Ticker

6/recent/ticker-posts

Ruhanai

Yakasai, S. A. & Sani, A-U. (2021). Diwanin Waƙoƙin Aminu Ladan Abubakar (ALA). Kaduna: Amal Printing & Publishing Nigerian LTD. ISBN: 978-978-57624-9-0.

Mallam Amadu mai ruhani,

Mallam Amadu mai ruhani,

Kun ji gamon ALA mai waƙa da,

Mallam Amadu mai ruhani.

 

Zan nemi tsari gun Sarki Allah da akai na shaiɗanu zan hani,

Tsare ni tsarewa ya Allahu raba ni da ruɗin ‘yan zamani,

Ka ba ni wadatar zuci Allah ka sa na fi ƙarfin duk sheɗani,

Ya Allahu ya Ƙayyun na yi tawassili da Ƙur’ani.

 

Ka ƙara daɗin tsira ya Allah ga Ahmadu Mamudu bawan Allah,

Manzon baiwa ɗan Abdallah Muhammadu mai kwana yin sallah,

Tsira da aminci ya Allahu da alaye nasa bayin Allah,

Haɗa Asahabi ya Allah abin koyin bayinka Allah.

 

Ran Juma’a bayan almuru na hikima ni ɗaya al’umma,

Sai ga mota ta alfarma tai fakin da direba mai kima,

Ya zo shi sayen kaset a hikima ya ce wai ina Alan al’umma?

Na ce masa ni ne Alan waƙa yai mamaki ƙirar hamma.

 

Ya ce mini ALA ka burge ni da ka yi waƙar Sarki mai girma,

Sarki Ado Ɗan Bayero mai temako gurin al’umma,

Ya ɗauko alkhairi ya ba ni ya ce ci tukuici dan alfarma,

Albarkacin Ado Bayero da kai wasa shi cikin al’umma.

 

Mu kai ekscenjin lambar waya mukai ban kwana da mai ruhanai,

Ga shi gari da sanyin safe za shi Abuja mai ruhanai,

Ya zo muka tattauna ni da shi na ce masa nemi anan ruhanai,

Ya ce mini aiki ne ya saka ake mani inkiya da ruhani.

 

Ni na ga abin ai ban mamaki da Mallam Amadu mai ruhani,

Na ga abin zamɓam al’ajab da Mallam Amadu mai ruhani,

Kuma na ga karamar wannan ƙarni ga Mallam Amadu mai ruhani,

Toh ya ƙasaita ya gawurta ya tumbatsa mai ruhani.

 

Ya ba ni du’a’i in lazimta ya ce da fa an mai rauhani,

Ya ce mani sharrin ɗan Adam da aljan ka kere a zamani,

Ya ce mani kar kai hasssada ga kowa ko ƙyashi a zamani,

Ashe Mallam babban gwarzo ne a fannin karatun Ƙur’ani.

 

Ya ba ni du’a’i in lazimta ya ce da fa an mai rauhani,

Ya ce mani sharrin ɗan Adam da aljan ka kere a zamani,

Ya ce mani kar kai hasssada ga kowa ko kyashi a zamani,

Ashe Mallam babban gwarzo ne a fannin karatun Ƙur’ani.

Daga Diwanin Waƙoƙin Aminu Ladan Abubakar (ALA)

Post a Comment

0 Comments