Ticker

6/recent/ticker-posts

7.26 Muhammadu Miftahul Futuhati - Daga Diwanin Waƙoƙin Aminu Ladan Abubakar (ALA) (Page: 352)

Yakasai, S. A. & Sani, A-U. (2021). Diwanin Waƙoƙin Aminu Ladan Abubakar (ALA). Kaduna: Amal Printing & Publishing Nigerian LTD. ISBN: 978-978-57624-9-0.

Amshi

Muhammadu miftahul futuhati, linzamin rayuwata.

 

Da sunan Rabbu Ubangiji,

Mai tudawili na dare da rana.

 

Da ƙarfin iko nasa Allah,

Akan ce Rabbul alamina.

 

Da ƙarfin ƙudura tasa Allah,

Kunfa yakunu take gudana.

 

Da ya so zartarwa Buwayi,

A take abin nan zai gudana.

 

Da yas so ƙera sama sama'i,

Cikin kwana shida ta wakana.

 

Da ya so yai a cikin daƙiƙa,

Wallahi kamar kiftar idona.

 

Da sunansa nika togacewa,

A duk farkon al'amarina.

 

Da nai haka buɗi za ya samu,

Ɗiyan waƙa sui ta gudana.

 

 

Da an ji a ce ba shi yake ba.

Fusahar nan in anka tona.

 

Da yardar Rabbu nake bazata,

Babu tsumi wayo a guna.

 

 

Sila ta salati da'iman,

Gun Karibu masoyin kalikina.

 

Sila ta kaɗaitar kaliƙina.

A bautar Rabbu Ubangijina.

 

Silar imanina da Allah,

Da annabi tsanin arzikina.

 

Sila ta shiga ta issilama,

Ya zam hasken al'amarina.

 

Silar in san haƙƙi na Allah,

In yi shi in san kuɓuta da raina. 

 

Sila ta kiyaye hududullahi,

Haƙƙin mai iko da raina.

 

Sila ta sanin haƙƙin sahabbai,

Haɗa ahlil baitin nabina.

 

Silar koyinmu da attaba'u,

Mu san falalar Allah gwanina.

 

Sila ta sanin darajar iyaye,

Da kare mutumcin walidaina.

 

Sila ta in tsarkake kaliƙina.

Da safe da yamma Ubangijina.

 

Na shaida babu abin bautata,

Sai Allahu Ubangijina.

 

Na yarda muhammad ɗan Amina.

Ma'aiki ne bawan gwanina.

 

 

Na yarda da kutubussamawiyyati,

Duk daga Allah malikina. 

 

Na yarda da dukka mala'ikunnan,

Raƙibu Atidu suna biyana.

 

Na yarda da dukkan ƙaddara,

Da ta zo a cikin al'ammarina.

 

Na yarda da kyakkyawa a kaina

Na yarda da mummuna a kaina.

 

Na yarda da komai daga Allah,

Yake ba kokwanto a raina.

 

Na yarda da mutuwa za na koma,

Gurin mai iko kaliƙina.

 

Na yarda da tambayar kabari,

Siraɗin farko 'yan uwana.

 

Na yarda da ranar Alkiyama,

Yaumussa'ati za a zauna.

 

Ranar tsayuwar nan a rana.

Ran sakamako ‘yan uwana.

 

Ranar tafarfasar ƙwaƙwale,

Saboda kusancin kai da rana.

 

Rana ce ta ganin tsaraicin,

Tsaraitattu wannan fa rana.

 

Ranar tonon silili gurin-

Fagalallu 'yan uwana.

 

 

Ranar kuka gun shaƙiyai,

Su ko sa'idai sui ta murna.

 

Ranar yin danasanin Kafurai,

Musulmi za su murna.

 

Rana ta fargabar halittu,

Ranar ceton annabina.

 

Ranar rikicewa da ruɗu,

An nufi Allah Khaliƙina.

 

Ranar mulki ce ga mai shi,

Ba inuwa sai Malikina.

 

Ranar annabi zai kirari gurin,

Allah da ya busa raina.

 

Na yunƙura in yi yabon masoyi,

Annabi ne babban masoyi.

 

Mai darajar da ta zarci shayi,

Mai hali na yabo da koyi.

 

Mai nasaba ciki babu shayi,

Rabbu hane ni da in yi sanyi.

 

Kan lamarin da na tsara zan yi,

In yabi annabi babu shayi.

 

Babu kure ciki ko bulayi,

Sai madarar ƙaunar masoyi.

 

In faɗi tarihin masoyi,

Ku ji busharorin masoyi.

 

 

Babu kasala babu sanyi,

Ba nukusani babu shayi.

 

Kuj ji abin da Yahudu kan yi,

Daga busharorin masoyi.

 

Duka a cikin waƙar da zan yi,

Nutso a cikin bahari fa zan yi.

 

Hujjoji na zuwan masoyi,

Har ahlil kitabi sun yi.

 

Annabi ni a cikin yabonka,

Na nufi in faɗi lamarinka.

 

In yi kirari a gareka,

Sai na yi bitar haƙƙurinka.

 

In faɗi yaƙoƙin ga naka,

Da hijira da ka yo da kanka.

 

In faɗi adalcin ga naka,

Mu'ujizoji tambrinka.

 

Jarumtarka da kwarjininka,

In faɗi Isra'inga naka.

 

Da Mi'iraji da ka je ka,

In faɗi yarda a kai ka jeka.

 

Faɗar Allah wanda yai ka,

Aj ji dalili nak kiranka.

 

Aj ji matakan da ka taka,

A ji abokin rakiyarka.

 

 

Yarda ka je kuma har ka sauka,

Fadar Allah wanda yai ka.

 

Kun ka yi gani ga shi ga ka,

Yai maka marhabin da sauka.

 

Kad da na je ni na fara suya,

Ban saka albassa ciki ba.

 

Farkon fari cikin ruwaya,

Ban yi bayanin haihuwa ba.

 

A tsarin na zubo ruwaya,

Na zarce ban taɓa nasaba ba.

 

A tarihin khairin bariyya,

A ce na yi ban taɓa salsala ba.

 

Tun daga annabi Adamunmu,

Zuwa kan annabi babu aiba.

 

Annabi Ibrahim Khalil,

Badadin Allah ba da wai ba.

 

A 'ya'yansa daga Isma'il,

Banu kinana su kay yi lamba.

 

A nan aka fid da Ƙuraishawa,

Banu Kinana idan ka duba.

 

 

Cikinsu Ƙuraishu buwayayye,

Ya fid da banu Hashim mu duba.

 

Banu Hashim a cikin tsatsonsu,

Ya zo da Ahamadu ɗan Suwaiba.

 

Du'a'in annabi Ibrahim,

Yai maka mar habin da sauka.

 

Rabbana wa ba'as fihim rasulan,

Min hum roƙon annabi.

 

Busharar Isa ibni Maryam,

Rahamatan lil alamina.

 

Mafi falala a cikin halittu,

Mafi daraja daga khaliƙina.

 

Mafi daraja a kason mutane,

Muhammadu maulana nabina.

 

Mafi daraja a kason Ƙabilu,

Badadin Allah annabina.

 

Mafi daraja a cikin gidaje,

Nabiyullahi na gun Amina.

 

A sanda aminatu tai mafarki,

Na hasken zankon annabina.

 

Ya haske duk duniya da haske,

Katangun Sham wane fa rana.

 

Bushara ce aka wa Amina.

Da samun sirril alamina.

 

Annabi hasken shirriyata,

Khairul khalkil alamina.

 

An haifi Muhammadu Litinin,

Sha biyu ga Rabiyul Auwalina.

 

 

Ac cikin shekara ta giwaye,

Ya zo mai Makkatu mai Madina.

 

A sanda su Abrahata suka zo

Su rushe Ka'abar khaliƙina.

 

Ya zo da baraden masu yaƙi,

Dubu ɗari shida don khiyana.

 

Da giwayensa bakwai da toro-

Na giwa sha uku a sanina.

 

Su kai gangankon zai yi fansa,

Da rushe ɗakin Malikina.

 

Abrahata gwamna ne a Yeman,

Na sarki Najjashi a sanina.

 

Ya kwaikwayi ɗakin ka'aba ne,

Yana fahari don isgilina.

 

Sai wanni mutum a banu Kinana.

Ya je ya yi kashi don ya ɓanna

 

Ya harzika sai ya taso mayaƙa,

Da zummar fansa ko a kuna.

 

A nan Allah ya kiyaye ɗakinsa,

Rabbul ka'abati Khaliƙina.

 

Cikin wannan zango ma'aiki,

Ya sauka bayanin malamaina.

 

Waɗansu su ce kafin a yi,

Wa su sanda ake yi malamaina.

 

 

Wasu ko suka ce bayansa ne ma,

Ƙauli uku aka yi wo bayana.

 

Amma babu kure a shekarar-

Giwaye ya iso gwanina.

 

Da ƙaulani a wata na haihuwa-

Khairul khalkil Alamina.

 

Waɗansu ka ce a Rabiyu Auwal,

Waɗansu su ce kuma Ramadana.

 

Amma an taru a Litinin ne,

Ya zo duniya manzo nabina.

 

Waɗansu su ce maka sha takwas,

Wasu kuwa takwas ga wata su zana.

 

Sahihin zance sha biyu ga wata,

Aka haifi abin riƙona.

 

An haifi Muhammadu ba shakiki,

Li abbi li ummi ɗan Amina.

 

Babu ƙani ko wa gare shi,

Abin koyinmu dare da rana.

 

Sai dai baffanni ‘yan uwansa,

Uwa da mahaifi annabina.

 

Aminatu ta ga abin al'ajab,

Ran sauƙarsa abin yabona.

 

Yana a abin al'ajjabi,

Haihuwarsa cikin tsarki nabina.

 

 

Da yankan cibi nai ya sauka,

Da shayi ɗaha abin yabona.

 

Marhabin lale da zuwan ma'aiki,

Madubin bautar Kaliƙina.

 

Marhaban lale da zuwan masoyi,

Naziru bashirun annabina.

 

Marhaban lale da zuwan habibi,

Da yaz zama hasken addinina.

 

Marhaban lale da amintaccen,

Da yaz zam rahmar alamina.

 

Ya tabbata tsarki gunsa Allah,

Maƙara aminci gun nabina.

 

Mahaifin annabi Abdullahi,

Ya rasu kan haifar nabina.

 

Waɗansu su ce daga haihuwarsa,

Ya amsa kiran Allah gwanina.

 

Mafi rinjaye sun wuce kan,

Ya rasu kan haifar nabina.

 

Ya taffi fatauci can ƙasar Sham,

Da ya yi zango a garin Madina.

 

A nan ajalisa ya riske shi,

Ya amsa kiran Allah gwanina.

 

A hannun dangi 'yan uwansa,

Shaƙiƙan ummi 'yan Madina.

 

 

A nan aka binne shi Madina.

Gidansu Mugira bincike na.

 

Muhammadu ya tashi maraya,

Bai riski mahaifi ba nabina.

 

Aminatu ta shayar da manzo,

A yayin raino ɗan Amina.

 

Suwaibatu ta shayar da manzo,

A yayin raino annabina.

 

Da shi da Abu Salama da Hamza,

Suwaibatu tas shayar a jina.

 

Halimatu ta shayar da manzo,

A yayin raino annabina.

 

Da Abdullahi jinin Unaisa,

Da Shema'u bisa bincike na.

 

Ba zan manta ba da Ummu Aiman,

A masu riƙo nai ɗan amina.

 

Barrakatul Habashiya Aiman,

Wacce ya gada ɗan Amina.

 

Wacce ya aurar wa da Zaidu,

Zaid bin Harisa ɗan Amina.

 

 

Wacce ta haifa masa Usama,

Abin ƙauna gun annabina.

 

Kun ji iyayensa na raino,

Da shayarwarsa abin riƙona.

 

A sanda Aminu ya issa yaye,

Halimatu taɗ ɗau annabina.

 

Ta ɗauki mafi tsarkin halittu,

Da albarka duka alamina.

 

An kai shi gurin raino Habibi,

Ya sami ƙwarewa shugabana.

 

Ya sami ƙwarewa da balaga,

Da jarumta kuma annabina.

 

Yana a ta'adar Larabawa,

Ka tashi a ƙauye baina-baina.

 

Ka sam gogewa da makama,

Ka kwan da shirin ko za ta kwana.

 

Ina tuna ran wata ran ma'aiki,

Da Abdullahi suna a gona.

 

Abdullahi na gun Halimatu,

Wanda ta haifa nazzarina.

 

A halin kiwo sai Muhammad,

Ya ce masa je ka ga ummina.

 

Ka ce guzurinmu a yanzu babu,

Ta ba ka mu tai kiwo ƙanina.

 

Yana tafiya kuma ba daɗewa,

Sai ga wasu tsintsaye da rana.

 

Suna magana ɗaya ya yi nuni,

Ya ce shi ne suka dubi juna.

 

 

Ya nuna ma'aikinmu da baki,

Ya ce ai shi ne ɗan uwana.

 

Nan take kawai suka zam mutane,

Farare tas da shigarsu kana.

 

Suka nufi annabi ɗan Amina.

Suka kwantar shi abin yabona.

 

Su kai masa tsaga kirjinsa,

Yana kuma kallo shugabana.

 

Suka ciro zucin ɗan Amina.

Suka gutsiro nama sanina.

 

Akwai wata tasar ma'u zamzam,

Suka wanke da ruwa na ƙauna.

 

Ya ce masa ba ni ruwan dumanina.

Sai ko ya miƙo ba kiyana.

 

Ya sake ƙwaranyawa ma'aiki,

Ruwan nutsuwa gun shugabana.

 

Da yin haka sai suka ɗinke manzo,

Ta hanyar shafar annabina.

 

Nan take wajen ya haɗe da ɗinki,

Su kai tahamida babu ɓarna.

 

A take a gun suka sa sikeli,

Suka aza mai Maka mai Madina.

 

Aka aza bil'adamu goma,

Ya rinjaye su abin yabona.

 

 

Aka aza bil'adamu ɗarri,

Ya rinjaye su Muhammadina.

 

Aka aza bil'adamma dubbu,

Ya rinjaye su abin riƙona.

 

Ya ce da zai zuba duk umumi,

Wa auwalahum wal akhirina.

 

Muhammadu zai rinjaya dukka,

Mafificin Allah gwanina.

 

Suna gama aikinsu nan take,

Suka ɓata ba su ba bayana.

 

Sai annabi ya ji tsoro da hakka,

Ya koma gun ummi nabina.

 

Ya kwashe bayanin da ya faru,

Gareta Halimatu mai amana.

 

Ta ce masa Allah zai tsare ka,

Da sharrin dukka dare da rana.

 

Ta kasa zama a saboda tsoro,

Ta mai da Muhammadu gun Amina.

 

Ta ba ta bayanin da ya faru,

A kansa Muhammadu annabina.

 

Domin haka ta maido amana.

Tana tsoron a taɓa nabina.

 

To kun ji iyakar ɗan Amina.

Da rainon Sadiya mai amana.

 

 

 

Ruwayar nan daga assahiha,

Ɗari uku da saba'in da ukuna.

 

A san da Amina ta je ziyara,

Wajen danginta garin Madina.

 

Tana dawowa za ta Makka,

A daidai Juhufa ban Madina.

 

Tsawonsa kilo mitre ashirin,

Da ukku daga Juhufa Madina.

 

Garin da a kan ce Abbuwa'i,

A nan ajali ya ritse Amina.

 

A nan kabarin sayyada Amina.

Yake abwa'i a can Madina.

 

Yana shekara shida ne Amina

Ta bar shi maraya annabina.

 

Babu uba a garai maraya,

Babu uwar raino nabina.

 

Sai Shaiba ya karɓi riƙon ma'aiki,

Abdul Muɗallabi a sanina.

 

Kaka a guri nasa ɗan Amina.

Mahaifin Abdullah sani na.

 

 

Kafin na wuce ba ku tambayan ba.

Zan ɗan yi bayani baina-baina.

 

A kan hujjar da ake kiransa,

Bawa na Muɗallabi bincikena.

 

Muɗallabi saƙon Hashimu ne,

Shaƙiƙai sukke a bincikena.

 

Hashim kuma silar Hashimawa,

Karimi ne na yabo da ƙauna.

 

Shi ne farko da ya kai fatauci,

Garin Makka daga Sham sanina.

 

Hashimu akan ce massa Amru,

Ya auri fa Salma garin Madina.

 

Ya sauka wajenta daga fatauci,

Ya sake ya koma fita bayana.

 

Kafin ya iso Makka a Palasɗin,

A nan ajalinsa ya zo na kwana.

 

A can kabarinsa yake a Gazza,

Ƙasar Falatsinu abi nufina.

 

Asanda Muɗallabi yaj ji zance,

Na Amru yana da mace Madina.

 

Tana da ciki nasa yai wafati,

Ya shaida hakan nan ba kiyana.

 

Bayan da ta haife ɗa ya girma,

Ya je shi ya karɓo a Madina.

 

 

A wannan zangon Larabawa,

Ana cinikin bayi a baina.

 

Da hango Muɗalibi a hanya,

Yana tafe ga yaro da rana.

 

Shi ya riƙe ragamar taguwa tai

Yana bisa yaron kau da rana.

 

Sai sukka zata ko ya sayo ne,

Muɗallib mai bawa da rana.

 

Ya ce masu ba bawa bane ba.

Ɗa ne a gurin ɗan ɗan uwana.

 

Ɗa ne a gurin Hashimu Amru,

Suna nasa Shaiba 'yan uwana.

 

To tin daga nan takensa ya zam,

Abdul Muɗallib bincike na.

 

Amma kuma ba bawa bane ba.

Kaka nasa annabi ɗan Amina.

 

A ƙarshe shi fa ya zam magajin,

Riƙo na Banu Hashim sanina.

 

Ya gaji Muɗallib a kujerar,

Riƙo na Banu Hashim ku tona.

 

Ya shekara biyu ga kakansa,

Sannan ajali ya taho na kwana.

 

Kakansa ya ce da Abi Ɗalibbi,

Ga jikana nan amana.

 

 

Riƙe shi kama da ɗiyan cikinka,

Ko ma sama da haka ra'ayina.

 

Don ba shi da kowa sai maƙaginsa,

Sai kuma kai da na ba amana.

 

Ya zaunu a gun baban Aliyu,

Abi Ɗalib baffansa kana.

 

Ya shekara goma ta sha biyun ne,

Abu Ɗalibbi ya ce fa ɗana.

 

Na yunƙura za ni fatauci ne,

Ƙasar Sham za ni da kai fa ɗana.

 

Ya kimtsa da kyau kayan fatauci,

Ya ɗauki Muhammadu annabina.

 

A kwana a tashi suna ta zango,

Har dai suka kai zangon bayana.

 

Sun sauka gidan shaihi bahira,

Arrahib mai ilimin a nuna.

 

Ya san ilim Attaura rahib,

Sannan ilimin Injila kana.

 

A da can baya da ayarinsu,

Suna bi har su wuce shi baina.

 

Ba ya ko kallo ko taga su,

Bare fa ya sauke su da kwana.

 

Amma fa a wannan zamanin kau,

Ya tashi ya tarbe su da murna.

 

 

Ya ba su abinci na rai da motsi,

Ya ce masu marhabban a baina.

 

Bayan da suka nutsu sai ya wa,

Abu Ɗalib da su'al a guna.

 

Ina baban wannan gulamin?

Abu Ɗalibbi ya ce ai nina.

 

Ya ce in wanda nake nufi ne,

Maraya zai zama a sanina.

 

Abu Ɗalib kuma sai ya amsa,

Ya ce haka za kuma malamina.

 

Maraya ne ɗan ɗan uwana.

Dukkan lamarinsa yana wajena.

 

Sai yac ce to ga shawarwarina.

Gareka ka ɗauka ba kiyana.

 

Don na ga alamomi da dama,

Da sunka gabata a illimina.

 

A kan wannan yaro sahihi,

Alamun nan duka sun wakana.

 

Cikin Attaura har Injila,

Bayani nai duka ya wakana.

 

An ce a Ƙabilar Larabawa,

Nabiyullahi fa zai wakana.

 

Alamomin duka na gane su,

Ga wannan yaro ɗan uwana.

 

 

Ya ce da Abu Ɗalib kiyaye,

Shigarsa ƙasar Sham kwai kiyana.

 

Akwai fa Yahudu zuwa Nasara,

Da zarar sun gan shi da rana.

 

Suna da sani daga lammarinsa,

Suna hasadarsa in ma bayana.

 

Za su yi aniya su ga sun kashe shi,

Saboda Ƙabilanci khiyana.

 

Sai al'ajabi ga Abu Ɗalib,

Ya bayyana kan fuskarsa kana.

 

Ya ce da Bahira kai bayanin,

Alamomin da ka ce ga ɗana.

 

Bahira Arrahib ya nisa,

Ya shiga ciki ɗebo ruwana.

 

Sa in da Muhammadu ya cirata,

Ya je waje sauke raƙumana.

 

Ya ja ragamarsu ya sauke siddi,

Ya juyo gun baffansa kana.

 

Ya iske guri ya cikka danƙam,

Ana dakonsa ya zo a gana.

 

Sa'in da ya juyo kan isowa,

Ashe gajimare ya kare rana.

 

Yana tafe daf a saman Aminu,

Yana mar inuwa baina-baina.

 

 

A sanda ya zo daf da jama'a,

Duk an tsatse gun ya tsaya a rana.

 

Sai ko bishiyoyin kewayen nan,

Su kai masa inuwa annabina.

 

Ya dubi Abu Ɗalib Bahira,

Ya ce masa gaskata lammarina.

 

Alamomi na jimad da tsirrai,

Suna ta sujuda gun nabina.

 

Ka lura da yarda giragizai kau,

Suke rakiya da tsari na rana.

 

Haƙiƙa al'amari na yaro,

Nabiyun Rabbul alamina.

 

Nan take Abu Ɗalib ya yarda,

Ya koma Makka da annabina.

 

Ya ba shi kulawa ta musamman,

Nabiyullahi abin riƙona.

 

To kun ji alama a alamu,

Na annabta daga annabina.

 

Daga Yahudu zuwa Nasara,

Suna da busharar mai Madina.

 

Mahasudai ne da baƙar ƙiyayya,

Ta sa su ƙiyayyar annabina.

 

Sahihi siratu nabbawiyya,

Ta Albani Nasiruddena.

 

 

A shafi na asshirin da tara,

Ku duba za ku ishe bayana.

 

Hakanga a Siratussahiha,

Ta Baihaƙƙi ciki kwai bayana.

 

Na Doktor Akhar in ka duba.

Akwai fa ruwayar nan sanina.

 

Cikin shekaru ashiri Habibu,

Zuwa da biyar duka shugabana.

 

Ya ɗauki sana'ar ya yi kiwo,

Na dabbobi a biya gwanina.

 

Su ba shi amanar raƙumansu,

Ya kora yat tafi shugana.

 

Ya faɗaɗa harka ta fatauci,

Yana tafiya Sham shugabana.

 

Ya zo a Sahihu Buhari cewa,

Yana kiwon raƙuna gwanina.

 

Amana ta sa ta fara yaɗo,

Gami da karimci ga amana.

 

A sanda Khadija ta gayyace shi,

Da zummar su yi hulɗa nabina.

 

A sanda suka tafi sun ka dawo,

Sai Maisaratu ya faɗa wa Nana.

 

Atabau abadan fa a rayuwata,

Ba ya Muhammadu a amana.

 

 

Da karamci ga kyawun hali,

Maisaratu ya labarta wa Nana.

 

Da taj ji hakan ga Khadija Nana,

Ta kamu da ƙaunar ɗan Amina.

 

Ta nemi da sui aure da Mamman,

Ya lamunce mata annabina.

 

A sannan annabi shekarunsa,

Sun kai ashirin da biyar nabina.

 

Khadijatu ko na shekara ashirin,

Da takwas bisa bincike na.

 

Zama na Muhammadu da Khadija,

Abin sha'awa da zaman lumana.

 

Sun shekara kimanin ashirin,

Da biyyar duk a zaman lumana.

 

Annabi bai mata kishiya ba.

Sai da fa tay yi wafati Nana.

 

Khadijatu mai matsayi a mata,

Gurin Mamman da Ubangijina.

 

Allahu da kai nai ya yi aike,

Ya ce Jibrilu ka ce wa Nana.

 

Ina gaishe ta Khadija Nana.

Gidanta na zinare a Janna.

 

Na sakamakon haƙuri Mamman,

Masoyin Allah amnabina.

 

 

In ban da Khadijatu duk amata,

Wa Allah ya yi wa haka ku tona.

 

Sai Nana Khadijatu mai darajja,

Da fifikon daraja a baina.

 

An sami hadisi a Buhari

Da annabi ke yanka nabina.

 

Ya sa a yi yanka ya raba wa,

Ƙawayen Bintu Khadija Nana.

 

Saboda tunawa da wafati,

Na Nana Khadija ta shugabana.

 

Matsayi na Khadijatu gun Habibu,

Ya zarci kwatanci a gurina.

 

Har A’isha bintu Abubakar ma,

Ta ce a hadisi kanta Nana.

 

Ni ban taɓa kishi kan mace ba.

Sai Nana Khadija ta annabina.

 

Don yarda Muhammadu ke tunata,

Ya sa na yi kishinta a raina.

 

Da na lura da kimarta ga manzo,

Na ja baki ko na kama kaina.

 

Ta haifi ɗiya shida da ma'aiki,

Maza biyu mata huɗu Nana.

 

Alkasim shi ne ɗa na farko,

Sannan Addayyabuddahirina.

 

 

Da Zainab sannan sai Ruƙayya,

Da Ummulkulsumu ‘yan uwana.

 

Da Faɗimatuzzahara'u Nana.

Mai sunan kakar annabina.

 

Akwai Ibrahim wanda mariya-

Tul Kibɗiyyar annabina.

 

Saɗaka ce a wajen ma'aiki,

Ta haifi cikon na bakwai sanina.

 

Cikin surukai na Khadija Nana.

Akwai Usman Bini Affana.

 

Ya auri Ruƙayuatu Ussumanu,

Ta rasu a ɗakin Ussumana.

 

Sai annabi yak kuma ba shi Ummu,

Khulsumu aure Ussumana.

 

Zainab kuma ta auri Abul As,

Ɗan rabi siriki na Nana.

 

Sannan sai Faɗima Zahara'u,

Ta auri Ali siriki na Nana.

 

Ɗan baffan annabi ne Aliyu,

Ɗa ne ga Abi Ɗalib sanina.

 

Muhammadu ɗan asali da dangi,

Kuraishiyyu kuma Hashimina.

 

Bara ku ji ammomin ma'aiki,

Na Allah mai Maka mai Madina.

 

 

Da sayyaduna Hamza da Abbas,

Ɗiyan kaka gun annabina.

 

Abu Ɗalib da abu Lahabin,

A baffanni nasa annabina.

 

Azzubair Abdulka'aba Mukauwim,

Jarar da Kusam duka za ni zana.

 

Almugira Hajal, Mus'ab Naufal,

Da Al-auwamu cikin na zana.

Daga Diwanin Waƙoƙin Aminu Ladan Abubakar (ALA) 

Post a Comment

0 Comments