Yakasai, S. A. & Sani, A-U. (2021). Diwanin Waƙoƙin Aminu Ladan Abubakar (ALA). Kaduna: Amal Printing & Publishing Nigerian LTD. ISBN: 978-978-57624-9-0.
Amshi
Dakta Bukar Biu mai halin a yaba a yiwa kirari.
Cancanta ta sa ni yabon gatam adabi na Hausa.
Shimfiɗa
Hamshaƙin sadauki,
Mai ƙarfi suluki,
Ja ragama sadauki,
Za a bi babu raki,
Ga mai kare hakki,
Hanya babu miki,
Ba kuma tauye haƙƙi,
Sai dai kare haƙƙi,
Linzami na doki,
Kan adabi na baki,
Har adabi na inki,
Bikin sharafi na doki,
Wa zai je da jaki,
Da na nufi nai yabo sunan Allah na saka a fari,
Mai zarafi na mulki da ke saka al’umma sururi,
Mai ƙudurar kaɗaici da ke da buwayar duk buri,
Babu tsimi dabara da yaffice bauta mai a tsari.
Rabbu dubun aminci daɗa su ga Annabi mai karamci,
Ali ka sa Sahabu da sunka biyar sa cikin aminci,
Annabi mai karamci raba mu da masu yi mai butulci,
Nurul Annuwaru wanda zuwan sa ya ba mu ‘yanci.
Dr. Bukar Usman
Jigon wagga waƙa yabo na nufa a gurin Sadauki,
Yabo koko kirari gurin mashahuri ɗa na kirki,
Kadarko zan kira shi a kan adabi ko kuwa Danki,
Dakta Bukar Sadauki a kan adabi sam bai da miki.
Ya rage warwara a garen dangi kan wagga jigo,
In yi yabon Bukar Hamshaƙi da na kira da Gago,
Masu abin ake yi wa take mai jirgi na kago,
Mai hali na ungo bisa cancanta a ba shi mago.
Mai ilimi na Allah Bukar na Biu kan Arabiyya,
Ga ilimi da aiki a wannan fannin Arabiyya,
Mai tsoro na Allah Bukar mai ƙaunar mai biyayya,
Bukar ɗan Ussumanu ina yaba halayyar biyayya.
Kan sha’ani na mulki da hulɗoɗi na ƙasa ya ƙare,
A nan ya yi diggirinsa a kan mulki kuma har ya ƙare,
A nantin sisti nayin (1969) ne a ABU ya gama ya ƙare,
Batu kan eɗposure a nan daraja ta tuƙe ta ƙare.
Akan ce ja da baya ga rago ɗaurin ɗammara ne,
Tushen haihuwarsa Bukar Usmanu a garin Biu ne,
A nantin fotitu (1942) ne goma ga watan sha biyu ne,
Ilimi taƙwararsa da farko yai a garin Biu ne.
Ya ƙara taƙin karatu a King’s Kwaleji da ke a Ikko,
Idan kas ami dama ka dama inda ka samu iko,
Daga Ikko Kwaleji a ABU kuma yai yi dako,
Batu kan eɗposure a yanzu na yunƙura za na ɗauko.
A fannin tsara mulki da hulɗoɗi na ƙasar waje ne,
A nantin sisti nayin (1969) damin rumbu ya fito ku gane,
Famanan Sakatare a fadar nan ta ɗaya mu gane,
Fadar Shugaba na Ƙasa Dakta ku ji tinjimi ne.
Nantin sisti nayin (1969) zuwa kuma,
Nayintin nanti nayin (1999),
Yai dacen muƙami a fadar lamba ɗai a layi,
Ko da na ce a layi muƙamai nikka nufi da layin,
Yaz zam OON da Tarayya ta saka a layi.
Kambun OON ya karɓa daga Tarayya,
Ita ta ba shi OON domin tsantsar biyayya,
A zangon shekara ta dubu biyu (2000) sunka yo a baya,
Taƙaitawa nake yi idan ka ji na katse wata aya.
Tusauzan tatin (2013) ne kuma sashi sun ka ba shi,
Sashein Nazarin Harshe na ƙasa da Afurka Sashi,
Don bunƙasa harshe da al’adun Hausa su tashi,
Linguistic Association awad na suka karrama shi.
Daktan Adabi anka ba shi a ABU ta ba shi,
Sai taron gamayya da BUK ta shirya a sashi,
BUK da guiwar manazarta kuma sun ka yi shi,
Su ko a kan gamayya ta tatsuniyoyi anka yi shi.
Ƙasaita ta taron da anka yi Emeritos suka yi wa,
Emeritos a Hausa na ce maka gangaran na kowa,
Musamman anka tsara shi domin ƙarfafa ƙaimin guiwa,
Bukar Usumanu Gago kamarka a samu a yi sawwa.
Ban ga irin kamarka Bukar Usumanu a nahiyarmu,
Don ka zam kadarko na ratsewa mu fitar da kanmu,
Gatan adabinmu Bukar Usman har lammarinmu,
Mai son ci gabanmu a kan lamarin adabin ƙasarmu.
Ka zama fandishon Hausa bayan ka zama kadarko,
Kai ko jami’u na hawa bayanka bisa kadarko,
Idan aka ɗauke marubutan da ka yi wa ƙaimi da tarko,
Tarkon nasarar rayuwar mazari babban kadarko.
Kai ne kuma Shugaban Ƙungiyar Nazarin Adabin Bahaushe,
Kana daga Kwamitin Aminci na Ƙasa don Raya Harshe,
Sannan Katibi ne guda da ya himmatu raya harshe,
Don haka nai yabonka Bukar ɗan Shehu idon Bahaushe.
Rubutu ka yi zoƙar zuwa matani da na ma hikaya,
Rubutu ka yi zamƙam irin na zube da ya zam maraya,
Da Tarihin Biyu History of Biu a cikin ƙidaya,
Taskar nan ta Tatsuniyoyi za ni rufe ƙidaya.
A ƙarshe zan yaba wa uwar ɗakinmu Dupe a waƙa,
Eɓery successful man gefe mace marar mushaƙƙa,
Dupe Allah bar zumunci da ƙauna babu ɗison nifaƙa,
Kemi Allah ji ƙanta ka sa rahamarka da tausayinka.
Dr. Bukar Usman
Cikin fatan sabati na sa Mairo babbar ɗiyarka,
Ina roƙo ga Allah daɗo rahamarka da tausayinka,
Cikin kabarinsu Fati da Maryama ‘ya’yayen ga naka,
Da Maro da Fati Allahu ka yi musu rahamarka.
Halima Bukar Usuman na yaba ‘ya’yan maigidana,
Hadiza Bukar Usuman cikin ‘ya’yan nan ba khiyana,
Hafsa Bukar Usuman ina baitocin so da ƙauna,
Sai autar cikinsu da akan ce Zara Bukar amana.
Dakta Bukar mai halin a yaba a yi wa kirari,
Cancanta ta sa ni yabon gatan adabi na Hausa.
0 Comments
ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.
HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.