Ticker

6/recent/ticker-posts

Farfesa Yakasai

Yakasai, S. A. & Sani, A-U. (2021). Diwanin Waƙoƙin Aminu Ladan Abubakar (ALA)Kaduna: Amal Printing & Publishing Nigerian LTD. ISBN: 978-978-57624-9-0.

Amshi: Wallawala zan yi da harshe na,

In yaba wa gwarzo na,

Ka daɗe cikin muradinmu,

Farfesa Yakasai.

 

Walwala zan yi da harshena,

In yaba wa gwarzona,

Ya daɗe cikin muradina,

Salisu Yakasai.

Ya Ubangijin da yai ƙalbi, a cikinta yai hubbi,

Nai tawassali cikin ƙalbi, bi hubbi Mahmubi,

Wasiɗa da so ga Al’arabi, Mahamudu Annami,

Ƙara laffazi na harshena, mai samanu mai ƙassai.

 

Sannadi na so idan kac ce, I la’ila ha illalla,

Kana kuma sai ka zan cewa, Muhammadurrasululla,

Idan na ce da so mafi a’ala, babu gilla ba illa,

Dulmiyanni son Habubulla, in dulmuya ma sosai.

 

Turge na wagga wagga waƙa tau, sanadi na so sosai,

Za ni walwale bayanina, in sake shi in fus sai,

A cikin yabon masoyina, Farfesa Yakasai,

Haihuwar gari na Yakasai, Za shi waƙe Yakasai.

 

Sannadi ya sa akan yi yabo, ba da ko muƙami ba,

Darraja ta sa akan yi yabo, ba da darhami ba,

Nasaba ta sa akan yi yabo, ba da ko sadaki ba,

Yau ina yabon ka don ƙauna, Salisu Yakasai.

Professor Salisu Ahmad Yakasai

 

Professor Salisu Ahmad Yakasai

 

Wanni ne ya ce da ni Ala, shawara garan babba,

Ka zamo a yau kana waƙe, ba na ba ka sisi ba,

Ka yi tsohuwa ta Illela, ba gamo da sisi ba,

Ka yi baituka na makkaho, yau kana ta Yakasai.

 

Ni Aminu na yi waƙoƙi, day yawa a don sa kai,

Ni Aminu na yi waƙoƙi, day yawa na sarrakai,

Ni Aminu na yi waƙoƙi, na ‘yan siyasar sa kai,

Yanzu jami’a nake kallo, fagen nazari sosai.

 

 

Inda ad da ma’anar adabi, yadda sani na al’ada,

Inda anka walwalar harshe, bisa ƙa’ida ƙaida,

Inda aka warwarar jigo, na nazari bisa ƙaida,

Su suka cancanta in waƙe, in wa kambama sosai.

 

Su suka keɓe sanin daɗi, da rabe aya tsakuwa,

Nagge suke ko’ina daɗi, inda tai katantanwa,

Jinsu da ganinsu ba ma yi, bisa ƙalƙalar fawa,

Mu muke da baituka cure, su su walwale sosai.

 

Inda aka san sufantawa, a ma a abuntawa,

Inda aka san kamantawa, aka san jisintawa,

Inda aka san kuzuzuta, kambami na yabbawa,

Inda aka san dabantawa, masana sani sosai.

 

Wanda aka ce Prof ne shi, ka ga maƙura kenan,

Ba batun in warware maku shi, kawai masani kenan,

Bincike ka je ka yo gunsa, kai kawai fa shi ke nan,

Salisu Amadu Yakasai, babban masani sosai.

 

Salisu a kan batun ƙauna, ka biya ni ka tara,

Me kake biɗa da ni in ma? Zan yi babu kekkera,

Ka biya ni kan batun ƙauna, ba tsumi da dubbara,

Dole in yabe ka don ƙauna, dattijo Yakasai.

 

Duk abin da mun ka wa adabi, ba biyan mu za ai ba,

Warwara da kun ka wa adabi, ba biyanku za ai ba,

In yabe ku as saman kowa, ban ƙasa a guiwa ba,

Ga ni a Ɗanfodiyo yanzu, sanadinka Yakasai.

 

Inda aka san zubin jigo, warwara da kullewa,

Inda aka san zubin ‘ya’ya, da awo da tsarawa,

Inda aka san hawa sauka, rauji da karɓewa,

Inda aka san awon bahari, da awon ɗiya sosai.

 

Godiya nake gurin Allah, da cika ta burina,

Ma’ana cika ta burina, saƙo ga dangina,

Ni a yau ana fahimta ta, saƙo a waƙena,

Godiya ina yi wa Allah, tahamida ma sosai.

 

Gaisuwa gare ki Maimuna, uwar gida ta Yakasai,

Maman Muhammadu Najibulla, a ɗiya na Yakasai,

Uwa ga Ikkiram abar ƙauna, ‘yar ɗiya ta Yakasai,

Ba ni manta Faruƙu Bello, shu’umi na Yakasai.

 

Ɗalibi a gun furofesa, na Gusau hurabbina,

Sahibin IB Malumfashi, farfesa jigona,

Sahibi na Misba Bello, Farfesa Yakasai,

Ɗan uwan Muhammadu Gwadabe, da Ittijo Yakasai,

 

Idan ka ce wane ne Yakasai, ɗalibin Gusau nawa,

In ka so ka gane Yakasai, na Ibro Malumfashina,

Da ka matso ka gane Yakasai, malami gurin Shuniya,

Dattijo Yakasai, uban gidanmu Yakasai.

 

Malaminmu Yakasai, sahibinmu Yakasai,

Ɗan uwanmu Yakasai, hadiminmu Yakasai,

Hadiminmu Yakasai, godiya ga Yakasai.

Daga Diwanin Waƙoƙin Aminu Ladan Abubakar (ALA)

Post a Comment

0 Comments