Ticker

6/recent/ticker-posts

7.23 Farfesa Ango Abdullahi - Daga Diwanin Waƙoƙin Aminu Ladan Abubakar (ALA) (Page: 341)

Yakasai, S. A. & Sani, A-U. (2021). Diwanin Waƙoƙin Aminu Ladan Abubakar (ALA). Kaduna: Amal Printing & Publishing Nigerian LTD. ISBN: 978-978-57624-9-0.

Amshi

Farfesa Ango Abdullahi

Kwalejin Lafiya Fasaha.

Farfesa Ango Abdullahi,

In adɓance suna ilimmi.

 

Shimfiɗa

Farfesa Ango Abdullahi,

Majami'ar sanin ilimmi,

Farfesa Ango Abdullahi,

Matattarar sanin ilimmi,

Farfesa Ango Abdullahi,

Kwaleji ginshiƙin ilimmi,

Farfesa Ango Abdullahi,

Kira su baharul ulumi,

Farfesa Ango Abdullahi,

Mabubbugar sanin muƙami,

Farfesa Ango Abdullahi,

Hudan li kullil umumi,

Farfesa Ango Abdullahi,

Nurul haka'ikil umumi,

 

Allah abin yabo da bauta Allah Aleemu mai ilummai,

Haki da sharraɗi na bauta da ragamar riƙon muƙamai,

Ka sa su ƙarƙashin na sannai matattarar sanin ilimmai,

Ka ƙarfafe ni Mabuwayi za ni yabon gidan ilummai.

 

Ga gaisiwar uban muƙamai abin yabon jimad da tsirrai,

Mabubbugar sanin asirai taska ta illimi da sirrai,

Nurul huda mijin Khadija sirrul asarari mai asirai,

Shugaban dukan halittu aljan mutum gami da tsirrai.

 

 

 

 

Farkon abin da mai halitta ya fara yi cikin halittu,

Allo na kuddura akay yo lauhil mahfuzu kan halittu,

Sai alƙalam abin rubutu kafin a ƙagi duk halittu,

Wannan madogarar riƙo ce kan ilimi da ma rubutu.

 

Farfesa Ango Abdullahi na nufi in yi wa rubutu,

Matattarar sanin ilummai a ƙarƙashin sanin rubutu,

Kun san yawan sanin ilummai fa ba shi sa mutum ya zautu,

Matattarar sanin ladubbai da ke saka mutum ya saitu.

 

Farfesa Ango Abdullahi matanƙwarar hagun da dama,

Fannin sanin hagun da dama ba su sa'a fa in gaya ma,

Da babbaƙu da farfaru duk je ka kawai a bibiya ma,

Boko ulumu Arrabiyun babu ta inda sun gaza ma.

 

Kai har special rukunnai farfesa Ango bai bari ba,

Masu buƙatuwar musamman ba sui ƙasa ta durƙuso ba,

Mai tawayar gani makanta da ma kurumta ban cire ba,

Su ne special a keɓe ba za a bar su kan sani ba.

 

Akwai special target ma ga masu uzzurin buƙatu,

Primary a shekara biyu, da nasara cikin karatu,

Secondary a shekara ɗai ka kammala ta ka naƙaltu,

Farfesa Ango Abdullahi babu kamarku makrantu.

 

A ɓangare guda na dama da rukuni na makarantu,

Da rukuni na tahafizu haddar kur'an a makarantu,

A rukuni na Issilamic da islamiyun karatu,

Ga kuma jami'a a keɓe reshe guda fagen karatu.

 

Bordin school da jeka dawo a rukuni na makarantu,

Sannan adult education a rukuni na makarantu,

Yanzu faculty za ni zano a rukunin zubin karatu,

Farfesa Ango Abdullahi ta yi daban a makarantu

 

 

 

School cleanical norsing daga facuties rukunnai,

Science community health ma a rukuni cikin rukunnai,

Aotoupedic cast physiotherapy a rukuni cikin rukunnai,

ƁHW da TBA traditional birth attendence.

 

Ga ilimin sashin haƙori dental da ɓangare suna yi

Dental therapy, dental assistant, dental technician suna yi,

Sannan school enɓiromental farfesa Ango duk suna yi,

Enɓiromental assistance farfesa Ango duk suna yi,

 

Enɓiromental technicians farfesa Ango na koyarwa,

Enɓiromental officer farfesa Ango na koyarwa,

Sashe na kimiya ƙwararru suna da ɗakunan gwadwa,

Labouratories gurin gwadawa gwaje-gwaje na illimarwa.

 

Science lap technology nutrition na musamman

Medical lap science na nan da medical emegin na nan,

Helth impormation management a rukunai ciki suna nan,

A rukuni na makarantu wa za ka iskuwa hakan nan?

 

Sashe na adminstration za ni in zayyana a sannu,

Suna da low school priɓate a rukuni cikin sanannu,

Busness admin cikin rukunnai a rukunin sahun sanannu,

Public admin kusan suna nan sun kai agar cikin sannanu.

 

School of education fanni science school ciki ana yi,

Sannan da art education couses dukansu ma ana yi,

Kana da cumputer studies aji-aji duka suna yi,

Cumputer engineering haɗa graphics suna yi.

 

Sai networking a gano certificate da diploma,

Suna national diploma high national diploma,

Ga kambunan karramawa da anka ba su takarima,

Yawansu ya wuce a ƙirga sai dai in tsakuro kaɗan ma.

 

 

 

Primary secondary ma ba na biyunsu in gaya ma,

Sun ɗauki world the best Ƙur'anic gasar kira'a in gaya ma,

Gasar da anka yo a Makka da nursery school kuma ma,

Gasar sakandire aji biyu high jam namu ne ya sama.

 

Sai tafsirin alfatawa in English da an ka yo ma,

National Islamic oriantation su suka tsara ai hakan ma,

Rukkunin cikin faculties da library kuma ma,

Suna da library local har da na zamani in ce ma.

 

Asibitinsu na musamman kana abin hawa isassu,

Abin fa sai ido ya duba faɗi da baki bai isar su,

Bari in zana bord trusty ku san fa sun wuce isassu.

Farfesa Ango Abdullahi komai suna da su isassu.

 

Prof. JS Mari yana cikinsu bord trusty,

Prof. Isa Usman yana sahunsu bord trusty,

Prof Garba Kalayi a rukuninsu bord trusty,

Prof. M.I Dimbilin tsaka tsaki na bord trusty,

Prof. Binta I. Yusuf tana cikin body trusty,

Prof. Rukayyat Rufa'i tana sahu na ‘yan trusty,

Dr. Aliyu Shamsuddeen yana tsakarsu ‘yan trusty,

Engineer Hasan Suraj a rukuninsu ‘yan trusty,

Malam Hamza Ramalan suna cikinsu duk trusty,

Malam Abubakar Abdulrazak a ɓangaren cikin trusty.

Daga Diwanin Waƙoƙin Aminu Ladan Abubakar (ALA)

Post a Comment

0 Comments