Ticker

6/recent/ticker-posts

Kwamishinan ‘Yan Sanda Faruk Usman Ambursa

Yakasai, S. A. & Sani, A-U. (2021). Diwanin Waƙoƙin Aminu Ladan Abubakar (ALA). Kaduna: Amal Printing & Publishing Nigerian LTD. ISBN: 978-978-57624-9-0.

Amshi:

Kwamishinan ‘yan sanda Faruƙ Usuman Ambursa ka biya,

Ka zamo linzami maganin sakakken doki ka biya.

 

Ɗan halak ka fasa Ummaru ne a filin daga,

Awartakin riƙe ƙarfe ko in ce da shi alharƙa,

Ƙwal uwa gun dakka da mai ƙiriniya da ayaga,

Rahamar al’umma zuwan Ummaru filin daga,

Mai igwa mai tanka artabu sai a filin daga,

Ummaru ne linzami maganin sakakken doki,

Lafiya ta san wa zuwanka Ummarun Ambursa,

Lafiya tas samu Kaduna ko’ina muka zaga,

Don Ummarun Ambursa kowa yana ta yin son barka.

 

Komai na zo zan fara in dai abin fa zai yi ƙabuli,

Sunan abin tinƙaho a shimfiɗa fa kafin ƙauli,

Da nai hakan an ƙare zan warware dukannin ƙulli,

Allahu zai dube ni aikin ya zamma gagara gasa,

Kin biya.

 

Allahu kai na kirawo ka tallafe ni in da na kasa,

Da rayuwa da kininta kai ka so na ƙasan mulkinsa,

Samu rashi bunƙasa suna a ƙarƙashin mulkinsa,

Sarkin da bai runtsawa nan na tashi zan nufin gunsa,

In biya.

 

Allahu don manzonka wannan da ka kira shi sama’i,

Sayyidul sahadati da kan nufe shi yai isira’i,

Baitul muƙaddasi zango har sai da ya ishe ka sama’i,

Mai so da ƙaunar Mammam na tsare ni har Ambursa magiya.

 

 

 

 

Zan yabon hamshaƙi yau kwamishinan ‘yan sanda,

Mai gaskiya da amana mai hana fajirai ɗaga sanda,

Gugu uwar fangoma ga faɗuwar gaban mai sanda,

Ni na gani na shaida hali na Ummarun Ambursa zan biya.

 

Abin da ke burge ni daga hali na ɗan Ambursa,

Riƙo da tsoron Allah ciki na dukkanin aikinsa,

Riƙo riƙon addini don ba shi sakaci ko wasa,

Allah yana bayanka Umar Ussuman Ambursa na biya.

 

Wanda ke riƙe salla an ce tana hanin alfasha,

Tana hanin aikin tir sannan tana hanin alfasha,

Na zam ganau kan wannan wallahi Ummaru kai ka sha,

Gama ka riƙe yin salla yin ta ba shi babu makusa ka biya.

 

Fage na harkar aiki Ummaru bai gudu don tsoro,

Masu tsoron Allah babu abin da za su yi tsoro,

Uban maza mai horo kyauta kamar da indararo,

Yanzu za ni kirawo ‘yam maza a harkar aiki in biya.

 

A Guiwa lokal gommen Ummaru yai riƙon DPO,

Jega lokal gommen Ummaru yai riƙon DPO,

A Tsage lokal gommen Ummaru yai riƙon DPO,

A Gumi Garki Abuja Ummaru yai riƙon DPO ya biya.

 

A Sakkwaton Usumanu Ummaru yai riƙon Two IC,

Can a birnin Zazzau Ummaru yai muƙamin AC,

Area fa commandor Abuja ya riƙe ikilasi,

Area fa commandor Jimeta ya riƙe bil hakki gaskiya.

 

Area fa commandor Ummaru ya riƙe Zariya,

Area fa commandor ya yo a Katsina alƙarya,

Yai muƙamin DC Abuja capital alƙarya,

Kwamishinan ‘yan sanda Ummaru ya riƙe Nasarawa ya biya.

 

 

A yau yana a Kaduna da tambarin muƙamin CP,

Wane rago ɗan nema ba duk jiki ba rigar CP,

Rago da rigar saƙi wane rago da rigar CP,

Gobe sai AIG fata ga Ummarun Ambursa na biya.

 

Ka ji bokkar daji toro uban maza ƙi faɗi,

Ga giye mai kiyo shi shi kaɗai inai ma taɗi,

Mai fita operation shi shi kaɗai su gan shi su faɗi,

Abin da kai mini Ummar na zo gida ina ta nishaɗi ka biya.

 

Kura mabi almuru baban Amina baban Zara,

Nai tambari nai waƙa Alan mutan Kano wan Zara,

Miskilin mai waƙa idan na yi ta sai an lura,

A yau yabon Ummaru ɗan Usumanu ɗan Ambursa zan biya.

 

Taƙadarin mai waƙa nakan ji mai nazar ya furta,

Ko gagarin ɗan waƙa mais a makwaikwaya yin mita,

Taƙadarai kuma waƙa mukan taɓa ta har da gwaninta,

Ubangiji ya hore ya tallafe ni ya zam ka sa in biya.

Daga Diwanin Waƙoƙin Aminu Ladan Abubakar (ALA)

Post a Comment

0 Comments