Ticker

6/recent/ticker-posts

7.19 Mashal Sadiƙu Dogarin Ƙasata - Daga Diwanin Waƙoƙin Aminu Ladan Abubakar (ALA) (Page: 330)

Yakasai, S. A. & Sani, A-U. (2021). Diwanin Waƙoƙin Aminu Ladan Abubakar (ALA). Kaduna: Amal Printing & Publishing Nigerian LTD. ISBN: 978-978-57624-9-0.

Amshi

Gaisuwar dogarin ƙasata soja mashal Sadiƙu baba,

Garkuwa mai kare ƙasata ko da an so da ko da an ƙi.

 

Shimfiɗa

Tamburanka nake a tsafta,

Gagarau mai halin nagarta,

Gangaran mai abin bajinta,

Tungulun maganin magauta,

Ga ƙwaram firgitar magauta,

Ga azaba ta masu wauta,

Mai ƙure ƙirƙirar maƙeta,

Abi doka kawai a huta-

Soja mashal Sadiƙu baba.

 

Duk abin da nake a farko fari Allah na sa farko,

Mai buwayar kun fa yakunu durƙuso yau nake sakko,

Na yi dako gami da koko daƙwara ce a yau na ɗakko,

Sa kayar nan ta zam gareni atafa don na sami haiba.

 

Ma ta ƙaddama ma ta akkara Rabbu yafe abin da nay yi,

Zunibina yana da nauyi yayyafa min ruwa na sanyi,

Inda naƙ ƙari yin bulayi sai na komo gurin Buwayi,

Mai abin basuwa da karɓa mai rabon falala da riba.

 

Kar na miƙe ƙafa da zance gaisuwa na baro a baya,

Gaisuwar shugaba na farko mai kadarkon gudu a ɓuya,

Sayyadul alamina kas sa kafatan ba ɗigo na ƙarya,

Annabinmu abin kwatanci da ba ay yi kama da shib ba.

 

Shimfiɗar tafiya fa na yi sai batun tafiya a fili,

Soja zan wa yabo a waƙa don abin da a kai a fili,

Daga sanda ka sauƙe kaya na wuta bayyane a fili,

Daga nan na fahimci aiki na gurin S. Sadiƙu baba.

 

Na gano hadari na kaka da ba za ya zub da ruwa ba,

Holoƙo hadari na kaka da ba za ya zub da ruwa ba,

Isumullahil'a'azammu na kira da na hangi baba,

Ya aje rundunar mayaƙa ba Arewa ba ba Kudun ba.

 

Chineke God na ji an ce daga Enyamiri mazaje,

Hande em bone ɗan Fulani ya faɗa da ganin mazaje,

Tungulun yaiwa kansa fili da ira ta zaman mazaje,

Da na waiga na hangi mashal soja mashal Sadiƙu baba.

 

Kai tuwon dare babu daɗi kai ku kauce a sake sanwa,

In ko ciwon ciki suke yi gafara ga maba da kanwa,

Ai abin da a kai a bara comflict na kusa da hanwa,

Atisaye na ce da wannan yanzu za ai ruwan akuba.

 

Ga hazo nan ku ce kumama da ya daina gudun hayaƙi,

Ga maza rundunar sadauki wani zai bi sahun musaki,

Rundunar farmaƙi na zaki masu watsa dabar awaki,

Bana wanga gamon mazaje ba da ni a arankaya ba.

 

Hadari malafar sama'u girgije alami na marka,

Girgije alami na marka wata ran alamin mushakka,

Soja marmari daga nesa mai rawar fitina mushakka,

Baba fild mashal na waƙa ka yabon ka fa ba da wai ba.

 

Bahari na Sa'idu Mamman na Gusau mai kama da sarki,

Malamin da kowa ni sarki ka haɗa su ya zam musaki,

Gangaran uban gwanaye namijin da na ce sadauki,

Kai uban Zahara'u ɗin da Hanan jinniya ta hubba.

 

Sarari mai haji da kallo maganin mai yawan hakilo,

A kada a raya ka baba bai hanin fama a gwalalo,

Maƙiya da mahassadanka ba bihim sai da ko kallo,

Mazari kake baba mashal mai kaɗawa kama da ƙwallo.

Daga Diwanin Waƙoƙin Aminu Ladan Abubakar (ALA)

Post a Comment

0 Comments