Ticker

6/recent/ticker-posts

7.18 Mashal Sadiƙu - Daga Diwanin Waƙoƙin Aminu Ladan Abubakar (ALA) (Page: 327)

Yakasai, S. A. & Sani, A-U. (2021). Diwanin Waƙoƙin Aminu Ladan Abubakar (ALA). Kaduna: Amal Printing & Publishing Nigerian LTD. ISBN: 978-978-57624-9-0.

Amshi

Mashal Sadiƙu baba Abubakar mai halin nagarta,

Horon maza da gaske yana ga cheif of air staff ne.

 

Shimfiɗa

Massassabi masaba,

Awartakin azaba,

Ga masu ƙulla gaba,

Ko masu ƙulla zamba,

Zaki mai hana gaba,

Arangama da baba,

Sai wanda bai sani ba,

Shiru shiru ga baba,

Ga wanda ba shi zamba,

Haba-haba ga baba,

Ga wanda bai manuba,

Farin gani da baba,

Ga wanda ba su zamba,

Makyarkyata aƙuba,

Ga masu shirya zamba.

 

Allah abin riƙona wanda ka sharen zubar hawaye,

Mai ɗazu yau da gobe Maliku share zubar hawaye,

Mai tattalin na goye raya maraya ya zam a raye,

Sa in zamo tsayayye babu galauniya da maye,

Matattarar nagarta kai na nufa da yabo a raye.

 

Allah ka ƙara yarda har da aminci gurin fiyayye,

Mai Makka mai Madina annabi kaka gurin tagwaye,

Da tabi'ai sahabbai har ahali na gida alaye,

A gaisuwar yabon nan har ulama'u irin sufaye,

Tsanin yabon da ƙauna don kwaɗayi da tsumin tsumaye.

 

 

 

Hali abin yabawa babu kama da halin nagarta,

Aikin ƙwarai da horo na 'yan maza da halin jarumta,

Horon maza ilmi kana da tsabar halin nagarta,

Mashal Sadiku baba masu halin a yaba nagarta,

Chief of air staff ne masu hali na yabon nagarta.

 

Ko da fage na fama in ka ga sojan sama a girke,

Arangama a rannan ba ta da kyau ai kawai da sake,

In da kafa ta sulhu ay yi idan an ƙi ko  da sake,

Za a gama a sannan babu taƙi ɗan taƙi na take,

Cikinsu ‘yan daƙiƙu za a a share jini a take.

 

Sojan sama a yanzu za su su yi wa garinku rumfa,

Sui farmaki da safe kan a jima a jido lifafa,

In ka ji ta da gayya to fa salo ne ya sauya siffa,

Da ka ji ta da zaune so aka yi lamarin ya tsufa,

In an daɗe ana yi ba su awa ashirin a tsufa.

 

Shuri gidan matsafa wandara tsafi guri yake yi,

Tsafin guri yake yi dogara wargi guri yake yi,

Sai an daɗe ana yi za a rabe zahiri na mai yi,

Turƙashi ƙare zance mai ɗamarar sa maza bulayi,

Aikin ake da gaske ai matsawar anka shata layi.

 

Wai ƙi gudu nakan ji masu kirari suna biyawa,

Noman kare ake yi da an gano sa gudu tahowa,

Mai da gari kufayi yanzu gari ya zamo kushewa,

Sai ungula da karnai suka zaman dabdala da kewa,

In an ƙi ga wajen nan masu azal sa wuce kushewa.

 

‘Yau shekaru shida cif! Boko Haramun ana ƙwamawa,

Salo-salo na yaƙi yaƙi ya cinye ana bugawa,

Tsibi-tsibi bala'u ke ta amo nan da can kumawa,

An tashi wanga birni gobe ko wancan ake idarwa,

Mashal Sadiƙu baba duk a daƙiƙu ka zan gamawa.

 

 

Cida razana bebe sanya kurame su kama waige,

Dage uban mazaje mai rufe ramin haƙar kurege,

Sai da ruwa na ruɗe anka yi damun ruwa na talge,

Handi em bone baba in ji Fulani da sunka hange,

Hangen fiton jirage ran yaƙi da maza a zage.

 

Aiki yana ga mai shi ka ji batun masu yin azanci,

Cijiji inji yara sun ga gizaka kamar macuci,

Har an yi an gama kaf an kire dukkan lakar macuci,

Sai walwala ake yi ko ta ina kasuwa tana ci,

Madalla mai da horo baba uban mai dabo da kauci.

 

In ka ji tada ƙura baba Sadiƙ bai iso gurin ba,

To ga makwanta ƙura Alhaji Mashal Sadiƙu baba,

Yanzu ka nemi ƙura a 'yan daƙiƙu da ba yawa ba,

Ana zaman lumana Sadiƙu ba za a sanka gun ba,

Ana zama na gaba Sadiƙu ku ke rabon aƙuba.

 

Ga mai yabon azanci Alhaji Alan Kanon Kanawa,

Dan Dije wa ga Dije mai takanas ɗan garin Kanawa,

Kura mabi maraice shakurukundum nake yabawa,

Waƙa ki min ison nan share fage kafin isowa,

Zan ko na gai da mashal don mu yi gani abin yabawa.

 

Na ɗaura ɗammarata Aminu sojan sama fa zan yi,

Na tarkace kiɗan nan na tafi koyi da baba zan yi,

Busan badujalar nan da begilan fama ake yi,

Ko zaune ko kwance in yi barin rayukan ɓarayi,

Weapon sophisticated in yi ruwan bambamai a layi.

 

Haifaffe gari na Bauchi kai kwamanda a Meduguri,

Kai chairman Task Fouce ne matsayinka a Meduguri,

Kai kwamanda a Forthacout da barinka a Meduguri,

Daga nan ka wuce kaduna kai air officer kwamanda.

 

 

 

Can a Nijerian Airfouce Headƙurters da ke Abuja,

Kai riƙon administration chief a head ƙurter Abuja,

Daga nan shugaban ƙasarmu lamba one a garin Abuja,

Sai ya ba ka wannan mataki Chief of Airstaff na soja.

 

Kai ka samar da base a Bauchi na airfouce base a Bauchi,

Da spacial opration na command a gari na Bauchi,

International standard hospital ka gina a Bauchi,

International standard school ka gina a Bauchi.

 

Ka yi fiɓe hundred building officers soldies a Bauchi,

Soldies for militry couse abroad ka yi babu ƙunci,

Don kimanin mutum dubu biyu ka fitar su je su karanci,

Ilimi na intellency don ƙasar mu mu tsere ƙunci.

 

Ka yi odar sophesticated fighter jet huɗu na yaƙi,

Tanadin Boko Haramun militant da suke ta yaƙi,

Kan a waiga haka a dawo a gwaji an ka ƙare yaƙi,

Chief of airstaff ƙwararren masani na lago a yaƙi.

Daga Diwanin Waƙoƙin Aminu Ladan Abubakar (ALA)

Post a Comment

0 Comments