Ticker

6/recent/ticker-posts

Farfesa Sa’idu Muhammad Na Gusau

Yakasai, S. A. & Sani, A-U. (2021). Diwanin Waƙoƙin Aminu Ladan Abubakar (ALA). Kaduna: Amal Printing & Publishing Nigerian LTD. ISBN: 978-978-57624-9-0.

Ga ka farfesa,

Ga ka katibi kan adabi,

Sannu farfesa Sa’idu ɗan Muhammadu na Gusau.

 

Rabbi na gode da dubun basira da ka ban,

Kuma na gode da tulun basira ka zuban,

Falalar Allah da ka ba ni a watan Sha’aban,

Ka tsare min ita kar ya zam ta zam tai nusau.

 

Gaisuwa gun Mahmudu ɗan ƙabilar Arabi,

Sayiddul umma ga cikamaki gunsu Nabi,

Sayyidul akalaƙi abin a dube shi a bi,

Na yi tsani na da biyar sa sawu fa da sau.

 

Yau akala na karkata na tunkari Gusau,

Zan yabon masani mutafanninin nan na Gusau,

Wanda yai harsasai kala-kala yamma ya sau,

A fagen ilimi yau da gobe ya zamma da sau.

 

Wanni ya ce ALA me za ka kallo a Gusau?

Wa kake so ka kwarzaza ka wasa a Gusau?

In kuɗi anka ba ka ai Kano ta fi Gusau,

Ko fagen bunƙasa da yalwata sun fi Gusau.

 

Dakata in ana ƙi gudu ba sa gudu ne,

Yada ka ji ana ga maɗi ba mai zuma ne,

Ba kitabul ra’asi gunsu fesa shi gwani,

Ni ganau jiyau na zam a kan Sa’idu na Gusau.

 

Maƙurar lauya idan ka ce SAN hakane,

Sanda duk ka ji gangaran gwani ƙure anne,

Sanda duk ka ji an taru to fagen yaƙi ne,

Maƙurar ilimin zamani kwa farfesa a sau.

 

 

Wani farfesa ne a ɓangaren Turanci,

Wani doktore ne a ɓangaren Larabci,

Shi kwa mutafannini a ɓangaren Larabci,

Kuma farfesa ɓangaren adab ɗa a Gusau.

 

Masanin harshen Hausa ɗan Muhammadu na Gusau,

Masanin luggar Hausa ɗan Muhammadu na Gusau,

Manazarci ne katibi da yam mamaye sau,

Ya yi fintinkau da tarar shi za a yi ginsau.

 

Adabin Hausa na yaba ka farfesa Gusau,

Manazarta ma ka yi tubali sun ɗara sau,

Littafan turƙe da dabarbaran Hausa kasau,

Har da ta’alifai na saya da dama a Gusau.

 

In yana Larabci da za a sanya hijabi,

Sai ka ce masa makkiyu kuma ƙabilar Arabi,

In yana Turanci lakata harshen adabi,

Sai ka ce Banasare da yai ɓatan kai a Gusau.

 

A fagen harshen Hausa gangaran ka fi gwani,

In yana Magana baguragura gun koyi,

Sai ka ce maɗari ke zuba da jera tunani,

Ga azanci ga hikkima a gun ba gimsau.

 

Alan waƙa yake yabon ka dan ka ɗara sau,

A fagen waƙa kai rubutuka sun fi casau,

Haka labaran ƙage kai nazar kansu a sau,

Binciken ALA da yawansu taskarka Gusau.

 

Shehu ɗan Shehu ɗan Muhammadu ɗan kullum,

Shehu ne tammi a gurin Gusau ɗan kullum,

Ɗan uwan Mallam shehu na’ibin ɗan kullum,

Ɗan uwan alƙali na alƙalan yanzu Gusau.

 

Na taho murna yau kake bikin taka ɗiya,

A walimar nan ta Sa’adatu gunka ɗiya,

Ala san barka da zaman lumana amarya,

A cikin waƙar gangaran na yankinmu tisau.

Daga Diwanin Waƙoƙin Aminu Ladan Abubakar (ALA)

Post a Comment

0 Comments