Ticker

6/recent/ticker-posts

7.24 Hindu Ta Bunun Bargu - Daga Diwanin Waƙoƙin Aminu Ladan Abubakar (ALA) (Page: 345)

Yakasai, S. A. & Sani, A-U. (2021). Diwanin Waƙoƙin Aminu Ladan Abubakar (ALA). Kaduna: Amal Printing & Publishing Nigerian LTD. ISBN: 978-978-57624-9-0.

Amshi

Uwargida sarautar mata Hindu ta Bunun Bargu,

Allah ya ƙara danƙon ƙauna taki da Bunun Bargu.

 

Shimfiɗa

Za ni yabon uwar mata-

Uwar mata

Za ni yabon uwar mata

Sarauniyar mata

Adon ganin mata

Abin kwafar mata

A halinta ba wauta

Zaɓi ga Bunu mai tsafta

Taurariwar cikin mata

Hindu ke ce uwar mata

Mai kyauta yi a kyakyata

Halinki Allah alkinta

Maman Walid kin huta,

Maman Farida kin kyauta,

Uwa ga Zahara kyauta,

Ɗiya ga Hindu mai kyaita,

Da Bunun Bargu mai tsafta.

 

Allah mu na ta gode ma,

Jallah wa azza mai girma,

Allah Wahabu mai girma

Muna yabo da alfarma.

 

Ƙara isa ga manzona,

Farin ganin idanuna,

Wanda nake yi wa ƙauna,

Saboda son ka sarkina.

 

Hindu saraunaiyar mata,

Zan kambama a waƙata,

Giwar sahun cikin mata,

Kin fi gaban sanin mata.

 

Uwar gida rugin ɗaki,

Gida yana a hannunki,

Bunun Bargu angonki,

Ya yi na'am da halinki.

 

Duk wani babba mai mulki,

Ko mai kuɗi cikin ɗaki,

In ka gan shi ya na raki,

Cikin gidansa ba sauƙi.

 

Mijin ki babu gantsarwa,

Bai da hali na ƙisshirwa,

Bunun Bargu son kowa,

Allah ya ƙara dafawa.

 

Sannu majinginar ‘ya’ya,

‘Ya’yanki masu tarbiyya

Ga ilimi da alkunya

‘Ya’yan saraki mai gayya.

 

Hindu Bunu ce tsani,

Halinki babu mai rauni,

Mai ilimi na zamani,

Ga son kula da addini.

 

Uwar gida gwanar mata

Hundu abar kwafar mata,

Baƙonki na ganin gata,

Mai son ki bai wulaƙanta.

 

 

 

Bunu duk nagartarshi

Da kyan hali iri nashi,

Hindu kina kamar nashi,

Kin kwaikwayon dabi'unshi.

 

Sannu uwar gidan zaki,

Bunu ya fahimce ki,

Hindu fa ya karance ki,

Sabida haƙƙuri naki.

 

Allah ya ƙara buɗawa,

Ya raya masu tasowa,

Ya kau da duk abin yarwa

Da ‘yan gani a kushewa.

 

Ki ƙara godiyar Allah,

Domin kina cikin daula,

Gidanki babu mai maila,

Da ‘yan ɗiyanki ba wahala.

 

Kyauta ta Rabbu gun bawa,

Sai mai rabo ya ke baiwa,

Mai godiya da ƙarawa,

Zai yi gamo gamon baiwa.

 

Hindu ga mai mutunci ce,

'Yar zuri'a ta dangi ce,

Mai haƙuri da kowa ce,

Hindu maso zumunci ce.

 

Ala yana ta sambarka,

Da baitukan yabon barka,

Halinki duk na san barka,

Mijinki mai halin barka,


Hindu sarauniyar mata,

Hindu ja ragamar mata,

Hindu zaƙaƙurar mata,

Hindu adon ganin mata,

Hindu tauraruwar mata,

Hindu zubardajin mata,

Zinariyar adon mata,

In ga ta a cikin mata,

Mata gurin Bunun Bargu Allah riƙa da sarrauta.

Uwargida sarautar mata Hindu ta Bunun Bargu,

Allah ya ƙara dankon ƙauna taki da Bunun Bargu.

Daga Diwanin Waƙoƙin Aminu Ladan Abubakar (ALA)

Post a Comment

0 Comments