Ticker

6/recent/ticker-posts

Taken Maza Buratai

Yakasai, S. A. & Sani, A-U. (2021). Diwanin Waƙoƙin Aminu Ladan Abubakar (ALA). Kaduna: Amal Printing & Publishing Nigerian LTD. ISBN: 978-978-57624-9-0.

Shimfiɗa

In ka ji taken maza da bamban da na mazajen ɗaka,

In ka ji sautin maza da bamban da na maroƙan baka,

Soja mazajen dawa da ke tattaga mazajen ɗaka,

Tambayi ‘ya’ya maza a Sambisa sa shaida maka,

Tambayi ‘ya’yan mazan garin Goza sa shaida maka,

 

Ga artabun maza na Baga ka ji mazan ɓarraka,

Ya yi rawar jinjina a Gambori da aka yi raraka,

Ya yi rawar saluti a Dambuwa ka haɗa Muncika,

Madagali ya shiga da kai nai babu ragin ɗan ɗaka,

Na ji mutanen Chibok suna ga mai gama aikin duka,

Mugulu Mubi da Bama tuni an yi musu fansa duka,

 

Ga Abadas Kukawa da Ganzai na ji suna harraka,

Gaza da Mubargwami da Ɗikwa an gama aikin duka,

Ta da ƙayar baya yau a fili ya zama shiƙar ɗaka,

Ɗan Buratai ƙi gudu ke sa masu gudu raraka.

 

Ka ji kiɗan nassara Allahu ya dafa maka,

Ku haɗa Nijeriya ƙasa ɗaya babu rabon wariya da gaba.

 

Soja abin alfahar hafsan soja turmi sha daka,

Ka shiga kundin ƙasa tarihi ba zai manta ka ba Buratai.

 

Amshi: Gaida mazaje nake Tukur Yusufu mazan taffiya,

Ɗan Buratai ƙi gudu da ke sanya mahara sui gudu mazaje.

 

Na yi daɗin godiya ga Allahu da nake bautata,

Jalla abin yabo da ba nai masa kinin bautata,

Wanda ya ban hikkima na gode ya kuma ninkan ita,

Na kuma duƙa maka rukunin ga na salon bautata.

 

 

 

Sha yabo sha ambato da yaz zamo mana abin kwaikwaya,

Wanda muke bibiya siraɗi mara ƙaho ko ƙaya,

Annabi sha baituka da bege mara abin zolaya,

Cikamakin mursalai macecin masu riƙon gaskiya.

 

Za ni yabon ‘yan maza, za ni yabon ‘yan maza,

Wanda na wa addu’a,

Wanda na wa baituka,

Wanda na wa baitukan barade,

Wanda na wa baitukan mazaje.

 

Za ni yabon ‘yan maza ɗan Buratai sha daka,

Wanda na wa baituka da fatan ya zama ƙwal kan ɗaka,

Wanda na wa addu’a ya zama Chief of Army duka,

Yanzu ko ga baituka na gwarzonta sha ƙundum duka.

 

Wanda ya san illimul nujumi za yai maka jinjina,

Masu bugun ramli in suka yi za su daɗa yin jinjina,

Wanda ya zo shekara ta 1960 akwai maggana,

Shekara ashirin da bakwai nuwamba ita nake maggana.

 

Daga cikin halayyar Buratai ka ga da sauƙin hali,

Ga kaifin hankali tunani da nazarin hankali,

Ga ko riƙon gaskiya amana bisa zubin hankali,

Ga shi da son bincike da jajircewa Tukur adali.

 

Ga ilimi Yusufu Buratai ya masanin tarihi,

Yai digiri Yusufu Buratai fari a kan tarihi,

Na biyu kan falsafa Philosopy da ya yi a tarihi,

Haka a kan Arrabik kawai sai dai a yi maka sharhi.

 

Har a naɗe duniya ba a manta da mazajen jiya,

Su jenaral Geoge C. E Marshal soja mazajen jiya,

Da Wustan Cocil mazaje a yaƙin duniya,

Haka Tukur Yusufu ba a manta shi ba nan duniya.

 

 

Baya bara in tina da sanda ya riƙe Niger Delta,

Ta da ƙayar baya masu satar mai na ƙasar Delta,

Shi ya baje saunarsu maha’inta daga Niger Delta,

Yanzu arewar gabas ya karɓa babu tsagaitar wuta.

 

Lieutenant General Yusuf Tukur Burutai (Nigerian Chief of Army Staff)

 

Lieutenant General Yusuf Tukur Burutai (Nigerian Chief of Army Staff)

 

A sanda ƙasar duniya ta yarda a yanzu muna kan ƙaya,

Sanda aka yo mana hasashe za mu zamo Bosnia,

Sanda aka yo mana tsuruɗen za mu zamo Libbiya,

Sai fa Janar ya ɗane muƙami na riƙe Nijeriya.

 

Arewa yankin gabas kwacokam sun zama Somalia,

In da ka zaga duka kufai ne babu abin moriya,

Mun ga kisan ja’iba na gilla da ya wuce bibiya,

Sai na tuna lokaci na bayi ya wuce a yi tsinkaya.

 

Arewa yankin gabas a yanzu ungulu ke dafdala,

Saboda gawarwakin mutane ungulu ke dafdala,

An kashe ‘ya’ya maza waɗansunsu sun zama a wahhala,

Ba adadin rayukan marayu sai dai a ce lahaula.

 

An kaɗe matattakin Musulmi da na Kirista duka,

An rurrusa mana Masalla gami da Cocin duka,

An yi dashen bom waɗansu sassa birni har ƙauyuka,

An ruguje mana kasuwanni da satar kayuka.

 

Waɗansu an kwantar da su ya dabba ana yanka haka,

Wasu an ɗaure su ne da dutse a sa a ruwa a haka,

Waɗansu an harbu su ne waɗansunsu an ƙona duka,

Mutan Nijeriya Arewa muna kuka haka.

 

Mai amsawar kira ga bayi ya karɓa mana kira,

Ya karɓo addu’a ta bayi ya canzo zakkara,

Ya bai wa Buhari shugabanci ya zamto zakkara,

Ya zaɓo mana Tukur Burratai muna yin kabbara.

 

An ba shi wata uku a kawo mana ƙarshen fittina,

Fitinan Boko Haram ta zamto tarihi ab bana,

A kai saran gaɓa a kai wa Tukur hafsa bana,

Cikin kwanannaki talatin sukay yi ɓatan dabo a gona.

 

Chief of Army Staff Buratai fa ba soko ba ne,

Shi ba soja ba ne a baki kuma ba wawa ba ne,

Yana kishin ƙasarsa Naja kuma ba ɗan rashawa ba ne,

Allahu ka taimaka wa hafsa na soja ya kau da ‘yan ta’adda.

 

 

Da zuwa nasa lutanal jeneral soja sun ɗaukaka,

Daraja tasu ta daɗu musamman kayan aiki duka,

Kayan aiki duka da kayan buƙatu su duka,

A yau duka sansanin ta’adda sun kauce su duka.

 

Da shi aka yi mamaya a Gambori har Gwaza duka,

Soja mazan taffiyaaa

Soja mazan taffiya a daga mazan ‘yan raraka,

Kai da gano Tukur a daga za ka yi mar caccaka.

 

Soja mazajen dawa da ke tattaga mazajen ɗaka,

Ka tambayi ‘ya’ya maza a Sambisa sa shaida maka,

Ka tambayi ‘ya’yan mazan garin Goza sa shaida maka,

Ga artabun maza na Baga ka ji mazan ɓarraka.

 

Ga artabun maza na Baga ka ji mazan ɓarraka,

Ya yi rawar jinjina a Gambori da aka yi raraka,

Ya yi rawar saluti a Dambuwa ka haɗa Muncika,

Madagali ya shiga da kai nai babu ragin ɗan ɗaka,

Na ji mutanen Chibok suna ga mai gama aikin duka,

Mugulu Mubi da Bama tuni an yi musu fansa duka,

 

Ga Abadas Kukawa da Ganzai na ji suna harraka,

Gaza da Mubargwami da Ɗikwa an gama aikin duka,

Ta da ƙayar baya yau a fili ya zama shiƙar ɗaka,

Ɗan Buratai ƙi gudu ke sa masu gudu raraka.

 

Ka ji kiɗan nassara Allahu ya dafa maka,

Ku haɗa Nijeriya ƙasa ɗaya babu rabon wariya da gaba.

Daga Diwanin Waƙoƙin Aminu Ladan Abubakar (ALA)

Post a Comment

0 Comments