Ticker

6/recent/ticker-posts

7.27 Rabbu Yarje - Daga Diwanin Waƙoƙin Aminu Ladan Abubakar (ALA) (Page: 375)

Yakasai, S. A. & Sani, A-U. (2021). Diwanin Waƙoƙin Aminu Ladan Abubakar (ALA). Kaduna: Amal Printing & Publishing Nigerian LTD. ISBN: 978-978-57624-9-0.

Amshi

Rabbu yarje na tsara baituka son kowa,

Gunsa Manzo abin yabo a san dacewa.

 

Rabbana kay yi aringizon salatin baiwa,

Ga madubi abin yabo a kan dacewa,

Shugaban abin biyar ɗafar maƙalewa,

Mabiyata majingina tudun haurewa,

 

Ainul Rahamni,

Nurul Ainaini,

Sahibul Ƙur'ani,

Abal Hasanaini,

Abin yabo gun kowa.

 

Wanda girgije yake bin sa yake masa rumfa,

Wanda anka ganin sawunsa a tsandauri fa,

Wanda ba a ganin sawunsa a yashin nan fa,

Wanda rana ba ta saka shi ya yo inuwa fa,

Wanda yakkira wata ya zo gun ya tsage fa,

Wanda ke ƙamshi ba da turare ba da suffa,

Wanda arna ke ce da shi Aminun nan fa,

Wanda ke kanshi duk jikinsa ko yai zuffa,

Shugaban bil-adama da Rauhanai fa,

Mai kyan zubi da tsari mai kyawun siffa,

Mai ƙyalƙyali wane na tagulla da azurfa.

 

Yau Alan waƙa ke yabon son kowa,

Sayyidil arifina kai nake fa yabawa.

 

Na taso Ubangiji da son wanda ka so,

Da ya dace da a so,

Sonsa ai wasoso,

Zucciya tai naso,

Sonsa ya mamaye sassan jikin duk mai so,

Shi nake so da son aso da ingancin so,

Sabbaba min yaz zamma son ya zamto soso,

Sulluɓe saɓona saboda shi son kowa,

Kogin baiwa,

Mara gantsarwa,

Manzon baiwa,

Manzon kowa, abin yabo gun kowa.

 

Rabbana kai kai manna darrajar dubawa,

Ka tsare mu da kama da dabbar korawa,

Muka zamto tsatso-tsatso abin tacewa,

Salsalarmu ta zama ba halin shafewa.

 

Antal Jabbaru,

Antal Ƙahharu,

Antal Shakkuru,

Masanin Asararu

Ɗahirul Maɗahuru,

Abin biyar bautawa – Bautawa - Kai muke bautawa.

Daga Diwanin Waƙoƙin Aminu Ladan Abubakar (ALA) 

Post a Comment

0 Comments