Ticker

6/recent/ticker-posts

7.28 Ganganko - Daga Diwanin Waƙoƙin Aminu Ladan Abubakar (ALA) (Page: 377)

Yakasai, S. A. & Sani, A-U. (2021). Diwanin Waƙoƙin Aminu Ladan Abubakar (ALA). Kaduna: Amal Printing & Publishing Nigerian LTD. ISBN: 978-978-57624-9-0.

Amshi

Sallu alaika Almusɗafanmu abin koyinmu,

Mu yi gangankon yabo da ƙauna mai ɗorewa.

 

Rabbu ilahu Aminu ALA ya gode ma,

Da ka ban iko nai waƙa gun Manzon girma,

Sayidil luɗufi mai alfarma gun al'umma,

Mai albarka madubin albarka gun kowa.

 

Sallu alaika Almusɗafanmu inai ma lale,

Hubbub ilaika Almusɗafanmu mabuɗin kulle,

Soyayyata da ni da kai ba walle-walle,

Mai albarka idaniyar albarkar kowa.

 

Hubbu ilayya Al'annuwaru abin a yabawa,

Miftahul Jannati haske mai haskawa,

Mai kore duhu farin gani magani ga kowa,

Tsayayyen gwadabe mara gantsarwa gun kowa.

 

Kadarkon hikima ba ai ma shinge ɗan baiwa,

Gwalalon Rahama kowash shige shi ya dacewa,

Gulbin fusaha Aminu dace da sonka baiwa,

Nurun Nuri Sallah alaika kogin baiwa.

 

Hasken haske, walƙiya abar ƙyallawa,

Tsatson tsarki, mai tsarki da tsarkakewa,

Ainun Rahama tsanin gamo da Rahamar baiwa,

Nurul Anwaru zukatanmu suna zambarwa.

 

Sayyidil Anam masoyanka sun fi in ƙirgawa,

Suka ce ALA baka waƙe kogin baiwa,

Da akwai taraki in ka yi Allah zai ma baiwa,

Ka yi albarka ka zam tauraron kowa.

 

 

Rasulullah waƙeka ba a yi da garaje,

Sai da izinin Ubangiji in har ya yarje,

Kayi min luɗufi da hikima kar in yi garaje,

Sarki Allah ina tawassuli da yabawa.

 

Wannan Bahari ba shigar kowan kowa ba,

Sai mai ilimi makusancin Rahama ba wai ba,

Ina jalabi ka min taraki ba zan kauce ba,

Alfarmarka Ubangiji mai kowan kowa.

 

Na yi Sujuda da goshina don neman yarda,

Yarda in zana yarda na rera yarda abin yarda,

Waƙen yardajjenka yarje min in ida,

Bisa salama Ra'ufu Rahimu, afuwan Aiwa.

 

Sallu alaika Sayyidiul Auwalina,

Sallu alaika Sayyidil Akhirina,

Sallu Alaika Sayyidil Nabi'ina,

Sallu Alaika Sayyidil Mursalina,

Sallu Alaika Sayyidil Muttaƙina,

Sallu Alaika Sayyidil Saajidina,

Sallu Alaika Sayyidil Raki'ina,

Sallu Alaika Sayyidil Alamina.

Daga Diwanin Waƙoƙin Aminu Ladan Abubakar (ALA)

Post a Comment

0 Comments