Ticker

6/recent/ticker-posts

7.25 Karibu Ɗantata - Daga Diwanin Waƙoƙin Aminu Ladan Abubakar (ALA) (Page: 348)

Yakasai, S. A. & Sani, A-U. (2021). Diwanin Waƙoƙin Aminu Ladan Abubakar (ALA). Kaduna: Amal Printing & Publishing Nigerian LTD. ISBN: 978-978-57624-9-0.

Amshi

Marhaban lale da sauƙarka sahibinmu Karibu Ɗantata.

Tamburan ALA mai waƙa ke yabo ga Karibu Ɗantata.

 

Godiya ga Mamallaki Allah

Mai abin baiwa da karɓewa.

 

Mai aro a guri na mai mulki,

In ya so kuma sai ya sauyawa.

 

Godiya a gare shi takkebu,

Shi kaɗai Allahu mai kowa.

 

Ga yabo gun sahibi nawa,

Tambura na Karibu Ɗantata.

 

Ga yabo ga Karibu sallalah,

Annabin da ba ai kamatai ba.

 

Shugaban duka talikan farko,

Wanda bai taɓa saɓa Allah ba.

 

Annabin da muke wa baitoci,

Shukkiran da abin yabo babba.

 

Duniya duka na yabon halin,

Ɗan Amina makwaikwayar bauta.

 

Ni Aminu ina yabon ƙauna,

Ba batu na wuri da sisi ba.

 

Darraja ta batu a kan ƙauna,

Bai faɗo ba zanuwa zai ba.

 

 

Dukka alatu da duk ke nan,

Bat ta kai ƙauna a kima ba.

 

Duk abin da kuɗi ya sama ma,

So ya ba ka gabansa ba wai ba.

 

Samfurin daraja a kan ƙauna,

Rabbu ya yi a kan kiran sallah

 

Dubi in ka kirayi Jallallah,

Dole sai ka kira rasulallah.

 

Babu sarki face Allah,

Ahmadu a garai rasulallah.

 

Sanadin haka tambarin ƙauna

Ke gwadi daga mai halittata.

 

Ka ga Rabbu fa bai yi abba ba,

Ba uwa a garai bare abba.

 

Kana Rabbu fa bai yi saƙo ba,

Lasharika lahu gwani Rabba.

 

 

Kana Rabbu fa bai yi mata ba,

Ko a ce ya yi ɗa da jika ba.

 

Rabbu ya yi Karibu ba wai ba

Sahibinsa makwaikwayar bauta.

 

Gawaddabe ɗoɗar a kan turba,

Karkata ko dai da ka duba,

 

Sarari maƙurar gudun doki,

In ya nisa ba za ya jure ba.

 

Al’amin kamfa haƙin tuji,

Sai fa wanda ba za ya gane ba.

 

Rugugin na cida ishe kurma,

Sai jikin da ba zai yi motsi ba.

 

Sulkumin guzuri gurin falke,

Ɗan abin da ba za a rassa ba.

 

Hadari malafa ta alƙaryu

Gajimare ado na mai duba.

 

Marhaban lale da sauƙarka,

Sahibinmu Karibu ɗan babba.

 

Tamburan ALA mai waƙe,

Ke yabo ga Karibu Ɗantata.

 

Ga yabo a gaba ta cancanta,

Gun Karibu abin yabo nawa.

 

Masanin ilimi na addini,

Masanin boko gwani nawa.

 

Mai halin a yaba a kwarzanta,

Mai halin kyauta wajen kowa.

 

Mutumin jama'a nake yiwa,

Baituka a cikin fusahata.

 

Daga Abdulkadir Ɗantata,

Baba ga Ruƙayya Ɗantata.

 

Ɗan Abdu uba gurin abdu,

Baban Abdulkadir Ɗantata.

 

 

Gaishe ka uba ga Maimuna,

'Ya'yanka kakaf a waƙata.

 

Ango na Samira ‘yar baiwa

Mai sonka na sa a waƙata.

 

Gimbiya fa Samira sannunki,

Jinjinarki daban a waƙata.

 

Kin zamo tauraruwar mata,

Martaba ga Karibu Ɗantata.

 

Na kira ki uwar maƙera ma,

Ba guso a gida na Ɗantata.

 

Kin zamo a gare shi alkyabba

Mai adonta Karibu Ɗantata.

 

Abdulkadir Sunusi Ɗantata,

Allah kyautata kwanciyar baba.

 

Mariya Sunusi Ɗantata,

Allah ja kwananki don Rabba.

 

Hajiya Balaraba Tata,

Allah kyautata kwanciya Rabba.

 

Hajiya A'i S. Ɗantata,

Allah gafarceku da tsafta.

Daga Diwanin Waƙoƙin Aminu Ladan Abubakar (ALA)

Post a Comment

0 Comments