubakar (ALA) (Page: 291)

Yakasai, S. A. & Sani, A-U. (2021). Diwanin Waƙoƙin Aminu Ladan Abubakar (ALA). Kaduna: Amal Printing & Publishing Nigerian LTD. ISBN: 978-978-57624-9-0.

Amshi:

Galadiman Udubo shatiman Jama’are abin yabo,

Magaji Muhammadu Duwa Custom Comptroller ina yabo.      

 

Alhamdulillahi Ubangiji mai mallakin mu gaba ɗaya,

Buwayayye masanin fake da sirri namu gaba ɗaya,

Ka ƙara amincinka duka ga Al’arabiyu abin biya,

Da alaye da sahabihi da tabi’ut tabi’u bai ɗaya.

 

Buwayayye masanin fake da sirri namu gaba ɗaya,   

Ka ƙara amincinka du ka ga Al’arabiyu abin biya,

Da alaye da sahabihi da tabi’ut tabi’u bai ɗaya,

Alhamdulillahi Ubangiji mai mallakin mu gaba ɗaya.

 

Yabo yau zan ga abin yabo mai halaye duka na yabo,

Magaji Muhammadu Udubo ka ɗauki kaso guiwar rabo,

Idan aka ce guiwar rabo da mun guiguiwar rabo,

Da yardar Allah mai rabo sai ka zama tauraron yabo.

 

Abin da ya sa naɗ ɗau ƙalam na tashi nake yi ma yabo,

Abin da kake wa al’umma ya kyautu a tsara ma yabo,

Abin da kake wa addini ya kyautu a shirya ma yabo,

Masallatai ka giggina ka gyara waɗansu tsubo-tsubo.

 

Da na shiga birnin Udubo ana ta yabon ka tsubo-tsubo,

Ƙauye da maraya Udubo ba inda ba kai abin yabo,

Ka giggina burtsatse kuma an samu salama sai yabo,

Kai rijiyoyi Udubo da kansu suna fatan rabo.

 

Waɗan da ka sa suka dogara da kansu ba za su ƙidayu ba,

Ka kai su abin yi federal haɗa da state ba a ƙi su ba,

Haɗa da matakin gunduma ka ba da scholarship uba,

Da mai galihu da mara shi ba wanda ba kai wa abin yabo.

 

Da mai galihu da mara shi ba wanda ba kai wa khairu ba,

Waɗan da ka sa suka dogara da kansu ba za su ƙidayu ba,

Ka kai su abin yi federal haɗa da state ba a ƙi su ba,

Haɗa da matakin gunduma ka ba da scholarship uba.

 

Maza mata na yi maka na yi maka fatan khairu har can gaba,

Yara manya na yi maka fatan fatan khairi gaba,

Malamai ma su faɗa a ji suna ba su sami kamar ka ba,

Sarakai na ai Ɗanmu ne albarka ma sai can gaba.

 

Meye sirrinka Galadima ka ba ni na samu na taƙama,

Sirrin laƙani na farin jini ka bani in shafa mui kama,

In sam daraja makamanciya da taka in zam mai taƙama,

Ko ba mulki ba dirhami in san daraja daga al’umma.

 

Ina zaune a cikin gida Umar ya kira ni da Udubo,

Ya ce ALA ka ci ɗamara yabon na gwanaye abin yabo,

Galadiman Udubo muke so kai wa yabo da abin yabo,

Abin faharin ‘yan Udubo ɗan dattigaɓo ina rabo.

 

Mai kyauta babu nufin riya Galadiman Udubo gari,

Mai tausayi ne mai haƙuri Galadiman Udobo gari,

Mai sauƙin kai mai kyauta yi sannan ba ya alfahari,

Magaji Muhammad ‘yan maza abin faharin jama’ar gari.  

 

Mai alkhairi ba ya rashi Shatima abin faharin gari,

Mai jin kai ba ya tasgaro Galadiman Jama’ar gari,

Abin da ka so jama’a ta so Allahu yana albishiri,

Shaidar jama’a muka bibiya ka tabbata jinsi na gari.

 

Irinka ake wa wakiltakar mutane ba baragurbi ba,

Mai son jama’a mai taimako shike mulki ba aibu ba,

Mai ba da abin da ya mallaka ake wa naɗi ba o’o ba,

Allahu ya ida abin na nufi abubaka zan wa farin uba.

 

Alhaji Bashar Magaji naka ya ɗau nauyin waƙar uba,

Na gode Bashari maza madallah Bashari maza ga waƙa ta farin uba,

Ga waƙa ta farin uba ina waƙa ta farin uba,

Madallah da farin uba.

Daga Diwanin Waƙoƙin Aminu Ladan Abubakar (ALA)

Post a Comment

0 Comments