Ticker

6/recent/ticker-posts

7.20 Ginshiƙin Adabi - Daga Diwanin Waƙoƙin Aminu Ladan Abubakar (ALA) (Page: 332)

Yakasai, S. A. & Sani, A-U. (2021). Diwanin Waƙoƙin Aminu Ladan Abubakar (ALA). Kaduna: Amal Printing & Publishing Nigerian LTD. ISBN: 978-978-57624-9-0.

Amshi

Dakta Bukar na Biu Katibi Ginshiƙin Adabi,

'Yan Hausa na ta yabon gudunmawarka sashen adabi

 

Shimfiɗa

Alfijir ya ketto ga alamu na waye gari,

Rana idan ta fito tai rabon ayyuka a gari,

Na zamma ɗankadafi na dafe ginshiƙi na gari,

Toro idan ya riƙa shi kaɗai ke kiwo a gari,

Ba ko gwaji zuma da maɗi ko bare sukari,

In Rabbu ya yarda yanzu ka zam kara da gari,

Alan Kanawa ne ke yabon ka ba alfahari,

Ƙauna da cancanta shi ya sa nake ma shi'iri,

Dakta Bukar na Biu ka zamo gangaran na gari,

Gatan maso adabi a yabonka ba na garari.

 

Farkon mafarina na sako Rabbu kan shi'iri,

Neman amincewar Rabbu ƙarfin cikin sadari,

Jigon zubin waƙa sai ya zamma ƙarin gishiri,

Sai warwarar jigo ta sauƙaƙa ya kukan kanari.

 

Mafaka malafata dogaro da ƙaunar Bashari,

Mai gargaɗi bushira kan tafarki na alkairi,

Shumagaba na gari da ya ida saƙon khairri,

Nurul huda Ɗahe ɗan Amina Sarkin Haƙuri.

 

Jigon zubi na yabo zan yabo ne a gun Bahari,

Fannanu zan wa yabo mai dabi'u na alkhairi,

Gishirin miyar adabi Dakta Malam Bukar Bakari,

Jirgin fito a tafi tarrago ko na ce Bahari.

 

A yabon ƙashin bayan addabi sai fa an nazari,

In an karambani makkawa babu ai garari,

Ko tuntuɓen baki anka yo an yiwo garari,

Ni na yi togaciya da Rabbu Allahu Alkabiru.

 

Sarari gaji da gwani zan yaba wa kyawon ƙuduri,

Mazari uban nazari ga cida mai amo a gari,

Haɗari Ado a gari allamin zubowar marari,

Dakta Bukar na Biu alƙalam mai karab da gari.

 

Matsalan kiɗan kurya yarda ke sa jiki marari,

Haka baitukan waƙa ke sakawa kamar mazari,

Hadarin ginin baiti ya wuce na baka a kwari,

Ku ji baitukan waƙa na sakawa a yada kwari.

 

Kifi kada a ruwa sun yi bamban da ɗan gwadari,

Haka ko ruwan zam-zam ya yi bamban da na tsari,

Tsaran Bukar na Biu ka daɗe kana zaga gari,

Ka gama ka kauce min bai da tamka kakaf a gari.

 

E!!! Wani na da ilimin nan ya rage shi aiki na gari,

Ilimi da aikinsa shi yake nuna ɗa na gari,

In babu aiki kyau ka zamo jaki alfadari,

Masalul himari ka ce yahamilu asfara gari.

 

Wani ga tulin ilimi ba taro darhami da ɗari,

Marashin kwabo da ɗari yaya zai zam karab da gari,

Wani ga tulin ilimi kana ga ɗan sule da ɗari,

Ba hikkima fusuha yaya zai zam kamar Bahari.

 

Wani ya yi rankatakaf ga sani ga kwabo da ɗari,

Kana fagen hikima manihi ne gwanin shi'iri,

A fagen mu'amilla a nan a kai massa shan sukari,

Dakta Bukar na Biu mai hali tarra duk na gari.

 

Rimi ado na gari damina dausayi na gari,

Samji a taka ka yanzu a kwan cikin garari,

Tugi tsiron tsauri kofako ka fito a gari,

Daktoro ɗa na Biu mai halayya ta wa shi'iri.

 

 

Yaro na nake a tsaye jallabi na kawai zikiri,

Sarkin karambani rarrafe ne nake shi'iri,

Ka ji tuntuɓen harshe shekaruna ka yo nazari,

Kar ka hukunta ni rukkuni naku Al-Bakari.

 

Kwana a tashi ka yo safiya zuwa waye gari,

Da yaro ake babba dare yana yi da alfijiri,

Kuna ɗauke sawunku da tafuka naku a sarari,

Muna sanya sawaye namu don kwaikwayo na gari

 

Mai inkiya da yabo Al-aminu ALA bahari,

Alan Kanonmu gari gwaddabe na waƙa shi'iri,

Shi ke ƙwarara yabo gun Bukar abin alfahari,

Saƙo na yaushe gamo ga shi nan sai a min nazari.

Daga Diwanin Waƙoƙin Aminu Ladan Abubakar (ALA)

Post a Comment

0 Comments