Ticker

6/recent/ticker-posts

7.22 Hashim Ubale - Daga Diwanin Waƙoƙin Aminu Ladan Abubakar (ALA) (Page: 339)

Yakasai, S. A. & Sani, A-U. (2021). Diwanin Waƙoƙin Aminu Ladan Abubakar (ALA). Kaduna: Amal Printing & Publishing Nigerian LTD. ISBN: 978-978-57624-9-0.

Amshi 

Yau gida na karkata zan waƙar namijin mazaje,

Ubangida da halin kirki sannu Hashim Ubale.

 

Shimfiɗa  

Yau yabon na babban gawo ne mai jure marka,

Yau yabon na sawun giwa ne mai baje na jaka,

Madugu uban tafiyar talaka dole in taɓa ka,

Tsuntsun da ke shakkar marka ba shi daka taka,

Idan ana dara bisa al'ada sa uwa a baka,

Duk wanda ke tsumin tsintsaye ai ba shi nuna bakka,

Da za su gan ta sai su fashe su tafi kai ka nuna hauka.

Yau gida na karkata zan waƙar zaƙaƙurin mazaje,

Yau gida na dawo zan waƙar phamacist Ubale.

 

Allahu Wahidun Masanin sirrin baɗini da farke,

Mai juya yau da gobe da'iman rayayye a farke,

Sarki da gyangyaɗi ko barci ya koru gunsa take,

Ka ba ni izini in yi baitocin sa Hashim Ubale.

 

Kamun ƙafa ga ɗan Abdullahi ubangida ga Dije,

Baba ga taufatul ahawaziyya ‘yar ɗiya ga Dije,

Tushen jinin tsatson ahalal baiti yau gidansu zan je,

In miƙa wasida da biyayyarsu nasaba a lale.

 

 

 

Ƙauna ta sa nake maka ƙaunar mu'amalarka,

Hali ya sa nake maka waƙa hali na tarbiyarka,

Khairi ya sa nake maka waƙa na hangi taffiyarka,

Sara nake da duban bakin garma na ce Ubale.

 

Gidan da anka ce da badangalci na taho a gujje,

Har na ji ma waɗansu suna cewa ya nake garaje,

Na taho in sa da bushara ne khaliƙinmu yarje,

Allah yi lamuni a wurin Hashim phamacis Ubale.

 

Wanda kaj ji iyalai nai suna yunƙurin yabo nai,

Ko ba a ce ba ka san adalci yakana guri nai,

Babu musu idan ka ji na ce kwai wahala iri nai,

Allah ya ida dukka muradinka Hashim Ubale.

 

Halin mutum abokin taku ne Hashim Ubale,

Aikin mutum madubin zuciya tasa ɗan Ubale,

Himma adon nagartar ɗan Adam Hashim Ubale,

Wannan batu na masu azanci ne Hashim Ubale.

 

Na san mu'amala uban ɗaki ba shi nuna darga,

Tushen gida irin ilimi ne shi babu nuna yanga,

Allahu ka sani ba ƙarya nai ba ko nuna burga,

Sara nake gaba ta muhalli kan phamacis Ubale.

 

An ce hali fa zanen dutse ne ba rabe-rabe,

Halin mutum abokin takunsa ba rabe-rabe,

Allah ka ida burin ƙaunarmu sa mu kai ga gobe,

Allah isar da zomo ga harawa Hashim Ubale.

 

Duniya gidan ka zo na zo ba madauwama ba,

Duniya gidan zuba dashi ce ba da kangara ba,

Madalla da masu halin kirki za su kai ga riba,

Allah ya ƙara ƙarfin imani phamacis Ubale.

 

 

 

Duniya malafar sarari ce Hashimu ɗan Ubale,

Sarari maƙurar mai hange sir! Hashim Ubale,

 Lafiya ko jarin talakawa Hashim Ubale,

Tabbata haƙiƙa talakawa na gidan Ubale.

 

Girgije abin sha'awar kallo kan ruwa ya sauka,

Damina alamar albarka in ta zo ma shuka,

Ga ruwa abokin aiki nan masani na doka,

Karkara da birni an san ka pharmacis Ubale.

 

Jirgin sama ko mata ta daka ta san zubinka,

Jirgin sama ko ba ta gan ka ta san irin dirinka,

Ko da kuwa ɗa ne nag goye ya san da iska,

Hantsi kake leƙa gidan kowa Hashim Ubale.

 

Ga mai takanas baban Mamman bakirul ulumi,

Sha ƙwaramniya gugan ƙarfe baba ga Ummi,

Mai uwar maƙerar nan Hajja gantamau na Lami,

Shi yake yabon gwamnan gobe Hashim Ubale.

 

Anka ce kiyaye mai laya zamani gabanka,

Sanda duk ka ɗauki abin sara ka kiyayi kanka,

In ta ɓaci koko rashin aune sai ka sari kanka,

Ka yi taka ka yi ta ɗan yaro Hashim Ubale.

Daga Diwanin Waƙoƙin Aminu Ladan Abubakar (ALA)

Post a Comment

0 Comments